Sashe 126
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kan sabreen data iss gaban maamah ta tsugunna tana gaidata. "Allah yasa qwallonka ne ya fada a raga......zanso naga first born na gold runner" Sosai maganar taja hankalin fu'ad,sai ya kasa cewa farouq komai yadai bishi da kallo. Zuciyarsa bugawa takeyi so fast amma yanason dakatar da ita. Bayason maganan farouq ta masa tasiri,ya tasirantu da cewa shine kuma bashidin bane. Sautin dariyar maamah a sanda take tsugunne gabanta tana gaidata shi yaja hankalinta,ta daga kanta a hankali ta kalleta. Qaqqarfan murmushi takeyi da gaske wanda yafi kama da dariya "Kin gama naki......ni kuma zanyi nawa" Abinda tace da ita kenan kawai tana maida kanta ga wayarta. "Tashi kije yarinya" Hakanan ta samu qwarin gwiwar aje mata murmushi itama sannan ta yunqura ta miqe tana fadin "Hasbunallahu wani'imal wakeel,ni'imal maula wa ni'imannasir". Da kallo maamah ta bita sanda take takawa tana barin wajen. Ta aje mata shakka sosai cikin ranta,ta sani itadin kuma shaida ce,ba kasafai murmushin yarinyar yake xama alkhairi ba,so amma koma meye wannan karon ta shirya kawar da ita me gaba daya idan ta kama ayi hakan. Amna ce ta rugo da sassarfarta ta kawo mata runguma,abinda ya kusa sabbaba faduwarsu gaba daya,Allah ya kawoshi ya sanya hannu ya tareta ta fada hannunsa. "Ki kula" Ya fada adan dake sannan ya maida dubansa ga amna. "Be soft with her amna" Kai ta gyada a sanyaye kunya tana kamata. Kwanaki ne kadai tayi bata ga adda sabreen din ba,amma sai taga ta canza mata gaba daya. Wani ajiyayyen kyau na musamman,qamshinta da komai nata ya zama wani na daban *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ 109 a nutse amna ta riqe mata yatsu,duk da yadda ta fahimci fu'ad din kaman yafi so tabar masa kayansa,to amma itama sabreen ita ta naniqewa,saboda bataso yayi wani abu daban da zai sanyata jin kunya gaban anni. Tayi imani kuma dukka hankali da idanun maamah yana a kansu,nunawa ne kawai ba zatayi ba. Abu guda daya daya tsaye mata a rai,ya gaza barin kwanyarta ta huta duk da yadda takejin jikinta shine dariyar maamah din. Ta gama karantar kowanne taku da motsi na matar......ta kuma sake sallamawa al'amarinta daga labarin fu'ad din. Ta tabbatar ba wata halitta da bazata iya cutarwa ba tunda har ta iya cutar da mijinta da kuma d'anta. Directly or indirectly tana farautar rayuwar 'ya'yanta ne ba tare da tasan hakan ba. A ranta taji dole ta qara takatsantsan da ita fiye da baya,sai taji kaman a baya ma kulawa da kiyayewa al'amuranta da takeyi kaman tayi sakaci,tabbas inda tasan wacece ita har haka......inda tasan wacece ita irin sanin da tayi mata a yanzu lallai ba shakka zata kiyaye komai nata fiye da yadda tayi a baya. "Hannunki dumi adda.....kaman akwai zazzabi a jikinki" Amna ta fada cikin kulawa dab da zasu qarasa kusa da anni. Kai ta girgizawa amna din tana sanya murmushi saman fuskarta "Ba wani me yawa bane......zai sauka in sha Allah,karki gayawa anni ki daga hankalinta" Dan jim tayi kaman ba zata amsa ba,don bataga dalilin da mutum baida lafiya ba kuma sannan yace kada a fadi. Hannu anni ta miqa mata sanda take shirin durqusawa ta gaidata. "Dawo nan ki zauna" Ta fada qasan ranta wasai da farinciki. Iya yadda taga fu'ad din ya koma a 'yan kwanakin da baya kusa dasu kadai ya bata tabbacin lallai komai yana tafiya daidai,ba fu'ad kawai ba.....hatta sabreen din ta canza mata gaba daya. Fatarta wani glowing kawai takeyi,hakanan idanunta sun qara haske da kuma girma. Tsananin kunyar anni takeji kaman zata nutse......ko kusa ko alama yadda takejin nauyin anni yana kamata batajin koda kusa da haka akan maamah,bata ce kuma ga dalili ba. "Sai kuma ka buge da sacemin diya ko?" Anni ta fada tana duban fu'ad daya gaidata. Karon farko shima kunyar anni ta kamashi,tattausan murmushin nan nasa da anni ta jima bata gani ba ya subuce masa,yasa hannunsa ya shafi baqa sidik din sumarsa da kudin da take lasa yayi jarin mutane da yawa. Matsawa amna kadan tayi kusa da anni tana rada mata sabreen din zazzabi takeyi. A nutse amna ta dubi fu'ad "Me ya samu ameenatu?" Fararen idanunsa ya sauke kan fuskar sabreen din sannan ya dubi anni. "Dan zazzabi ne dazu da zamu fito ya sauko mata......nace ma muje ta karba magana but ta dage wai zatayi managing" Kai anni tadan kada kadan. "Manage da ciwo?......to Allah ya sawwaqe,idan muka sauka dubai bai tsaya ba sai taga likita,ba kyau zama da ciwo ai" "Ameen" Ya amsa yana satar kallon sabreen din. Jinsu kawai takeyi,amma wani sabon amanne suketa kokawa dashi. "Bani ruwa amna" Ta fada a hankali tana tunanin idan tasha ruwan zai fada mata. Motsin bakinta kadai ya kalla ya fahimci me tace,ya matso a hankali bayan ya karbi gorar ruwan hannun jordan dake nesa kadan dasu,ya bude mata ya tako inda take yana tsugunnawa saman qafafunsa yakai robar bakinta. Tsam maamah ta dauke idanunta tana kullesu gaba daya,qirjinta na sake bugawa sosai tana jin kaman haki yanason kamata. Zazzabi?.....wanne irin zazzabi bayan ba'a Nigeria ake ba ballantana ace malaria ce?,wannan tsugonnan bata ruwan......ko ita da take uwarsa ba zata iya tuna ranar daya tsugunna haka gabanta yana bata ruwa ba......lallai dole ta batar da yarinyar nan bat daga duniya. Kai ta girgiza masa alamun xata iya sannan ta karba da kanta. Kurba uku tayi taji kaman ya isheta,sai ta miqa masa robar. "Is okay?" Ya fada yana motsa labbansa a nutse idanunshi a kanta kaman me tsoron kada ta bace masa. Kai ta gyada a kunyace tana saka kanta cikin mayafinta,bataso batason wannan kallon,halakata yakeyi gaba daya. "Kai Muhammadu" Maamah data gaza jurewa ta qwala masa kira,tana jin ya kamata ko yaya tayi wani abu da zata shiga lamarin ciwon don samun report da zai bata daman aiwatar da duk abinda ya dace da gaggawa. Tsam ya miqe yana amsa mata,sannan ya fara takawa gabanta sanda farouq ya iso yana gaya musu lokacin tashinsu yayi. "Sakamin takalma na......bazan iya durquso ba" Ta fadi tana qoqarin saisaita fushinta. Baice komai ba ya tsugunna gabanta yana tura mata takalman,ta fara saka qafafunta a ciki qirjinta a quntace. "Ita matar taka me ya sameta da ni bani da mutuncin sanin komai saidai naji daga bakin bare?". Daidai sanda ta gama zura takalman sai ya zare hannuwansa yana shirin miqewa. " Zazzabi ne kawai......shima din dazu ne yazo bawai a kwance take ba". "Zazzabi?,tana iya cin abinci?" Kai ya gyada mata a nutse don baisan me zaice mata ba,ita sabreen idan ya sakata sahun masu cin abinci ma ya zalunci sakamakon da zai gayawa.me bincike. "Akwai tashin zuciya?" Ta sake tambaya cikin bin qwaqwafi da son tabbatar da zarginta. Kai ta girgiza mata alamun a'ah. "Ciwon mara ko ciwon ciki fa?" Ta sake tambaya tana kafeshi da idanunta. Kansa ya mayar gefe kafin ya dawo da dubansa kanta. "Ban sani ba maamah.... Duka duka zazzabin na awa daya ne". " Eh dama da irin sakacinnan naku sai ciki ya shiga ya fice abinsa ma baku sani ba......banason ganganci da rayuwa shi yasa nake tambaya,dama wani aikin ai sai uwa ita data damu da rayuwar 'ya'yanta damuwa ta haqiqa.......tana yin amai ne?" Tambayarta ta qarshe da yaji yakai bango,hannuwansa suna zube a aljihun wandonsa sai kawai ya zubewa maamah kallonsa. Karon farko kenan tun bayan shudewar shekaru ashirin kusan da hudu rabon daya kalleta tsakiyar qwayar ido irin haka. Komai daya danganceta yaji yana dawo masa.......gaba daya tambayoyin nan nata basu zama komai ba face suna sake bude masa wani abu da yake zargi a kanta. Duk yadda ake maganar kwarjininsa bata taba yarda da gaske yana da wani irin kebantaccen kwarjini ba sai yau. Idanunsa sukayi mata wani irin nauyi,sai taji tana daburcewa. "To Allah ya kawo sauqi,sai a bincika ai aji meye,ko tsohuwar malaria ce" Ta fada tana miqewa tsaye,wanda hakan bai sakashi dauke kallonsa ba a kanta,har sai da yaji muryar farouq "Dude....." Waiwayawa yayi yana dubansa,sai ya nuna masa agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa,wannan shine ya ceci maamah daga irin kallon nasa ya juya yana nufar farouq din. "Wai......ka jini da yaro?,haka yakewa mutane?......muje zuwa,na rantse har da Allah muddin abinda nake zargi ya tabbata ga yarinyar nan bazan taba aminta na hada jini da ita ba......muddin wani me rai ne a jikinta ni mariyatu bazan bari ya taka duniya ba" Ta fadi tana cike da fatan ya zamana ma ba abinda take tunani bane. Amna najin takunsa a bayansu ta zame hannunta daga na sabreen din ta qara sauri zuwa gaba ta cimma anni abinta suka jera tare. Matsowa yayi yana daidaita tafiyarta da tashi,ba zato y dauki hannunsa ya aza saman kafadarta yana jawota zuwa jikinsa. "Kinga yadda kike tafiya kuwa?,you need my support......dont reject it" Ya qarasa fada yana furzar da iska. "Inajin body temperature dinki kaman yana hawa......you need medical care........banaso komai ya tabaki duniyata" Ya fadi yana waiwayawa ya dora mata qwayoyin idanunsa. Nauyin nan dai taji,sai tadan basar tana dauke kanta gefe "Zafin kaman na dazu ne,bai wani qaru ba" Ta fadi saboda batason yace zaa kaita asibiti. Idan tayi ciwo a Maldives ba zata damu ba......amma ciwo tsakanin makka da madina bata son hakan ta kasance,saboda qashene da take da burin xuwa a rayuwarta kafin ta koma ga mahaliccinta.....qasa ce da ta tara tarin shigifar addu'o'i take kuma kuma son tayi bajakolinsu a nan.....ba zataso wani abu ya kawo.mata tsaiko ba. Tana da tarin buqatun da batasan adadinsu ba,batasan kuma kwanaki nawa zata shafe kafin ta gama jerosu ba. Ba idanun wanda sukayi masa nauyi,a haka suka jera suna taka steps na jirgin har suka isa ciki. Suna shiga din matuqin jirgin yayi salute nashi sannna ya bashi hannu sukayi musabaha ya buqaci magana dashi,wannan ya sanya ta zame jikinta suka jera da amna suna wucewa ciki don samun seat din zama. Tuni maamah ta yiwa kanta mazauni a executive suit,a nata zaton shine guri na qarshe da yafi kowanne tsari,batasan sam da VIP suit ba,wanda wada dama mazauni ne na fu'ad din shi kadai,saidai idan yaso wani ya shigo ya zauna. A Aminitiy anni tayi zamanta,zaman jirgi ba baqonta bane,amna ma a nan ta zauna sai sabreen ta zauna kusa da ita suna taba