Sashe 214
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
haka bane to yaya ne?,kin taba samun tazarar haihuwa irinta iffa?,ko kin taba kaiwa haka?,shi yasa nayita tambaya ba bayani gamsashe?,ko shi yasa naketa magana ke sam ba damuwa a lamarinki!!!" Ya qarasa fada da wata tsawa data sanyata danne kunnuwanta tana fadin. "Ya isa hamma!!" Ta fada da murya me qarfin gaske saboda tsoratar da tayi. "Tsawa kikeso kiyimin?" Ya tambayeta yana nuna qirjinsa da yatsansa. "Kiyi kome kikeso sabreen.......sonki da nakeyi ne ya jawomin......ki jani da duk kalar abinda kikaga dama.....kiyi duk yadda kikeso!" Ya fada yana wurgar da daya kwalin dake hannunsa a qasa. "Karka qarayimin tsawa hamma" Ta fada tana jin fushi ya fara taso mata. "Karka qara zargina akan abinda ba haka yake ba......idan ba haka ba..." "Ba zaki yafe ba?". "Basai na fada da bakina bama......na gaji hamma na gaji,wanne irin 'ya'yane ban haifa maka ba?,wanne irin baiwa ce Allah bai mana ba na 'ya'ya,samun tazara tsakanin haihuwa da wata haihuwar lallai sai ace sai ya zama daidai dana baya!......ana yiwa Allah dole ne?,idan kuma yace gaba daya ka gama haihuwa fa?!" Ta qarasa fada kuka yana qwace mata. Wani malulun bacin rai ya taso ya saukar masa,donme zatace idan ya gama haihuwa fa?. "Ban gama haihuwa ba sabreen.......saidai idan kece zakiyi silar faruwar hakan" "Eh nice din.....nice hamma" Ta fada itama a fusace cikin gajiya da jin bayanansa. "Okay.....okay.......yanzu kika fitomin a mutum.....kin tabbatar min da abinda nake zargi kenan". " Ba zargi dama kakeyi ba.....kana cusamin laifin da bansan dashi ba......ko meye kake tunanin na aikata na aikata hamma!" Ta fada da wani irin kuka. "Don kin aikata sai me?,saboda kinga na damu dake?,saboda ina sonki.......saboda kina ganin bazan iya rayuwa ba tare da ke ba?........idan na daina sonki shikenan?" Ya fada da salon tambaya yana dage mata girarsa dukka biyun gami da bude idanunsa da suka sauya launi. Wani irin abu taji kaman an jibga mata a saman kanta. "Kana zaton nima bazan iya rayuwa babu kai ba?,bazan iya rayuwa ba soyayyarka ba?......ka daina sona din fine......sai me?" Ta fada da qarajin kuka. A gaggauce ta juya ta fusgu hijabin data cire dazu ta maida,ta juya ko wayarta dake kuwwa bata dauka ba illa jakarta data ajiye ta fice a dakin a gaggauce. "Kiyita tafiya.....zan iya rayuwa nima ko babu ke" Ya fada a birkice kaman wanda zai zauce. Komawa yayi ya fada saman gadon yana jin wani irin bacin rai yana saukar masa. Tayi masa laifi kuma sannan ta fishi fushi?,ya samu yara alhamdulillah amma arziqin da Allah ya bashi yana jin yana buqatar qarin wasu......yanason ya gina family din da aka jima ba'aga irinsa ba......yanaso ya gogewa maamah gorin yawan haihuwar da tace asali dangin babanshi na dashi,haifarsu su biyu da tayi daga jikin ubansu ne. Wani irin duhu da qunci dakin yaji yayi masa,tsahon awa guda da wani abu yana zaune guri daya batare daya ko motsa ba. Sake maida dubansa yayi ga sachet din maganin,ya saka hannu ya daga yana sake karantawa sai yayi jifa dashi wanda kai tsaye ya sauka a bakin qofa. Hannu bibbiyu ya saka ya dafe kansa yana jin yana wani sara masa,yaushe sabreen ta fara sha?,wanne lokaci ta dauka tana sha?,kada ya zamana ta illata mahaifarta fa?. Juyi kawai ya dingayi tsahon awa uku,sai daga bisani a hankali hankalinsa ya dawo gangar jikinsa,ya miqe ya shiga bandaki ya daura alwala. Saman abun sallah ya zauna yana karanta wasu addu'o'i hadi da sunayen Allah,A hankali sai yaji zuciyarsa tana saukowa tunaninsa yana daidaita. Sannu sannu sai komai daya faru tsakaninsu ya dawo masa fes cikin kanshi,wani sashe na zuciyarsa ya dinga masa zafi. Kwanciya yayi niyyar yi kafin ayi kiran sallar asuba,amma sanda ya isa gadon da zummar kwanciya sai maganarta ta fado masa. "Hamma na gaji.....bacci nakeso nayi". A nutse ya sauka daga saman gadon,ya koma saman kujera da nufin kwanciya,nan ma sai yaji ya kasa. Da daya da daya ya dinga sauya guraren kwanciya amma ko ina ya sanya kai sai yaji ya kasa,sannu a hankali ya fahimci zuciyarsa na neman 'yar uwarta ne.....zuciyarsa na neman mahadinta. Duk yadda yaso ga kafewa wajen fita nemanta amma sai zuciyar taqi bashi hadin kai,daga qarshe dai ya fahimci ba wata mafita da yake da ita illa ya fita ya nemo duniyarsa. Yana miqewa ana kiran sallar farko,don haka sai kawai yayi alwala,ya zura riga ya sanya flipp flops dinsa ya murza qofar zai fita a dakin. Farouq ya samu daga bakin qofar dakin "Yauwa dude......dan yiwa adda magana please ta miqo maganin fannah,jiya ta manta maganinta a jakarta duka biyun.....kasan ba'ason fashin shansa" Farouq yayi maganar hankalinsa yana wani gurin bai bada hankali ga fuskar fu'ad ba. Wani irin sanyi jikinsa yayi kaman an watsa masa ruwan qanqara,ya juya gwiwarsa a sabule ya koma dakin ya hada kan magungunan ya bawa farouq. Sanda farouq din ya wuce sai yaji kaman bazai iya sake taku ko guda daya ba,sai a sannan tunaninsa ya dawo,fannah tana shan maganin planning saboda matsala da take da ita a mahaifarta,dole take shan maganin sabida akwai buqatar ta huta sosai tsakanin kowanne ciki. Sam bai kawo hakan a ransa ba,ta yaya ma zaiyi tunanin maganin fannah zai shigo jakar sabreen?. Yana rangaji haka ya dinga takawa har yakai masallacin harami,daidai lokacin da ake dab da tada sallar,yayi raka'atanil fajr yabi jam'i aka tayar da sallar. Koda aka idar zama yayi yayi addu'o'i sosai,yayi istigfari akan zato da kuma yanke hukunci ba tare da bincike ba. Ya jima sannan ya miqe ya fara zagayawa guraren da yasan tafi zama ko zai ganta,amma har ya gama zagayensa ya koma duba guraren da ba wajen zamanta ba baiga koda me kama da ita ba. Zuwa sanda rana ta fito ya gaji sosai,dole ta sanya ya koma masauki. Ya samu yaran duka sun gama shiryawa,kowannensu kuma ummeensa yake da buqatar gani,musamman su fauzan dake jiran fitowarta su duba gifts da suka samu kafin su wuce harami. Baisan amsar da zai basu ba,saidai kawai ya zauna cikinsu ya sadaukar musu da wannan lokacin,amma dai duk da haka hankalinsu yana kan uwarsu. Har azahar shuru bata ba dalilinta,ga anni na nemanta,maamah ma da bata iya magana sosai sau uku tana tambayarsa. Zuwa la'asar hankalinsa ya tashi,don masu neman nata suna qara yawa ne,iffa ma dake da shekaru biyar neman ummenta takeyi bare sauran da suke da hankali. Ya kasa gayawa kowa abinda ya faru,yadai ce musu tana masallacine kawai. Sannu a hankali hankalin anni yakai kai,saboda yaran da suka matsa da qorafin taje ta dade a masallacin. Zaman jiransa sukayi har yaran sukayi bacci bai shigo ba,yana can yana dubata a ciki da wajen masallacin. Bai shigo ba sai daya baza masu duba masa ita,wai ko madeena ta koma daya daga cikin gidajensa?,saidai acan dinma duka daya ne bata koma ba ba wanda yaga gilmawarta. Nigeria ya karkata kiran nasa,tsakanin abuja lagos da kano,can dimma duka daya,don bata je musu ba. "Innalillahi wa inna ilahi raji'un" Kawai shine abinda ya dinga maimaitawa,a rayuwarsa wannan shine ainihin color din tashin hankali tsurarsa daya taba gani ido bibbiyu. Yana kallon wayarsa na ruri da numbers na anni da maamah,kowacce kiranta yana katsewa na 'yar uwarta yake fadowa,amma ya gaza daga koda yatsansa ne bare ya amsa musu. A jikinsa yake jin bazai iya komawa masauki ba,idan ya koma da anni da maamah da dukka yaran me zaice musu?,sai kawai ya wuce bandaki ya sake alwalarsa ya dawo gaban ka'aba yayi salla raka'a biyu ya sake istigfari sannan ya zauna ya durqushe yana roqon Allah cikin qanqan da kai da neman afuwarsa da agajinsa. *_NACE BA......._* *_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._* *_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_* *_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada munga ingancinsa_* *_Da yardar Allah saikin godemin_* *_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR GASKIYA KENAN AHTO_* Golden oud Hawi Sandal balls Sandal flakes Cotton bakhoor Kabbasine mix Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk) Deep crush (luxury khumra). Signature oil Kuleccham Kabbasine spray *_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_* *_PRIME SCENTS(the scents of royalty_* *KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN HANKALI* *SUNA NAN A* *_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road kano_* *BA'A KANO KIKE BA?* *_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a duk inda kike cikin aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_* *DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE* wa.me/+2348103155915 KO KI KIRATA TA NAN 08103155915 _Zafafabiyar_ 177 *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX _________________________ *_PLEASE FOLLOW MY TIKTOK PAGE_* https://www.tiktok.com/@huguma.closet?_t=ZM-8y1pf9yfIVZ&_r=1 Baisan adadin lokutan daya kwashe a wajen ba,baisan mutun dari nawa ne suka zauna suka kuma tashi ba a wajen. Har zuwa sanda ya soma jin wani siririn sautin kuka daga gabansa. Guri ne da mutane masu damuwa da buqatu kala kala ke zuwa,don haka baiko dago ba yaci gaba da abinda yakeyi,saidai kukan dayaci gaba da tashi ya fusgi hankalinsa don sautin Sabreen yake ji sosai. A hankali ya matsa zuwa gaba,ya kuma daidaita zamansa daidai da inda ta zauna. Jin mutum kusa da ita sosai ya sakata daga kanta,idanunsu suka gauraya dana juna,take kowannensu wani qaqqarfan abu dake riqe da zuciyarsa akan dan uwansa ya motsa. Fatali tayi da abun,ta kuma yi zumbur ta miqe kamar wadda cinnaka ya cijeta,saidai ko gama daidaita batayi saman qafafunta ba shima ya miqe,hakan ya sanyata ta fara hanzarin barin wajen,don tabbas inda tasan zai fito da tsakiyar dare irin haka ita ba zata fito ba. "Sabreen" Ya dinga kiranta da tausashiyar murya sanda suka fita a haramin gudun kada ya janyo hankalin jama'a kansu. Kaman ba zata amsa masa ba........amma wata raunanniyar zuciyar ta gaza jure jin yadda yake jera kiran sunanta da wata irin sassarfa wadda tafi qarfin tata tafiyar,saboda qoqarin tsere masa da takeyi sai data hada da gudu gudu. "Ki dakata sabreen". " Bana buqatarka" Maganar data cake masa a tsakiyar qirjinsa kenan. Bazai iya jure jin sake fitar wata magana haka daga bakinta ba,don haka yayi taku uku qwarara sai gashi a gabanta,baiyi wata wata ba kuma ya dagata cak kaman yadda ya saba yi mata. Ya raina jawota da hannu