← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 215

Sashe 57

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kwabar data fara mata. "Da kinason gayawa fu'ad me?,ya saki yarinyar?,kada ya amince da ita?,kada yaci abun hannunta?,bayan ke kika aura masa ita?,ke kika bashi tabbaci akan ingancinta da kuma cancantar aurensa da ita?,bayan ko sati biyu ba'ayi ba ke dindai ke kika kafa masa sharadin ya bata kulawarsa?,ya sota?,ya jata a jikinsa?,kinason dabawa kanki wuqa?,kinason sanya wani zargin saman zargin dake kansa naki?". Wannan tunanin ya sakata sakin ajiyar zuciyar tana kiran number da tazo kai,a gefe guda tana mamakin abinda ya hana hajja nemanta ko zuwa gurinta ko tuntubarta akan matsalar da ta shaida mata jiya,TABBACIN DUKKAMIN MAGANGANUN LAILA BA QARYA KO SHAKKA AKAI KENAN. Sai taja qwafa tana gyada kai "Duk wanda yaci tuwo dani miya yasha" Ta furta a bayyane,daidai sanda taji an murda qofar dakin an shigo laila ta bayyana. Da kallo tabi lailan har zuwa sanda ta qaraso gabanta. Ta durqusa saman gwiwoyinta wani abu da bata taba yiwa maamah shi ba duk da matsayinta na qawar mahaifiyarta shekara da shekaru. "Ina kwana maamah" Ta furta cikin tsantsar ladabi har bata iya hada idanunta da nata. Kai ta daga ta kalleta,dukka wani bayanin plan nasu da lailan tayi mata jiya sai ya shiga dawo mata kanta tar tamkar a lokacin take labarta mata. Wani bacin rai da radadin da wanda akaci amana keji ya taso mata,sai ta maida kanta ga waya kawai tana tura masa saqo. Sai data tabbatar saqon ya shiga sannan ta kalli laila,wadda kafin lokacin duk wani kalar tashin hankali laila ta shigeshi. Tana jin kamar ta dora hannunta aka ta yita zunduma ihu,iya yadda maamah taqi amsa mata gaisuwa ya sanyata cikin firgicin kodai wani laifi tayi mata?. A yanzu a rayuwa bata jin akwai wani abu da zai daga mata hankali sama da taga fushin maamah.....ko kuma tayi wani abu da zai saba umarninta. "Lafiya qalau....." Amsa matan kawai da tayi ya sanyata sakin wata sassanyar ajiyar zuciya,tana godewa Allah da ba wani abu tayi daya bata mata rai ba. "Na shiga dakinki naga basu shareba.....na gyara miki,saiki duba idan akwai abinda baiyi ba ki gayan a sake gyara mikin". A nutse take qarewa laila kallo,ji take a ranta inama ace fu'ad ne haka a gabanta yake wannan bayanin bawai laila ba?,inama ace aikinta ya fada daidai?,i yanzu da batasan wanne irin farinciki take ciki ba.....lallai da zata kasance wata halitta mafi farinciki a fadin duniya,ta qarasa wannan tunanin tana runtse idanunta gami da budesu. "Basai na duba ba,saidai anjima kafin na kwanta ki sake" "To ba matsala.....waida so nake naje wajen hajja.....jiya muna magana bamu gama ba kika kirani" Kai ta girgiza,duk da tanason sake samun information,don tayi imanin duk abinda zasu tattauna tamkar a gabanta za'a yishi,to amma kuma tana buqatar ta kammala da aikin sabreen tukunna......tabbas komai da zai biyo baya me sauqi ne. "Ki kirata ki gaya mata nace ba yau ba,zan duba gobe na gani idan ya dace kije goben" Ta fada kanta tsaye tana ci gaba da riqon wayarta cikin jiran tsammanin shigowar kiran hanzari nan da kowanne lokaci. Sanda laila ke gayawa hajja saqon maamah kai tsaye murmushi ta saki bayan sun gama wayar tana jinjina kai "Mariya!.....Mariya,zan miki babban karatun da gogewarsa sai a cikin kabarinki,a sanda qasusuwan mowacce halitta ta jikinki ta gauraye da qasa,kin bani qofofi masu yawan gaske ba tare da kin sani ba.....zan shiga ta kowacce qofa......na fita ta kowacce qofa.....na shiga kuma cikin rigarki na dimauta duniyarki......sannan na hana muradinki da mafarkinki su zama gaskiya" Abinda ta fada kenan tana qurawa wayarta idanu dake aje tana ta burarin nemon taimakon a daga kiran daya shigo. Tun safen har azahar zuwa la'asar da tayi dukka cikin dakon shigowar kiransa take. Sai bayan la'asar din liqis cikin ba zata daya daga cikin masu aikinta suka shaida mata tana da baqo me suna hanzari. "Ki rakoshi can cikin setting room,kada a barshi a waje" Ta fada cikin doki da zumudi,ta miqe tana daukan dankwalinta ta maida kanta,har ranta tana jin mafita tana tunkaro ta. Fitowarta ya sanya hanzari sauke qafafunsa da suke dore daya saman daya. Sanye cikin baqar shiga,wandon jeans da shirt dukka baqaqe,sai baqar hular Ascot cap daya jawota tadan rufe fuskarsa kadan. "Barka da fitowa" Yayi maganar yana miqa mata nannadaddun takardun dake hannunsa,sai ta fasa zama ta sanya hannu ta karba sannan ta zauna dasu ta soma budewa tana cewa "Aiki dakai akwai jan kudi.....amma kuma akwai hanzari kamar yadda sunanka yake" Ta fadi a nutse tana bin list na sunayen da kallo da kuma hotunan. Sai data gama qare musu kallo tas sannan ta kaudasu daga fuskarta tana kallonsa "Kin gansu hajjaju?" Ya rigata fada,sai ta gyada kai ranta yana yin fari. "Kayi qoqari sosai hanzari.....amma waye kake ganin ya dace mu dauka?" Ta fadi maganar tana sake kallon list din. Matsowa gaba yayi kadan ya miqa mata hannunsa yana cewa "Kawo nan ki gani" Ba musu ta miqa masa,ya aza takardar saman teburin dake tsakaninsu yana binsu da yatsa daya bayan daya,kafin daga bisani hannunsa ya tsaya daidai fuskar mashkur,sai ya daga kai yana kallonta. Duk da baiyi magana ba bai kuma ce komai ba amma maamah ta fuskanci abinda yasa gaba da abinda yake nufi. Sai ta zuba masa idanu tana sauraron qarin bayaninsa. "Wannan shine mashkur......dan tsuntsu me wayo kenan..." Yayi maganar yana sake xuba yatsunsa saman fuskar mashkur. Sake jan hoton gabanta tayi,tunda ya aje din dama kusan fuskarsa tafi jan hankalinta. Yana da kyau daidai misali,wanda zaiyi daidai da plan dinsu,ta jinjina kai tana duban hanzari "Yayi......a tsara komai.....amma karka manta,secretly" Ta fada tana nuna hanzari da yatsa. "An gama" Ya furta yana murmushi. *FAREEDA* Ci gaba tayi da duba bayanan,murmushi yana sake wanzuwa saman fuskarta. Murmushin da takejin yana gauraya da farinciki da take da yaqinin zai zame mata tabbatacce ta hanyar samarwa da zuciya da ruhi abinda sukesu ta sassauqar hanya. Sake bude shafin qarshe na takardun tayi,take hotonta ya mamaye screen din tab din nata gaba daya,shafin qarshen daya zama shine na qarshe data bude cikin dukka bayanan data samu. Ta barshi a qarshe ne saboda dukka sauran shafukan na dauke da full details da bayanan da suka faranta mata rai sosai,sukayi kuma daidai da muradinta. Hoton sabreen din daya cika allon tab din ta zubawa idanu. Wani abu yana tsarga mata tun daga tsakiyar kanta har zuwa tafukan qafafunta. Wani mahaukacin wutar kishi ke ruruwa cikin zuciyarta. Ta kusa kwashe sakanni talatin a haka,kafin ta dafe dukka hannuwanta saman kujerar da take kai tayi zullo zuwa gaba har a sannan ta gaza dauke idanun nata. Labbanta suka motsa kadan rana son kiran ainihin sunan nata,saidai ya tsaya ne can qasan maqoshinta ba tare da sautin harafin ya fita ba. Adan hanzarce ta maida hannunta saman tab din tana komawa shafin da yake da alaqa da komai daya shafi sabreen din,ta sake karantawa sosai kamar me shirin haddace komai daya shafeta "How comes?" Ta tambayi kanta tana yamutse fuska lokacin da takai qarshen bayanan "Karuwa?......How did he get married to her?" Ta sake tambayar kanta da kanta "She's karuwa officially fa?" Ta kuma nanatawa cikin zallar mamaki. Ba wata amsa data samu daga kowanne sashe na kwanyarta,saita dage kafadunta duka biyun sama tana sakin murmushi,lallai komai zai tafi da alama daidai "Fu'ad isn't your type madam.....its over between you too" Tayi maganar tana nuna hoton sabreen da dan yatsa,saidai ba abinda ya canza zuciyarta daga mahaukacin kishinta da takeji. Ta kowacce fuska,ta kowanne bangare sabreen din ta yaga mata indai ana batun kyau ne da sassanyan zubi da ta tabbatar yana daya daga cikin abinda ya fusgi hankalin fu'ad din,banda hakan.....yadda ta samu full details dinsa zai wahala ya nuna interest akan karuwa har ya aureta. "It's my turn......my time to shine has come" Ta fada da qwarin gwiwa,ta miqe tana nufar closet dinta ta sauke luxury luggage dinta guda daya ta fara s electing kaya tana shiryawa a ciki ba tare da jiran kowa cikin masu aikinta ba. Cikin qasa da mituna sha biyar ta gama packing komai da komai nata,sannan ta dawo ta dauki wayarta ta kira number abbanta. "Hello dad....." Ta fada a shagwabe. Ita din 'yar gaban goshinsa ce da dukka yaransa babu wanda ya kamo matsayinta a zuciyarsa. A kullum tana maida kanta tamkar 'yar shekara goma a gabansa,haka shima yake biye mata,saidai hatsabibancinta da girman izzarta ta dara tashi shi da yake da muqamin ambassador din gaba daya. "Dad.....ayimin booking flight please......gobe nakeso if possible,it's an urgent dad..." Ta furta a shagwabe kamar yarinyar dake tsakanin shekara shida zuwa bakwai "Thank you dad" Ta fada da murnarta jin ya bata tabbacin zaisa a mata booking private jet. Da murmushi sosai a fuskarta ta soma turawa zababbun qawayenta da za'ayi tafiyar tare dasu request. Cikin qasa da minti goma ta gama komai,sai ta sauke wayar ta matsa gaban dan wani madaidaicin table dake dauke da tukunyar shi sha ta fara qoqarin hadata. Tanajin a yanayin da take ciki na farinciki ita daya zata tayata sarrafa murnarta, Kyakkyawar zuqa tayi mata tana bulbular da iskar daga dukka qofofin hanci da bakinta,ta lumshe idonta fuskar sabreen na mata shawagi tsakanin tunaninta da qwayar idanunta "Blast it!" Ta fada da qunan zuciya tana kaiwa iska naushi,tana jin kaman tayi using acid ta dauke wannan kyan da ya hanawa zuciyarta sukuni. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Daga dariq dan shihab RA,manzon Allah S A W yace "juma'a haqqi ce kuma wajibi akan kowanne musulmi yayita cikin jam'i,sai akan mutum hudu kawai(ta sauka),MACE,BAWA,YARO DA MARA LAFIYA"_ _Abu dawud ne ya rawaito_
Chapter 57 · 0% Book details