Sashe 4
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
wani irin fitinannen qamshi take barwa gurin. Wani irin mayen qamshi me matuqar naci da mannewa jiki dama dukkan wani abu da mutum zaiyi mu'amala dashi. Qawatattun idanun nan nata da a yanzun suka koma rusunannu ta daga a nutse tana duban me gyaran jikin dake faman gyara wutar da zata sake turareta da ita. Ta zama wata kurmar qarfi da yaji,magana na mata wahalar gaske,kwanyarta da nazarinta harma da dukka tunaninkan da takan raba dare tana yinsu.....dukkansu sunfi ta'allaqa da kuma rinjaye akan YAYA WASAN ZAI KAYA?......wa zata fuskanta cikin fuskoki muryoyi dama ruhikan dake zagaye da wannan game din?. Idan ta tuna da mariya maamah.......tana jin wani abu sosai qasan ranta......jikinta kuma yana bata wani lamari me nauyi da batasan mene shi ba,amma kuma wani sashe na zuciyarta yana gaya mata ita din ba komai bace......tayi ganganci ne ma kawai data kutso kanta cikin rayuwarta......batasan wacece sabreen ba da gaske da bata aikata hakan ba.......bata kuma san meye da meye zata iya aikatawa ba. Motsawar sunan muhammad fu'ad kawai cikin kwanyarta shine abinda yafi sanyawa wani tsagi na zuciyarta damuwa.........lalata dukkan wata alaqa da kuma dangantaka cikin aurensu shine abu mafi sauqi da zata iya aiwatarwa......to amma kuma saki fa?.....A HANNUNSA YAKE!,amsar da akowacce rana take qara yawan adadin fargabarta. Lumshe ido tayi taja iska sosai cikin huhunta sanda muryoyi biyu suka sauka a tsakiyar kanta "Turaren ya hadu kona miqo miki ki zauna akai da kanki....." Cewar basudaniyar me gyaran jikin,yayin da nata maganar ya cakuda dana mamma bahijja data miqa mata wani bowl na tangaran "Bata din.....kafin hayaqin ya gama bin jikin ki saiki qoqari ki shanye wannan". Dara daran fararen idanunta ta daga tana kallon mamma bahijja kafin ta maida dubanta kan abinda take miqo mata,itama ita take kallo wannan ya hanata katabus na musanta mata,sai kawai ta miqa hannu ta karba,saidai kuma data fakaici ta juya,saita maidashi daga gefanta ta ajiye. Sanda tururin hayaqin ke ratsa sassan jikinta haka kowanne lungu da saqo na zuciyarta ke qoqarin bata mafita a lamarin dake tunkarota nan da kwanaki biyar masu zuwa. Zuwan mamman bahijja ya zame mata wani babban katanga daya hanata aiwatar da kowanne shiri da zai nesantata da auren.....duk da tarin bayanan da kawu yayi mata na ba inda zata shiga a duniya ta iya tserewa me jadda........saidai ta dauki.maganar tasa a wasan yara ne. Koshi waye.....ko kuma da meye yake taqama tayi imanin saidai idan bata sakashi cikin plan dinta ba..... "Adda baki sha bafa" Muryar huda da ke zaune gefanta ta fada,wadda kusan kowanne shirye shirye da ita ake aiwatar dashi. Maida idanunta tayi ta sake lumshewa muryar huda na dawo mata,ta fahimci dari bisa dari ba wani me adawa da auren,kusan kai tsaye ma zata iya cewa dukkaninsu maraba suke da abun,duba da irin walwalar da suke ciki gaba dayansu. "Ki nutsu sabreen.......ki nutsu.....karkiyi abinda zargi zai dawo kanki......karkiyi abinda su mamma bahijja xasu kasa karbarki da wankeki daga laifi duk sanda kika kammala da wancan game din kika dawo musu" Wata murya daga can qasan zuciyarta ta soma gaya mata. Idanunta ta bude ta aza kan huda har sai da hudan tadan sha jinin jikinta. Sunyi mata farin sani,daga kallonta kawai suna iya karantar umarni da kuma hani,amma ga sabanin tunaninta sai tayi mata nuni data miqo mata abun. A hanzarce kuwa ta ajiye littafin hannunta ta miqe ta dauko ta miqa mata. Tsure abun tayi da kallo wanda batasan da meye da meye aka hadasu ba,to amma koda meye aka hada din,ta tabbatar mamma tana asarar kudinta ne kawai,don haka ta kafa kai ta soma kurba a hankali gardin abun yana ratsa kunnenta duk kuwa da bakinta ba taste,haka zuciyarta a quntace take. *******Doguwar tafiya,hawa da kuma sauka,kutsawa cikin surquqi dukka ba damuwar maamah bane. Fatanta da burinta ta dangana ga mutumin data miqawa al'amarinta gaba daya,ta kuma sanya hope me yawa a kansa. A yanayin data ganshi a yau ya sake saka mata tabbacin samun cikakkiyar nasara. A hargitse yake yau din cikin zafin ayyukan mutanen da suka zabi ya zame musu abun dogaro kuma hanyar samun duniyarsu ba tare da damuwa da meye makomarsu ta lahira ba?. Bayan shafe shafensa da buge bugensa,ta hautsina dukkanin kayan aikinsa da yayi,ya kalleta da jajayen idanunsa qananun ainun dake cike da rashin tauhidi da kuma zallar sabo fajirci da fasiqanci. Dubane daya sake tabbatar mata ba rahama ko tausayi ko misqala zarratin a cikin ransa "Akwai tarin sarqaqiya......akwai tarin qalubale......akwai al'amura da yawa da zasu iya wanzuwa ko su biyo baya........ita din taurarinta nada tsananin haske da wahalar kutsa kai a cikinsu........tana da wahalar sha'ani na gaske......tabata kuma abune da zai iya zuwa da nasara da akasin haka.......kaman zan iya cewa KINYI KUSKUREN ZABINTA.......to amma kuma ba wani tauraro da zai iya shiga nasa taurarin sai natan......tamkar itace mahadi masarrafi kuma barin nasa taurarin......taurarinta sune abokan tafiyar nasa.........sunyi matuqar dacewa da juna.......wanda hakan shine zai bada damar tafiyar umarninmu da haninmu a kansa......kusan komai nasu suna matuqar kamanceceniya dana juna......ITACE TA DACE DA CIKAR BURINKI MUDDIN AKA SAMI GUSHEWAR AKASIN DA NAKE HANGOWA......saidai na gaya miki.....kamar akwai alamun KUSKURE DA NADAMA.......akwai babban waqeee'a......juyewar komai da lullubewar mayanin duhu bisa faifan qaddara". Tunda ya fara maganar gabanta ke wani irin faduwa. Hajja da suka gama sauraron bayanan a tare ta dora hannunta a kafadar maamah da zummar yin magana da ita da neman qarin bayani......saidai da sauri maamah ta zame hannunta daga kafadarta......tayi nisan da batajin zataji kira......zuwa yanzu nasara take nema ta kowacce fuska,ta kuma kowanne yanayi......bata buqatar tsaiko fashin baqi ko qarin bayani a yayin da take dab da cimma nasararta........bayan kuma a baya ya bata tabbacin ta wannan hanyar ce kawai nasara zatazo mata babu ko kwanto "Amma dai akwai hasken nasara ko dan kadanne?". Kansa dake cike da wasu irin gasussuka ya jinjina ba tare daya koda dubi idanunta ba. Cikin samun qwarin gwiwa tace "Nasara duk nasara ce komai qanqantarta,baa canza mata suna daga nasarar dai,hakanan daga qaramar nasara ake cimma babba......ayimin komai da ake da iko a kansa.......a sakamin yarinyar a tafin hannuna kafin samuwar fu'ad.......itace tsanin......ita zan fara mallaka don ta zama hannuna tsani na kuma idona zuwa ga wancan babban burin nawa!". Ta fadi muryarta na raunana tana tsoron jin akasin abinda zuciyarta ke muradi. "An gama!" Ya fada da wata kakkaurar murya maras dadin amo. Saita sauke ajiyar zuciya tana yi relax ganin yadda ya soma maida hankali akan aikinta. Boyayyar ajiyar zuciya hajja itama ta saki. Ba haka taso lamarin ya kasance ba,taso tana kuma so taji cikakken fashin baqi da qarin bayani daga bakinsa. Wacce irin sarqaqiya ce? Wanne irin duhu ne?. Wani irin baqin lullubin mayafi ne haka?. Wacce nadama ce zata biyo baya?. Meye kuskure a cikin zabin nata?. Dukka wadannan amsoshin tana buqatar saninsu ne don tasan daga ina zata dasa nata harsashin?. Daga ina tata TAFIYAR zata fara?. Ta wacce fuska zata saita tata DUNIYAR?,ta aza duniyar SHALELENTA?. Bata data cewa ko wani motsi,ta sani cikin aikinsa ba shishshigi,ke me rakiya kuma baki data cewa......hakanan baki da damar yin komayya kiyi tambaya akan aikin daba naki ba.....wannan kadai ya kashe mata jiki,ta zurfafa a cikin saqe saqe har ya kammala aikin maamah,ya kuma shaida mata su wuce zasu tadda komai cikin motarsu da qarin bayani. Bata sake gasgatawa da imani da zancansa ba saida suka samu komai a mota a ajjiye kaman yadda yace. Ta sake tsinkewa da lamarin aikinsa,inda da wani suka je wajen.....ko akwai gilmawar dan adam ta wajen sai tace an ajiye musu ne. "Kings abun mamaki hajja?,kullum mutumin nan sake dauren kai lamarinsa yakeyi" Ta fada tana juya kayan tsatsubar dake hannunta. "Kina zaton gurin qaramin mutum na kawoki......amma mariya?,me yasa kikaqi tambayarsa dukka qalubale da matsalolin daya hango miki?" Hajja tayi tambayar da tafi tsaya mata a rai.