← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 215

Sashe 105

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

lips dinta masu kalan red dake motsawa kadan kadan alamun tsiwa na cinta suna fusgar hankalinsa. Yasha imagination na sanda zata mallaka masa su ba gardama ba tare daya qwata da qarfi ba......bama iya su kadai bama.....dukkaninta yakewa wannan fatan da kuma burin. Lallausan tafin hannunta ya matsa yana sauraren Jin muryarta. Muryar data zame masa abokiyar hirarsa a mafarki tun waccan ranar data amsa wayarsa a garin makka. Idanunta ta jjanye daga kanshi,har yanzu batajin zata iya kulashi din......duk sanda ta kalli fuskarsa fareeda take gani kwance cikin qirjinsa.....duk sanda ta kalleshi munanan maganganunsa a kanta take tunawa.....muguntarsa da musguna mata da mugayen maganganu,don haka ta taka zuwa side din hagunsa da nufin rabeshi ta fice. Cak ya dagata ya azata saman kitchen cabinet din ba tare da tunanin tayi kusa da qofa ba,ko kuma jama'ar dake gidan ba. Hannayensa ya sanya ya zagaye bayanta dasu,ya hana mata kowacce dama da zata raba jikinta da nasa,ya kuma yi kane kane a fuskarta ya hanata matsawa ko kadan,da wannan daman ya samu ya riqe lips dinta da suke tsone masa idanu ya fara aike mata da wani irin tattausan kiss. Ba wannan zafin ba kuma wannan hanzarin,wani irin sarrafata yakeyi da wani irin sanyi da salo daya soma zare mata duk wani kuzari da takeji da kuma zafin da takeji a kansa. Duk wani tunani nata ya tsaya cak tun daga sanda ya wuce cikin kitchen din. Wani abune da yazo mata a bazata wanda bata taba tunanin zai faru ba. Yau fu'ad ne a gabanta ya tsallake yabi mace kitchen da zummar zai samo ruwan dumi?. Cup din hannunta ta ajiye tunaninta yana komawa baya,ta saita dukkan idanunta da hankalinta akan qofar kitchen din tana lissafin mintuna nawa zaiyi kafin ya fito. Falon yayi shuru saboda wucewar kowa sai ita daya data rage,ta dauke kanta tana duban agogon hannunta bayan shudewar mintuna biyar din data tabbatar ko dafa ruwan za'ayi wadannan mintunan sun wadatar. Kujerar da take kai din sai takejin kamar ta mata nisa da bakin qofar. Miqewa tayi tsam tana canza kujera mafi kusa da bakin kitchen din tana sauke wani zazzafan huci,tanata qoqarin hana zuciyarta ci gaba da hasashen abubuwa daban daban da zuciyarta ke saqa mata. "Da gaske yarinyar nan 'yar bariki ce.....da gaske bariki takeson gwadamin?.....wai uban me yakeyi a kitchen din?,da gayya ta tsareshi kenan don ta gwada mata iyakarta?" Wadannan tunane tunane su sukaci gaba da kai kawo tsakanin zuciya da kwanyar maamah. Sake matsawa tayi kujera ta gaba tana sake zurfafa jinta da kuma idanunta akan qofar kitchen din,amma bata iya jiyo komai,abinda ya sake assasa baqincikinta. Wai wanne tsautsayi ne ya hanata tsaiwa a nigeria tasa ayiwa fu'ad da sabreen din mummunan farraqu?,irin farraqun da ko me irin sunanta zai tsani ballantana ita da kanta. Maida idanunta tayi ga agogo tana duba adadin lokutan da aka shafe. To badai dafa ruwan dumi ba....ko dan mutum za'a dafa a wannan gabar yaci ace ya dahu wani irin tsalle zuciyar ta keyi,wani sashe na zuciyar na bata shawarar shiga kitchen din da kanta taga qaryar rashin kunya. Sau uku tana miqewa sai ta koma ta zauna cikin shakka da kokwanto. Batasan ya zataji ba idan taje ta tadda daidai da abinda tunaninta yake bata. Qaqqarfan motsin da taji daga kitchen din ya qarasa tunzura zuciyarta,ta miqe da wani irin gaggawa ta durfafi kitchen din. Baya fahimtar komai sai sabreen din dake gabansa......kowanne sashe na jikinsa karbar saqo yakeyi iyaka,baisan wanne irin kebantaccen shauqi yakeji haka a kanta ba. A yadda yakejin kansa a lokacin yana jin kamar duniyar ma tayi musu kadan shi da ita. Ya sake zurfafa harshensa cikin bakinta yana sake zare mata duk wani kuzari nata. Qwace masa numfashinsa ya dinga yi yana kamoshi da qyar,a daidai wannan lokacin maamah ta qaraso bakin qofar kitchen din cikin zaton zata samesu tsakiya ko qarshen kitchen din. Tamkar an juya kwanyarta daga sama zuwa qasa haka taji. Wani irin shock jikinta ya dauka na tsakanin mamaki da kuma tsoro,jikinta da qafafunta gaba daya suka dauki kyarma,saita juya da matsanancin sauri tana jin juwa na shirin kayar da ita. Tana juyawa yana zare bakinsa a nata,baiganta duka ba,amma yaga wani sashe na rigarta. Zazzafan numfashi ya furzar yana cure hannun sabreen dukka cikin kasa hadi da kifi fuskarsa a bayan hannuwan nasu yana qoqarin daidaita numfashinsa. "Maamah" Ya fada can qasan ranshi,kwata kwata ya manta ya barta a parlor,amma yayi tsammanin yadda anni ta wuce daki itama dakin ta nufa. Daga fuskarsa yayi data sauya launi yana zubesu saman tata fuskar. Fuskarta ta kawar tana qoqarin dauke hawayen dake shirin zubo mata. Ya gansu,don haka ya sanya hannu da nufin dawo da fuskarta saitin nasa,saidai ta rigashi ta hanyar ture hannuwan nasa. A wahalce a kuma kasalance yace. "Na jima ina baki wannan shawarar......zanci gaba kuma da maimaita miki ita....kada kice zaki gwada raba kanki dani......zaki wahalar da rayukanmu ne kawai......don fu'ad bai shirya rabuwa da duk macen data sanshi a d'a namiji ba......fu'ad bai shirya rabuwa da sabrrrr ba" Yana kaiwa nan ya zame hannuwansa daga nata,yaja baya still idanunshi a kanta yana tunanin maamah na parlor din har yanzu ko tabar wajen. Har takai qofar dakinta ta fasa shiga,ta samu kujera ta zube tana qoqarin qwato koda abu guda ne cikin tarin abubuwan da suke karakaina a kanta. Da gaske bariki ne zalla za'a gwada mata?......ta samu nasarar mallakarsa ne?,yaushe ta ingizashi zuwa soyayyarta?,tayi imani a banza fu'ad bazaiso mace irinta ba......matar da karuwanci da bariki suka zama shaida kuma tambarinta na farko koda mutuwa tayi?. Hannuwansa ya miqa mata bayan ya gama daidaita mode dinsa. Bata ko kalleshi ba bare yasa ran zata bashi hannun nata. "Musunki da gardamarki zasu iya tunzurani na aikata abinda banyi niyya ba.....karki manta kawaici kawai nakeyi miki.....karki yadda kawaicina ya qare......kika bari hakan ta faru.....to tabbas ki rubuta ki ajjiye zan daukeki na kaiki wata duniya da ba wanda ya isa ya ganki sai muhammad fu'ad shi kadai". Fararen idanunta da suka sake glowing saboda siririn hawayen da yake a ciki ta watsa masa,kai tsaye ya saka hannu yana dafe qirjinsa hadi da lumshe idanunsa kafin ya sauke hannun nasa ya saka hannu ya kamo lallausan tafin hannunta yana sauko da ita. "Kinci bashi da yawa na rashin kula da abubuwan da suka ratayi a kanki nawa......duk wani abu nawa daya kamata ace kinyi bakiyi ba ki rubuta ki ajiye ya shiga sahun bashi". Kasa musanta masa tayi sanda yake riqe da hannunta suna fita a kitchen din. Hannun kujera ta koma ta zauna tana hade hannayenta a qirji zuciyarta tana mata wani irin zafi. Bata jin zata iya daukan wannan abun sam ba zata jura ba.....tana da shakka idan har zata iya barin sabreen a gefen danta har xuwa lokacin data tanadar mata. Sanda ta daga idanun nata don sake duban kitchen din sai tayi kyakkyawan gani,yana riqe da hannunta gam da taketa qoqarin zamewa. "Kina qarawa kanki laifi akan laifi......please ki hutar da kanki" Ya fada yana lumshe idonsa gami da jin yadda riqe hannunta kadai ke sakarwa jikinsa wadansu kaifafan makamai. "Muhammadu" Ta kirashi da wani kaifi da yake nuna zallar bala'i da bacin rai da zuciyarta ke ciki,musamman data lura bai ankara da wanzuwarta a wajen ba.
Chapter 105 · 0% Book details