Sashe 107
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
singalilin hannun ta ke gogar nashi tana tayar masa da tsigar jiki. "When.....sai yaushe zaki fahimci cewa KECE DUNIYATA?" Ya qarasa maganar yana ware idanunshi gaba daya akan fuskarta. Wannan karon kasa jure kallonsa tayi,saita runtse idonta tana hade rai sosai. "Banaso kana tabamin jiki.....bana so" "Am addicted to you.......tabaki shine favourite thing a rayuwata gaba daya" Ya maida mata amsa kai tsaye yana me bata tabbaci ya kuma sake matso da ita sosai yana mannata da jikinsa. Gigicewa tayi sanda taji ta saki ajiyar zuciya tare da tashi ajiyar zuciyar,kunya da wani irin takaici ya lullubeta,abinda taji haduwar jikinsu ya saukar mata ba zata iya shanyeshi ba idan bata bawa zuciyarta daman numfasawa ba......to amma kuma ta dauka a boye ta saki nata ajiyar zuciyar. Fitar sautin ajiyar zuciyar tata ya sakashi ware dukkanin idanunsa a kanta yana dubanta,duba ne na qurilla da son gane meye ya taba wannan zuciyar?. A gaggauce gama shiryawa tsaf cikin Holland vlisco me asalin tsadar,an xuba mata dinkin manyan mata na buba,ta kuma cika wuyanta da hannunta da kayan ado na gold. Macace me son izza da alfahari,wadda idan tazo guri so samu kowa ya dusashe a gurin sai iya tauraruwarta kadai. Ta tsaya gaban madubi ta tabbatar komai yayi a shigarta sannan ta juya ta dauki wayarta tana nufin fita a dakin. So take ta kasa ta tsare......so take komai zai dinga wakana cikin gidan ya dinga kasancewa saman idonta,bataso tsakanin sabreen ko fu'ad wani yayi wani motsi da zai zarta ganinta da idanunta,wannan karon salon da zata bullo musu dashi na dabanne,har sai ta samu tabbatuwar nasara a gareta. Tanaso da iya dressing dinta kawai ameentu ta fahimci wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa,ameenatu ta sake tabbatarwa da kanta cewa ita din fa itace mahaifiya ga muhammad jadda.......ba wata mace a duniya ta biyunta. Cikin takun isa take fita parlor din tana qarewa ko ina na parlor din kallo. Siyan gida a qasashen waje musamman gidaje irin wadannan ba abu bane da za'ayi maganan qananun kudade ba. Abinda ta lura dashi wasa wasa ameenatu ta maida mata yaro saniyar tatsa kenan,taja wata irin qwafa tana samun sofa guda daya ta hakimce a kanta. Daga inda take ta sanya remote ta kunna tv,tayi sa'a tashar farko ta kamota a inda suke gabatar da abincij breakfast na yaren mutanen qasar china. Minti uku kacal taji tunaninta ya koma ga kitchen din gidan,tanaso ta tantance dame dame ya jibge musu suke ci?,wanne irin gadara kuma ake gw adawa a wajen?,don haka ta miqe tsam tana maida flats shoe dinta tana nufar kitchen din. Yau kam sai data shigo sosai sannan idanunta ya sauka a kansu. Mugun gigicewa tayi fiye da jiyan,saboda yanayin data gansu a yau din yafi na jiyan munin gani. "Na shiga uku ni mariya!" Ta fada muryarta na rawa tana yunqurin juyawa,wanda saurin da take ta matsa a wajen santsin gurin ya debeta ta kusa zamewa,cikin taimakon Allah ta kama murfin freezer ta riqe tana tsaiwa saman qafafunta. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ 94 Daga shi har sabreen din sai a lokacin suka dawo hayyacinsu. Ita ta fara zamewa ta tsakiya tana raba jikinta da nashi haushi yana cikata. Yana son lalla qarfi da yaji sai ya koya mata dabi'ar da ba tata ba......lallai lallai sai ya sanyata tana yin abinda ba halinta ba.......batasan me zata masa da zai sanyashi nesanta kansa da ita ba. Batason yadda yake warning nata kan bata isa ta raba kanta dashi.......a nata wajen ba wani abu me sauqi a wajenta sama da wannan din......zaman Maldives ya bashi wannan damar,isarsu Nigeria kuma zata yanke kowacce alaqa da yake tunanin ya qulla da ita. Juyawa tayi tana fita a kitchen din ba tare data sake kallonsu ba. Qirjinta ne kawai yake bugawa da wani irin bacin rai da kuma rudanin abinda ta gani din. "Wanne irin asiri tayi masa?,wanne irin asiri ne wannan?,maqale mata?" Ta dinga jerawa kanta tambayar da bata batasan amsarta ba. Yadda zuciyarta ke matsewa da bacin rai sai takejin idan tayi shuru tsaf zuciyarta zata iya bugawa......don haka ta soma sakin ruwan sababi. "Wanne wacce irin masifa ce?,gida sai kace gidan arna?,to wallahi ni bazan lamunci wannan ruwan tantirancin da barikin ba ehe....dole kowa ya gyara zamanshi,ni ba shashashar uwa bace ko banzar suruka,kome mutum yazo dashi ina daidai dashi ne". "Oops" Abinda fu'ad ya fada kenan yana dafe goshinsa da tafin hannunsa,zuwa yanzu yanajin anya zai iya rayuwa da mutane kuwa muddin yana tare da sabreen din?,anya gidan nan duk da haka bai musu kadan ba?,wannan zaman zai yuwu kuwa?. Duba daya sabreen tayi masa ta zare idanunta tana lalubar hanyar fita daga kitchen din ranta a bace. Jiya tayi zargin giftawar mutum dama a kitchen din,koda suka fita sukaga sai ita kadaice a falom zuciyarta ta dinga raya mata ita ta shigo......amma ba kasafai ta fiya son dorawa dan adam zargi ba,don haka ta cire abun a ranta,qarshe ma ta gayawa kanta. "Idanma itace ita ta jiyo......zaiyi mata dadi idan idanunta suka gani ta kuma tayata rabata da maqalallen d'anta. Dab da zata fice a kitchen din yayi caraf ya kamo hannunta yana sake janta jikinsa. Dubansa tayi idanunta na bayyanar da bacin da ranta yayi "Bayan maamah din ko akwai wanda kakeso ya sake shigowa ya ganmu ne?" Ta masa tambayar da salon gatse kanta tsaye tana duban qwayar idanunsa duk da tsaurin da kallon yake mata. "Yes" Ya bata amsa shima kai tsaye yana kallonta "Saura anni.....anni ce akwai ta rage bata gani ba.....ita nakeso ta gani.....don ta hakanne kawai zata fahimci ina tsananin buqatar matata". Har tsakiyar kwanyarta taji yadda ya fidda sautin maganar,wani abu me kama da jin kunya da nauyinsa ya danso kamata,saidai tana ganin ya kamata ta fito masa a mutum don ya sasssuta yadda yake yawan hada jikinsa da nata. Da alama da gaske yake fadi....da gaske yakeson annin ta gani,tunda daga nan inda suke tsayen tana iya jin muryar annin na tambayar maamah "Lafiya mariya?" Batajira jin amsar da zata bata ba ta soma kokawar qwatar kanta. "Annin ma?" Ta fada tana ware idanunta cikin kallon me kama da harara harara. Yadda ta yiwa idanun nata kusan kasheshi yaso yi,hannunsa ya miqa a hankali ya nufi gashin idanunta da suka sake zara zara saboda buda idanunta da tayin,abinda yadan saukar mata da tsoro ta rufe idonta da sauri. Kusan dariya abun ya bata,ya zuba mata idanu yana ganin yadda zuciyarta ke bugu sosai tun daga wuyanta zuwa qirjinta dake lullube da hijabi. "Bakisan harsashin da kika sake jefamin ba da wadannan idanun naki ba......a karo na gaba tsiwar nan zan cire gaba dayanta na maida gurbinta da zazzafar soyayya....." Ambatar soyayyar ya sakata bude idanunta a kanshi,tanason nuna masa tawayenta koda ta hanyar murguda baki ne amma tana kokwanton kada ta jawa kanta,sai kawai ta zabi zame jikinta daga nasa gudun kada annin ta samu isowar kitchen din. Still sake riqe hannunta yayi,ga mamakinta hankalinsa kwance yake janta zuwa falon kaman wani dan jagora. Daga can qarqashin zuciyarsa kuma wani kokwanto da mamaki ne fal ransa. Me yake tunzura maamah din a duk sanda ta gansu haka a tare?,bayan tafi kowa sanin igiyar aure ce ya hadasu?,me yasa yake ganin fushi kwance a fuskarta game da sabreen bayan a nashi tunanin zatafi kowa murna da farincikin kasancewar hakan?. Idan bar ba mantuwa yayi ba.....duka duka ba'a yi watanni biyu ba data masa kyakkyawan warning akan bawa yarinyar kulawa.....meye ya canza wannan?,wannan kadai yana sake bashi signal na AKWAI WANI ABU. Dukka juriyarta da dakiyarta ta tattara sanda suka iso parlor din,kanta tsaye ba tare da tabi ya banbamin maamah ba ta wuce zuwa dakin anni. Ko wani bai gaya mata ba tasan maamah din ta bita da kallo ne,kallon da ita daya tasan ma'anarsa. Tana qasan shower tana jin yadda ruwan kebin sassan jikinta amma mayataccen qamshin nan nasa bai matsa ko nan da can ba,duk inda ya aza hannunsa a jikinta sai ta tuna idan takai hannunta,ta kammala wankanta tsaf ba tare da tasan yadda suka qare a parlor ba don ba damuwarta bane. Ta jona dryer nan cikin toilet din da busar da kanta,sai abun ya fado mata a rai. Hala kishi maamah take da ita?,hala maamah tana tsoron kada ta karbe mata yaro?,qila maamah tana zaton mallakarta ce ita sabreen ke niyyar qwacewa?. Siririn tsaki ta saki a ranta tana fadin "Inda tabi a hankali ma wannan rayuwar tasu batamin ba......dab nake da bar mata d'anta" Tayi zancan cikin ranta saidai idanunta na kallon fuskarta ta madubin dake gabanta. Dif sai kuma tunaninta ya tsaya cak tana sake maimaita furucinta na qarshe. "Idan shi zaki iya barinsa.....zaki iya barin anni da amna?" Tambayar data tsaida duk wani tunaninta kenan,sai ta samu kanta da neman tabbacin zata iya ko ba zata iya ba?. "Su nadra huda haneefa sunfi muhimmanci cikin rayuwata" Ta gayawa kanta a gaggauce tana kunna dryer din da hanzari tana son binne wannan tunanin daga ranta. Idan banda rudin zuciya ma duka duka yaushe ta sansu?,yaushe ta fara rayuwa dasu da har zata shiga shakkar iya barinsu?. A nutse ya shirya cikin riga da skirt na sakakkun English wears. Basu kamata ba amma sun mata wani irin dan banzan kyau,musamman sata daure gashinta data gyarashi da kyau tsakiyar kanta. Wani qaramin hijabin ta samu ta sake dorawa saman kanta,saidai wannan din da kadan ya rufe saman qirjinta. Tana jin amna na mata tsiya "Wannan kwalliyar adda bazan iya cankan nawa hamma zai siyeta ba......kullum sai na dinga jin inama nice ke adda....inama nike da kyanki?" Harararta tayi "Zageni da kyau amna.....har kina iya cewa wai na fiki kyau?". " Da gaske nake adda....ke kam ba zaki gani ba tunda a jikinki yake" "Bazan gani ba dai saboda kin fadi abinda bashi bane.....matsamin kada lokacin walaha ya kubcemin" Ta fadi tana sanya dogon hijabinta,da wannan suka rabu amna ta shiga wanka ita kuma ta tayar da sallar. Tana shafa addu'o'inta anni ta shigo tana dubanta. "An gama breakfast.....lokacin cin yayi....ki fara yin gaba kafin amna ta gama nata laqai laqai din" . Kanta ta daga ta dubi anni,tanason gaya mata ba zata fita ba..batason sake fita kwata kwata bare taga matar,maganganunta na