← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 175 OF 215

Sashe 175

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Taku biyu tayi ta sake juyowa tana komawa bakin window din. Sake riqe wayar tayi sosai a kunnenta tana jin wani farinciki yana yawo da ita,jinta take tamkar a saman gajimare. Karon farko data fara kasancewa cikin sa'a a rayuwarta,karon farko data aiwatar da wani aiki da yazo mata da nasara ba a karon farko ba sai wannan.
"Komai kakeso zaka sameshi tunda har ka cikamin muradin raina,iya wannan nasarar daka tabbatarmin ta isheni farinciki......wannan yarinyar dake hannunku kadara ce.....kadara ce me girman gaske,kada kuyi wasa da ita har sai kun samu abinda kuke nema"
"Na sani hajiya,daga adadin abinda muka fara tambaya kuma muka samu tabbacin samunsu nasan munyi babban kamu,munyi kuma babban aikin da zamu fita daga talauci har abada".
"Qwarai da gaske" Ta fada tana jinjina kai.
"Ina yarinyar take?" Ta buqata ganin amna,ba bata lokaci ya juya kiran video call ya kuma haska masa amnar.
Tana ya she tun sanda suka sheqa mata abun bata dawo hayyacinta ba. Baki ta tabe
"Wai wannan abarce zata cakuda jinina da nasu?....kuci gaba da aliyarta.....tabbas sai na sanya sunyi nadamar hada hanya dani da kuma sanina koda sau daya ne a rayuwarsu" Ta fadi tana dauke idonta daga kallon amna.
Kiran ta katse tana sake murmusawa,idanunta kan farfajiyar gidanta.
"Wannan wasan zaiyi dadin kallo.....zan samu farinciki matuqa idan naje idanuna suka ganemin jigatar da ahalin alhj hamza sukayi tsakanin jiya shekaran jiya da yau" Ta fadi a ranta,sai kawai ta fada wanka.
A nutse ta shirya cikin qasaitaccen lace,lace ne na alfarma da ita kanta a jininta tasan ba qananun kudade fu'ad ya sanya ya siya mata shi ba.
Laluba ma'ajiyar sarqunanta tayi,duka gold sun qare sai fashions masu tsada. Su ta sauko ta zuba tsakanin hannuwanta wuyanta da kuma kunnenta,ta bade jikinta da turare,ta kuma dauko tsadajjen mayafinta mahadin lace din ta yafa.
Tunda tazo gidan taga yadda anni da musaddiq ke a birkice idanunta basu huta da zubda hawaye ba,ba iyasu ba.....hatta saddiq dimma da hudan gaba daya. Sak gidan ya koma musu kaman gidan makoki,sauqin abun daya duk an sallami kowanne baqo ba tare da an bari ya fahimci komai ba.
Duk yadda anni keji daga qarshe ita ta koma lallashin sabreen,wani irin abu takeji daya kasa tsarga mata,qaqqarfan zato da zargi maras iyaka dake mata kai kawo,wanda tayi imanin wannan karon komai ya kawo qarshe muddin ya tabbata abinda take zato dinne.
Chapter 175 · 0% Book details