Sashe 12
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bata kudadensu ba wajen siyan ticket na jirginsu sun cika jingim wajen shaida daurin auren ba,ya sake jan qaramin tsaki yana juyawa tare da neman nesanta kansa da hayaniyar wajen,guard dinsa da duk hautsinewar wajen basu yarda sun matsa ba suka biyoshi a baya. Can wajen motocinsu ya koma,sai daya shiga ya zauna sannan yace musu "Don't.....karku gayama kowa ina ta nan idan ba farouq bane ya tambaya". "Yes sir" Suka amsa a matuqar ladance suka maida murfin suka zuge masa. Rawanin duka da babbar rigar ya cire ya ajiye gefe,sannan ya koma ya zauna sosai yana nazarin wajen ta cikin motar. Abinda ya lura dashi,bawai farouq kadai ba,hatta da abba ya dauki abun very serious,yaga mutanensa a wajen har baisan adadinsu ba......haka anni,yaga familynta sosai,tamkar tana auren farouq ne,sai ya maida idonsa ya kulle yana son tuno waye da waye ya gani daga bagaren maamah?. Bai samu nasarar kaiwa qarshen tunaninsa ba knocking da aka yiwa glass din motar ta sakashi bude ido,ya ganshi farouq ne,yana daga kwancen ya danna remote ya bude mass murfin. Dubansa yayi sanda yake qoqarin shigowa "Reception zamu wuce.... Already wasu sun fara yin gaba,musaddiq da saddiq tun dazu suna ta wajen". Shi sai a sannan ya tuna ma.baiga kowa cikin su ba,ason ranshi farouq din ya barshi ya koma masauki ya kwanta ya rama baccin dake.kansa,ya kuma rage hayaniyar mutane da yakeji har cikin kansa,saidai kuma ya sani koda yace zai masa bayani ma farouq din ba fahimtarsa zaiyi ba,yadai fadi abu daya "Ina fatan daga can duk wata hidima ya qare baku qirqiri komai ba kuma......don bazan iya jure zuwa wajen komai ba". " Wanda baisan halinka bane zai wahalar da kansa shirya wani abu......walimar.ma saboda cika sunna ne da neman albarkar auren" Farouq ya amsa masa yana daga kiran abokinsa da yake gaya musu sun isa wajen "Muma muna dab......ka jirani" Yace yana sauke wayar. Siririn murmushi kawai fuad ya saki,farouq.....farouq..... Idan ba farouq babu shi.......kaman yadda yasan idan babu shi babu farouq din. Tunda momma bahijja ta tilastata tayi wanka,ta kuma shirya cikin wata sabuwar atamfar Hilton wax. Cikin kayan da momma ta zare cikin lefen ta bayar aka dinka ba tare da sanin sabreen din ba. Tun tana shiryawa taji shigowar uncle abdulhakeem da tun jiya suka iso suka kwana a tahir guests palace. Zancan duka ya shafi aurenta ne,wanda duk kalma daya da zata fita daga bakin uncle din nata sai taji kanta ya wani sara mata. Zazzafan mutum ne da ta jima bataga mutum me zafi da kafiya akan gaskiya ba irinsa. Ta jima tana tunanin idan ta kammala deal dinta ta tashi matsawa daga gurbin da take zuwa wani ta yaya zata bacewa idanunsa?,ta kuma zullewa duk wata tuhuma tashi?. Taji ya ambaci sunan su huda da nadra da tafi sati tana tunanin ina za'ayi da rayuwarsu?,amma tasan tayi kadan ta tsaya gabansu ta musu wannan tambayar,bata kuma samu jin abinda suke cewa ba sanadiyyar hayaniyar yan tafiya daurin auren data qaru. Ta gama shiryawar taji wani zazzabi ya sauko mata bayan ciwon kanta daya dinga gaba gaba saboda tunanin data matsawa kanta dashi,sai kawai ta lallaba can gadonsu nadra dake qarshe ta haye can ta qudundune. Page 10 Can cikin tsakiyar kanta maganganun mutane ke mata yawo sanda motar ke tafiya cikin nutsuwa saman lafiyayyar kwaltar dake shimfide a kanta. Muryoyin mutane daban daban da sukayi mata fadan shiga gidan miji wai a cewarsu "Allah yasa dai ki iya zama......don zaman aure daban da zaman bariki,zaman gidan miji daban da yawon bariki" Muryar bibo kenan da nata salon fadan da yafi kama da turun mutuwa "Da dadi ba dadi kiyi haquri ki zauna......Allah yasa mutuwa ce zata raba,kiji kiqi ji,ki gani kiqi gani" Muryar daada kenan wadda ta kama hannuwanta tana fada muryarta a sanyaye. Ko da can ba zatace ga wani mummunan abu da daada ta taba musu ba,ita dai barta da shariya da rashin shiga lamari da sabgar kowa cikin gidan. Idan ka ganta kuwa a ciki to tabbas abu yaci tura,amma bibo da yaabi koda dan wani akeyi suna iya ara su yafa tun usul. "Mommaa......nadra.....haneefa.....huda" Sunayen data iya kirawa momma kenan sanda take yunqurin sakata a cikin motar da zata yi musu jagora zuwa inda zasuje. "Ina sane dasu......kuna su din ba nauyinki bane" Ta amsa masa a tausashe. Ta cikin lafayar jikinta take iya hangen yadda motar ke tsala gudu abinta,amma saboda lafiyar motar da irin tsarin da akayi mata zaka rantse ba gudun takeyi ba. Ta maida idanunta ta lumshe,wasu hawaye da batasan sanda suka taru ba suka biyo kuncinta suka diga bayan hannunta dake ajiye saman cinyarta. Har yanzu dai ta kasa gasgata abinda take gani,har yanzu ta kasa gasgata abinda kunnuwanta da zuciyarta ke nanata mata. Da gaske mutumin nan yaci galaba a kanta da dukka tsarikansa.....da gaske shike da nasara ba ita ba.......da gaske ya cinye wasan a wannan gabar.....saidai kuma hakan baya nufin zaita nasara kenan a kanta,hakan baya nufin ta fadi kenan har abada.....lallai zata canza labarin......zata canza qaddarar da dukkan iyawarta. "Gidan mamarshi zamu fara shiga.......sai gidan riqonsa,kamar haka matar data shigo dazu tace ko?" Daada ta fadi tana dan duban momma bahijja da hannun sabreen yake cikin nata. "Eh haka ne" Ta amsa mata idanunta sauke kan faffadan sabon gate din gidan maamah dake nuna zallar dukiyar dake narke cikin gidan. A nutse jerin gwanon motocin suka cusa kai makekiyar harabar gidan data kasance mafarkin maamah na shekara da shekaru,gidan daya dauki hankula da bakunan dukkan jama'arta dake hulda da ita. Gidan da a cikin ranta ita kanta ta gamsu da dukiyar daya lashe,amma zuciyarta bata gama nutsuwa da hakan ba saboda har yanzu gidan alhj hamza kibiya da iyalinsa yafi nata girma yalwa da kuma tsari,ba tare data duba yawan da suka darata dashi ba,da kuma yawan al'umman da gidan ke dauka suke riqo a yanzu haka. Tunda motar ta tsaya a parking lot na gidan gabanta yake wani irin faduwa,ta maida idonta ta lumshe tana sauraren bugun da zuciyarta keyi da bata taba jin irinsa ba,sai taji bugun har kusa da maqogoronta. Sake runtse idanunta tayi sanda momma bahijja ke fadin ta fito,tana jin bugun zuciyar na sake daduwa amma kuma ta rasa me ya kamata ta karanta?,wacce addu'a ce ta dace da irin wannan yanayin da takejin kanta a ciki?. Riqon hannunta da momma din tayi shine ya sassauta mata abinda takeji kadan,ta sake riqe momma din itama da kyau ba tare tasan ta yadda zata gaya mata abinda takeji cikin qirjinta ba. A dan hanzarce ta shigo dakin nata,sannan ta maida qofar ta kulle ta kuma murza key. Da dan hanzarin still ta isa gaban madubin nata dake manne da wasu lafiyayyun lockers. Ta murza daya daga ciki ta bude ta,sannan ta saka hannu ta ciro baqar ledar dake a ciki ta dora saman madubi. Ko ina a jikinta amsawa yakeyi da wani irin doki da son fara aiwatar da nata aikin,a yau batasan sau dubu nawa tana addu'ar samun wannan sa'ar ba......batasan sau nawa ta roqi samun nasara a wannan ranar ba,nasarar da indai ta rasata kamar wadancan kwanakin ta tabbatar komai zaizo mata da wahalar gaske.....batasan kuma ta yadda zata tari abun ba. Kusan leda shidda ce,kowacce sai data kunceta sannan ta saka hannu ta fara ciro kayan ciki. Kusan tarkace ne a idanun me kallo,amma a wajen maamah gwara rashin million dubu da rasa daya daga cikin kayan. Wasu kwalabe ne masu dauke da wani irin baqin abu a ciki,wani kuma kore kore ne,saidai yana da dan qamshi qamshi kadan a ciki mara qarfi. Ta bude kowanne ta tsiyaya cikin tafin hannunta,ta kuma mulke hannun nata da kyau kamar yadda aka umarceta da tayi,sannan ta maida komai muhallinsa kamar bata taba komai ba cikin dakin. Gaban madubin ta tsaya tana qoqarin controlling kanta da daidaita nutsuwarta. Idanun ta fes cikin fuskarta tana maganar zucci da kanta da kanta,wanda batayi wani nisa ba knocking din da ake mata ya isa kunnuwanta. Adan fusace tace tambaya don bata buqatar doguwar mu'amala da kowa har sai wadda tayi shirin saboda ita ta iso "Zuwaira ce" Ta bata amsa a tsanake. "Sun iso,suna falon qasa sun......." "Gani nan" Ta tari numfashin zuwairan ba tare data jira sauran bayaninta ba. Ba sauran bayaninta take da buqatar ji ba,tunda taji abinda take buqatar jin,ta waiwaya tana zura takalmanta data cire tare da kallon tsadajjen mayafin data lullube jikinta dashi ta tabbatar ya zauna a jikinta......ya sanyata tayi kwarjini da wata irin kamala da sam zai wahala ka kawo wani abu me muni a kanta. Kyanta ya bayyana.....kamanninta da musaddiq sosai,yanayin jin dadin da kulawar data samu wadda take rainawa ta sake sanyawa jikinta ya murje sosai,hutu da quruciya sun bayyanar mata. Murmushi ta sakarwa kanta da kanta,sannan ta juya a hankali tana fita a dakin. Tun daga saman stairs din take raba idanunta tana son hangota. Bata wani sha wahala ba,ta hangeta zaune saman lallausan carpet din da aka qawata tsakiyar falon dashi. Qafafunta a tanqwashe suke,kanta a qasa cikin shigar laffayar da tazo mahadin lace din da aka zauna akyi dukka adon jikinsa da hannu(handmade lace),kamar yadda lafayar jikinta itama duk wani zare da duwatsun jiki da hannu aka gameshi. Abune na masu dashi,ba wani cikar jama'a masu yawa ko cinkoso,kowa yana zaune a nutse,yayin da gaisuwa ke wakana tsakaninsu momma da jama'ar da suka samu cikin falon. Da wani irin kirki na gasken gaske saman fuskarta,faffadan murmushi da fara'a me nuna tsantsar maraba da baqo ta iso rukunin kujerun tana furta "Lale maraba......sannunku da zuwa......sannunku da qoqari" Da murmushi a fuskar momma ta amshe maraban tana duban maamah tsaf tare da karantar yanayinta. "Bari na zauna kusa da diyata" Ta fadi tana zama kujerar dake kusa da sabreen din. Gaisuwa akayi cikin mutunci dason nuna ainihin zallar kirkinta,suka gabatar mata da amanar sabreen tare da dan qaramin jawabin girmama kowa ga sabreen din "Itama diyata ce ai tunda yarona take aure,kuma in sha Allah zakuyi alfahari da hada alaqa damu,Allah ya bada zaman lafiya,shi kuma Allah ya tayashi riqo" Maamah ta furta cikin zaquwa da gajiya da bayanan. So take kawai ta isa ga muradinta. Am nace ba.....idan ba damuwa inason ganin diyata a kebance,minti biyar don Allah" Maamah