Sashe 136
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
da bata muddin kinaso ta rayu yadda ya dace" Ya fada yana jin yadda bugun zuciyarsa ke daduwa daga yadda take yamutsa sumar kansa kawai. "Zaka samu sabreen fiye da yadda kake fata.....zaka samu dukkan wani cikar burikanka a tattare da ita.....harma abinda tunani bai taba baka ba". Maganarta ta tsumashi sosai,ta kuma sakashi daga kanshi daga cinyarta. Idanu ya zuba mata sosai yana kallon qwayar idanunta,sai itama ta samu kanta da mannewa kallon nasa,kafin ya miqe a hankali tsaye a gabanta. Hannuwansa ya miqa mata,sai itama ta aza nata ciki ya tashe tsaye sannan ya buda qirjinsa ya sanyata a ciki ya maida hannuwansa ya lullubeta da kyau. Ajiyar zuciya ce ta subuce masa,ya kwantar da kansa saman kafadarta. "Sabrrrrr........kinsan kin bani wata kyauta da ba wani dan adam daya taba bani makamanciyarta?" Ya soma da jefa mata tambayar data kasa gane ma'anarta. Shurunta ya fahimtar dashi cewa ya sanyata a duhu,don haka ya zare jikinsa a hankali sannan ya juyata ya rungumeta ta baya yana sake nutsata sosai cikin jikinsa. A tausashe ya dora duka tafin hannunsa saman mararta,ya dora habarsa saman kafadarta yana saka tausasan labbansa saitin kunnenta. "Sabrrrrr......you're pregnant......ciki ne dake,cikin muhammad jadda......zaki zama uwar 'ya'yana ameenatu". Wani irin abu ne ya tsarga mata tun daga tsakiyar kwanyarta har tafin qafarta,bugun zuciyarta ya qaru sosai. Samun kanta tayi da saka nata tafin hannun saman nasa dake mararta tun dazun,ta kasa fadin komai,don duk kalmar data kamo sai taji ta qwace mata,tana ci gaba da sauraren saukar numfashinsa cikin kunnenta. "Are you happy sabrrrrr?" Ya tambayeta a raunane yana fatan ya sameta cikin irin yanayin da yake jin kansa shima. Kai ta gyada a sanyaye,tanajin wani irin yanayi yana ratsata,mamakin yau itace wai dauke da ciki?,itama zata zama UWA?,zata haifi d'a ko 'ya a cikinta?,abun kamar cikin mafarki. "Alhmdlh" Ya fadi yana sauke mata tattausan kiss a wuyanta,a hankali kumya ja dawo da ita tana facing dinsa sai ya rungumeta tsam a jikinsa. Shuru ya ratsa tsakaninsu na sakanni,tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa ta cikin kunnuwanta dame kwance a qirjinsa,sosai kaman akwai wani abu dake taba zaman lafiyarta,kusan minti biyu sannan ya sauke sassauqar ajiyar zuciya a sanyaye sannan ya dagata daga jikin nasa yana kallon fuskarta. Qwayar idanunta ya laluba ya saka nashi a ciki,da wani irin coolness ya sake kiran sunanta. "Kinji yadda zuciyata take bugawa ko?" Ya jefa mata tambayar yana lalubar tafin hannunta ya matse gam cikin nasa. Kasa amsa masa tayi da baki sai kai data gyada mass,saboda cikin idanunsa abubuwa ne masu yawa ta gani suna yawo. "Sabrrrr.....na gode da kika karbi ajiyata da sauri haka......inajina kaman ni kadai nake rayuwa cikin duniya......ashe rashin haduwa da tawa DUNIYAR shine sila......sabrrrr......bansan dame zan saka miki ba......bansan kuma da meye zan gode miki ba....kome na kalla sai naga kamar yayi kadan,alfarma daya kawai nakeso ki yiwa rayuwata. Kallonsa da kalamansa gaba daya qara kashe mata jiki sukeyi,mamakin irin tsananin son da yakewa yara ne yake sake kamata,ta motsa labbanta a hankali "Tame?" "Kiyimin alqawari zaki rayu dani....kiyimin alqawari ba zaki taba rabuwa dani ba.....kiyimin alqawari zaki zauna dani,da dadi ko babu.....cikin wadata ko talauci.....sabrrrr kiyimin alqawari ba zaki taba tafiya ki barni da yara ba.....zaki zauna dani dasu a duk yadda nake ko suke,mu rainesu tare.......kiyimin wannan alqawarin sabrrrr cikin wannan garin me tsarki". Idan ba qarya idanunta sukayi mata ba hawaye ne kwance cikin idanun muhammad jadda din......taja numfashi sosai har kaman kayan cikinta zasu hade waje daya. Ita daya ce mutum na farko a duniya data taba ganin wadannan tsadaddun hawayen da suke zuba SILAR QAUNA daga idanun me jadda......tana fata ta zama mutum.na qarshe da zata gansu,kuma ta zama sila na goge hawayen daga idanunsa gogewa ta har abada. Abu daya ta lura dashi har yanzu yana da tsoro game da halin mata......har yanzu wannan ciwon da maamah ta dasawa rayuwarsu yana masa zugi da radadi.....har yanzu yana jin kaman abinda ya faru da abbansu zai faru dadshi,a yanzu haka a shirye take ta goge masa dukkanin wannan fargabar da shakkun,don haka ta zame hannuwanta daga nashi,ta sulale tana duqawa saman gwiwoyinta,sai ya gaza tsaiwa ya silale shima ya bita. Hannuwansa ta riqe da kyau tana kallonsa cikin tsakiyar idanunsa. "Allah ya zama shaida.....annabin Allah ya zama shaida,ni ameenatu sabreen na shirya rayuwa dakai da dukka abinda zamu haifa......na sadaukar maka da dukka rayuwata sadaukarwa ta har abada......dadi ko wuya sunyi kadan su raba tsakaninmu.....zan zauna dakai tamkar dominka kadai aka halicceni,bazan barka ba muddin bakai ka buqaci hakan......". Ai bai iya barinta ta qarasa fada ba ya hade bakinsu guri guda. Sai daya tabbatar ya kwashe ragowar maganar tass daga bakinta sannan ya zare bakinsa daga nata yana kallonta da birkitattun idanunsa. "Ta yaya zan iya rayuwa ba'a duniyata ba?.......ta yaya dan adam zai rayu babu duniyarsa?,indai babu ta yadda hakan zata kasance....to ki sanya a ranki ni Muhammad jadda don ke kadai MAAMAH ta haifeni". Batasan sanda ta zube saman kafadarsa ba tana jin wani irin alfahari yana ratsata,tana jin tabbaci da yaqini suna ratsata.....ashe akwai sauran maza irin muhammad jadda din?. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ 117 117 Guri kawai ta samu ta zauna cikin dakin daya kasance ita daya ce qwallin qwal a ciki. Duk yadda taso ta cinye ta kuma jure ta kasa,bata ankara ba kawai taji ta fashe da kuka. Ta yaya haka zata kasance?,bata tsira da komai ba sai hawan jini?. Wanne irin kafaffen yaro ta haifa?.....aure tsakanin musaddiq da amna?,wacce irin asara ke bibiyarta har haka?,da gaske kamam yadda boka ya gaya mata taurarin nasararta ke bacewa?,taurarin nasararta ke dakushewa?,ina dukka kaifin hankalinta da zallar iya takunta suka tafi?(ta mance cewa shi Allah gwanin hikima ne,yana iya yiwa bawa talala,yayi shekaru aru aru yana zalinci,a nasa hangen da tunanin nasara ce,sai Allah ya barshi da wayonsa da tunaninsa,ya turo.masa nasara a gabansa,plan dinsa yayita tafiya daidai,kwatsam idan yaso kamashi zai da damqeshi a tsakiyar wannan plan din da shirin nasa da yake tunanin sune mafita a gareshi,sai ya zurma yayita bundum bundum. Idan yana da rabo sai ya gane zunubansa da kuma kusakurensa yayi gaggawar tuba....idan baida rabo kuwa,zaiyita ganin INA DA SAURAN DAMA,INA DA SAURAN LOKACI yana tsaka da wannan lissafin sai ubangiji yayi ram dashi,dauri gaba dauri baya,me kwanceshi kuma sai ubangijin daya qulle abinsa. Duk runtsi.....duk tsanani,duk yadda za'a je a dawo karka yadda ka cuci kowa,daka cuci kowa gwara kowa din ya cuceka. Duk juyin da za'ayi ka tabbatar zuciyarka wankakkiya ce......kana bacci amma sai ubangiji ya zama jinka ya zama ganinka,ya zama me jagorantar al'amuranka,ubangiji ka barmu a naka duniya da lahira,karka bari duniya da abinda yake cikinta ya rufe mana ido don girman zatinka,karka bamu damar cutar kowa don isarka Abune a rayuwarta data manta rabon data yishi wato kuka,shekaru masu yawa da suka shude mata,amma sai gashi yau tana zubda hawaye sanadin anni amna da sabreen. "Lallai dole fansa ta biyo baya.....lallai dole ku biya bashi da fansar zubar wadannan hawaye......dole sadaukarwa ta biyo baya.....wala'alla akwai rayuka da zasu salwanta......rayukan da shudewarsu shine silar wanzuwa da samun nutsuwar zuciyata" Ta fadi a fili tana kallon idanunta da suka tasa saboda kukan data share mintuna tana yi. A gaggauce ta sake goge fuskarta ta,sannan ta koma wajen luggage dinta ta soma ninke kayan ciki tana zuba wadanda suke gefen gado da kuma cikin toilet din dakin. Tanajin ta qagauta gari ya waye,tana jinta.kaman saman qaya,a jikinta da ruhinta takejin bata da wani sauran zama a garin,bata da sauran abinda ya rage mata da zata zauna tayi cikin qasar(subhanallah).