Sashe 77
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shi kansa baisan yana yi ba,jifa jita take satar kallonsa,har a sannan kuma ta tabo sabreen "Adda........wai dama haka hamma yake da kishi?,daga cewa you look familiar?.....haka hamma yake sonki?" Ta fada tana murmushi kaman abun yana burgeta. Sau daya tak ta kalli fuskarsa sanda yake fama da system dinsa,saita maida idanunta ga window din jirgin tana duban yadda suke dai da daidai da gajimare. Abun yana burgeta,tunda shine karon farko data fara keta hazo......saidai can qasan ranta yana cunkushe da halayensa. "Ba kishi bane.....izza ce wulaqanci da kuma izgili.....har yanzu banga wani kyakkyawan halayensa guda daya ba......koma dai meye saura kwanaki kadan suka rage na barshi shi da halinsa dama tarin dukiyar dake sanyashi dagawa izgili da girman kan ma" Tayi dukka maganar a ranta,amma a fili murmushi kawai ta yiwa amna. Amnan bata damu ba taci gaba da dauko mata gulmarsa kadan kadan,tunda ta saba da halinta na wannan fannin. Ba komai sabreen din ke bude baki ta bada amsa ba a maganganu da dama. To a yanzun da yake tsaye a gabanta bata dubeshi,sam bata qaunar hada idanu dashi. "Ko meye zakiyi a yanzu ki dinga tunawa akwai igiyata a kanki......bazan kuma lamunci kowanne abu da zai zama tozarci ga igiyata ba......zan iya daukan kowanne mataki mara dadi muddin kikayi wani abu daya sabawa shari'a......ki kula,ki kula da kyau". Kasa jurewa tayi,haka siddan daga saukarsu a qasar,kowa ya sauka da walwala itama ta samu ta fara tattalin tata zai watsa mata ita. Fararen idanunta ta daga ta watsa masa wani.kallo tsakiyar idanu. Wani haske suka fitar sosai saboda fushin dake cikinsu,wani salon kallo da baiyi kama da harara ba,shi kuma ba kallon banza ba. Ta motsa siraran lips dinta zata ce wani abu,sau kuma taga hakan baida ma wani fa'ida......bata da sauran lokacin batawa,don haka ta soma qoqarin rab'eshi ta fice. Sosai taji an damqi hannunta da wani tsatsauran riqo,ta waiwayo da hanzari tana dubansa,ya damqeta ne ba tare da ya ko waiwayo ya kalleta ba,qeyarsa kawai take iya gani,da hannu daya ya jawota ya dawo da ita gabansa,ya sanyata a tsakanin idanunsa yana mata wani irin kallo da taji ya tsaye mata a sassan jikinta,ya kuma soma sauke rashin kunyar da taji tana taso mata "Duk sanda kika sake gangancin wuceni ina magana.....na rantse da Allah sai na gwada miki ina da banbancin da lusaran mazan barikinki marasa daraja......dole ki amsa min kowacce magana kaman yadda nakeso.....don banajin muryarki tafi tawa tsada ko daraja.....ko banza adadin mazan da sukaji muryarki baikai adadin matan da sukaji tawa ba......kinjini?!" Ya furta da dan tsauri idanunsa na kallon wani gurin daban sabanin cikin idanunta "Eh naji" Ta amsa a sanyaye kanta yana kallon qasa. Shigowar farouq ta gani daga bayansu,wanda ta tabbatar shi bai gani ba,sai ya sakar mata hannun yana juyawa gami da takawa a hankali yana ficewa a jirgin. Hawayen da take riqewa ne suka yiwa kansu da kansu hanya. Ta sanya tissue tana daukesu "Ya isa......ya isa" Take gayawa kanta da kanta. Tana cin alwashi a ranta ko ya bata takardarta.....ko bai bata ba,sauna sauka a nigeria zaman aurensu ya qare......ko ya sallameta ko bai sallameta ba wannan duka damuwarsa ce,alwashi ta ciwa kanta.....wannan karon babu abinda zai dakatar da ita......ba kuma wanda zai hanata. A hankali ta fara takawa itama tana nufar qofa da shimfidadden matakalar da aka jinginewa jirgin. A nutse take sauka tana qoqarin daidaita mode dinta gudun saka damuwa a zukatan amna da anni. Three pieces turkish gown ne a jikinta,wadda take hade da strips skirt da kuma blouse data zauna daidai jikinta,tayi kuma took in da ita kaman yadda tsarin kayan yake,sannan ta kawo doguwar gown din kayan me budadden gaba data sauka har qasa ta kuma bude sosai daga qasan. Qafafunta high hill ne masu madauri da suka dace da kalan rigan. Sosai kayan suka karbeta,baka ganin komai sai fuskarta,zaka rantse da Allah bata hada nasaba ta kusa ko ta nesa da nigeria ba. "Wallahi anni adda sabreen kyau takeyimin......komai nata me kyau ne.....duk kayan data saka sai naga kaman don ita aka yisu" Ta fadi maganan tana matsawa kunnen anni,saidai fuad dake tsaye daura dasu yaji abinda ta fada din. Haka kawai ya samu kansa da daga kan nasa,suka kuma yi masa jagora a kanta duk da yadda yake qoqarin hana hakan faruwa. A kasalance take tafiya saboda bacin rai,sai hakan ya sake zama kaman cikar adon tafiyartata. Idanunta suna lumshewa kadan gami da bude kansu duk a qoqarinta na hana zuciyarta karyewa,ta kuma hana idanunta zubda ruwan hawayen da takeji suna tattara kansu. Amna dake mata murmushi ta maidawa martanin murmushinta,abinda ya sanya pink lips dinta motsawa kadan. "Ya salam" Ya fada can qasan ransa saboda tsigar jikinsa da yaji ta zuba yarrrr.....tun daga tafin qafarsa har zuwa tsakiyar kansa. Wanccan ranar ya tuna.......ranar daya sanya lips dinsa saman nata......shi.kadai yasan me yaji,shi kadai yasan yadda ya iya qwace kansa daga yanayin daya shiga......yayi imani a ranar inda ace shi din manemin mata ne,baisan adadin mata nawa zai nema ba a ranar.....inda shi mashayi ne,baisan adadin kwalba nawa zaisha ba......inda ace shi din asharari ne bayajin cikin kwana uku ma wata macen zata sauke masa abinda yaji a jikinsa a wannan lokacin. Bayajin zai iya ci gaba da tsaiwa a wajen bare ta fahimta ko farouq ya gano canzawarsa,don haka sai ya juya kawai yana takawa a nutse yana matsawa daga wajen gami da sake kame kansa da kyau gudun zubewar kima. Dukkaninsu motar da tazo tararsu ta dauke,mota ce me seat kusan hudu bayan wajen hutawa daga can baya. Shi da farouq suna seat guda,sabreen anni da amna suna set na qarshe. "A ina ka samar mana gida?" Fuad dake gyara agogon hannunsa ya tambayi farouq. Takardun hannunsa ya fara budewa daya bayan daya kafin yace yana tsaida idanunsa akan wata takarda guda daya. "RANGALI ISLAND RESORT......garden villa na masa mana gida.....baiyi tsada cancan ba,duk da Maldivian Rufiyaa mukayi cinikin,ahmad ne ya siya gidan ta hannun wani,da nayi converting kudin da naira sai naga basuyi yawa ba" . Kai kawai ya jinjina,farouq akwai iya aiki,musamman idan akazo batu na tafiya tourism. "Ina fatan yalwatacce ne,kasan mun sake qaruwa this time?". Idanu ya zuba masa,kaman yace masa waye ya qarun da sukayi yawan da zaa nema bangajejen gida?,amma sai yaga kulashi ma bata time da plan ne,don haka ya bishi da " Yes" Kawai farouq yace masa yana boye dariyan dake qasan ransa. Idanunta akan hanya sanda suke wuce lafiyayyun hanyoyin da suka sha banbam dana qasarmu nigeria. Ko daga iya nan ta tsaya ta tabbatar wata duniya ta daban ta shigo. Ta shigo wata duniya da tayi nisa qwarai da tata DUNIYAr data rayu cikinta. Qarfi da yaji takeson komawa 'yar qauye,ta sauke nannauyan ajiyar zuciya sanda motarsu ke shiga wani street me dauke da lafiyayyar hanya da wadatar tsirrai. daga gefe da gefan hanyoyin tana iya hangen ruwa can nesa dasu,wani irin ruwa dake bada blue colour,bata sani ba.....color dinshine haka ko kuma 'yar tazarar dake tsakaninsu take nuna mata haka. Daidai qofan wani madaidaicin kyakkyawan gida motar ta fara slow kafin ta samu wajen tsaiwa. Su suka fara fita suka jira fitowar anni,sannan ita da amna suka biyo bayanta. Tare suka jera da farouq har qofan gidan su kuma suna biye dasu,jordan da drivern motar suna biye dasu da luggage dinsu. Dab da zasu isa qofan gidan qofar ta bude da kanta. Farin matashi ne ya bayyana wanda duka duka shekarunsa ba zasu haura talatin da takwas ba,daga gefansa musaddiq ne da suka jero tare,wanda kamanninsa da fuad ta wasu bangarori da yawa suke bayyana kansu. Yana sanye da jeans da shirt yayin da musaddiq jikinsa ke sanye da jallabiyya saqar marocco,kansa kuma akwai qaramar hular da mukafi mata laqabi da tashi ka fiya naci haka ma mutumin dake gefan musaddiq din. Akwai haske sosai saman fuskar tashi dake bayyana musulunci tattare dashi. Da sassarfa musaddiq din yake qarasowa garesu,idanunshi duka suna kan anni,yana isowa gaban nata baiyi duba da wani girmansa ba,ya bude dukka hannayensa ya rungume annin yana fadin "I missed you so much anni......sai naji kaman ba zakuzo ba.....kwana biyu kawai amma sai naji tayi nisa" Murmushin dake shimfide kan fuskarta kadai ya isa ya gaya maka farincikin dake ranta na ganinsa da tayi,zallar qauna irin wadda ba kasafai ake samunta wajen wani ba idan ka dauke uwa. "Kayi nisan kiwo yaro na......ka tayani roqon hammanku kada ya sake daukemin kai har haka" Ranqwafowa yayi wajen fuskar annin,yana yin qasa qasa da muryarsa don kada fu'ad yaji "Na rantse anni nima bazan sake yarda ba.....ki jawa danki kunne" "Kai kai......hamman?,ai kuwa kaman a kunnensa" Amna data zuro musu kai ta fada tana raba idanu. Duban amna yayi yana dan yamutsa fuska "Bama haka dake auta......kinsan ni dake duk muna together" Ya furta yana daga mata yatsunsa biyu cikin salon son samun goyon bayanta. Fuska ta shagwabe tana cewa "Zan iya haqura nayi shuru idan tsarabata tafi ta kowa yawa" Tayi maganar tana kashe ido daya sannan ta dora "Idan kuma ba haka ba.....ga addana a gefe,ita zan gayawa ta shaida masa abinda kace da mijinta" Ta qarasa maganar tana nuna sabreen da yatsa. Sai a sannan ta lura da sabreen din dake gefansu. Ya dora idonshi a kanta yana dan kafeta da kallo na wasu sakanni. Sosai yaji yasan fuskartata,ba yau ne ranar farko daya fara ganin fuskar ba. Cikin qasa da second biyar ya tuna inda ya santa. Tabbas bazai taba iya mantawa da fuskar ba.....fuskar data dinga fada saboda lafiyar anninsu.......fuskar data zama silar ceto rayuwar anninsu,to amma kuma sai yaji kaman bai kamata farat daya haka a matsayinsa na baquwar fuska a gareta yayi gaggawar tuhumarta inda ya santa ba.....ballanta ma ita din da take matsayin yaaya a wajensa. "Tuba naki adda.....ayimin aikin gafara.....da gaske hamma baida dadi shi yasa takeson hadoni dashi" Ya fada yana hade hannayensa duka biyu waje daya. Batasan ya akayi murmushi ya qwace mata ba,murmushin daya afku saman idanun fu'ad dake dan nesa kadan dasu yana karbar takardu hannun ahmad tare da sake karbar wasu bayanai,don tuni farouq ya wuce cikin gidan yana sake duba yanayinsa. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 Wani abu ya hadiye da baisan meye