← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 215

Sashe 80

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yaya zata iya hada numfashi dashi qarqashin rufin daki guda daya?,lallai inda tasan da yiwuwar faruwar hakan wannan kadai a wajenta ya isa dalilin da zai hanata yin tafiyar ma gaba daya. Sakin abinda takeyi tayi ta kuma ware veil dinta ta lullube kanta dashi dukka tana satar kallonsa. Baiko nuna yasan da tsaiwarta a wajen ba,hasalima yanata daddaga labulayen dakin yana laluba sauran gurare irinsu socket na dakin,switch da sauran gurare saboda tsaro,gudun samun wata boyayyar camera da basusan da ita ba. Baisan ta fice ba sai da yaji alamun jan qofar,ya bi qofar da kallo kafin daga bisani ya dauke dubansa daga wajen yana ci gaba da abinda yakeyi. Wannan dukka ba take taken raini bane ba?,amma ba wanda ya jawo masa illa farouq,kuma tabbas zaija kunnensa,bazai yiwu cikin qasashe biyu da xasu sake zuwa a gaba ya qara hada musu guri ba,duk da kusan duka qasashen ba inda baida gida mallakin kansa uku ko hudu,da kansa zai zabi gidan da yakeso saboda gudun faruwar hakan. Sai daya tabbatar da lafiyar dakin sannan ya soma rage kayan jikinsa,don bazai iya bacci haka ba,ko wankan ma bayajin zaiyishi sai idan ya tashi,duk da farouq nason rage masa jin dadinsa.....don da gaske hutu yazoyi,yazo.ya huta inda ba zaa sashi magana bs ko ciwon kai. Turus tayi sanda ta fito parlor din,wayam ba kowa sai dan motsinsu daga dakunansu. Bin duka qofofin dakunan dake kulle tayi da kallo,saita rasa meye abunyi. Da kunya dai ta jewa dakinsu anni wanda ta tabbatar a yanzun suma hutawa sukeyi,idan ma taje tace mata me?. Ba zata zauna daki daya da d'anta ba wanda mijinta ne a qa'ida duk duniya kuma haka suke kallonsu?,wanda sukasan sahihin zamansu mutanene daidaiku.......hatta da amna bata sanya ran ta gama fahimtar komai da komai. Rasa madafa tayi,dole a qarshe kwanyarta ta gaya mata bata da sauran wani abunyi illa ta koma dakin ta rungumi haquri na yau,zuwa gobe saita nemawa kanta dalili da mafitar da zata sanya a raba dakin. Daidai sanda ya isa bakin qofa da zummar kashe switch na qwan ita kuma ta murza qofar ta shigo. Baikai ga kashewa ba,don haka tsaf ta ganshi. Murdadde kuma qaqqarfan muhammad fu'ad jadda,ma'abocin daga qarfe da dukka surar jikinsa ta koma ta qarfafan maza,saidai surar batayi muni ba,ta dace da zatinsa ta kuma shekarunsa. Babu komai a jikinsa sai gajeran wando iyakar cinyoyinsa,gaba daya faffadan qirjinsa dake lullube da ni'imtaccen tattausan gashi ya tare kusan rabin qofar dashi,abinda ya sanyata saura kadan ta fada qirjin nasa,abinda kuma ya saka tsoro ya kusan sanyata shidewa,ta daburce duka cikin qanqanin lokaci,saita juya da hanzari da zummar ficewa a dakin don ba zata juri ganinsa haka ba. Sosai ya raina sanya hannu qwaya daya ya jawota zuwa gabansa,yanzun hakan ma yayi mata,ya kuma ajeta a gefe,ya saka hannu ya murza key din qofar ya rufe dakin,ya cilla key din saman gado sannan ya juya yana kashe switch din. Dakin yayi duhu,saidai duhun bazai hanaka ganin komai dake dakin ba amma bada fitacciyar suffarsa ba. Takawa yakeyi hankalinsa kwance zuwa gadon kaman ba'a tube yake ba "Sannu a hankali wataran zan baki mamaki tunda na hanaki wannan rainin hankalin da kikemin kaman dodo......sai kace a kaina kika taba ganin namiji a t......" Sai kuma bai qarasa ba yaja tsaki sanda yake dora kansa saman pillow hadi da lumshe idanunsa ya sauke numfashi. Komai ta kasa cewa saboda tsoro daya cakude da takaici. Ta zuba ma fuskarsa idanu duk da bata iya ganinta sosai tana jin bacin rai yana taso mata. Ta tsani koda kalma daya ta hadasu shi yasa take kauce masa,don kowacce magana zai gaya mata bame dadi bace a zuciyarta da kunnuwanta. Don kanta ta samu waje ta nade tana curewa guri daya bayan ta gaji da tsaiwa,don tuni yaja duvet ya rufe jikinsa dukka gaba daya har saman kansa. Tsakiyar baccinsa ya dinga ganinta tana nufoshi cikin swimsuit sanda yake zaune daga gaban swimming pool din yana kallonta. Kanta tsaye ta yiwa kanta mazauni saman cinyarsa,yayin da albarkatun qirjinta yake tokare masa fuska da wani irin salo na tsokana,baisan ya akayi ba ya samu kansa da goga fuskarsa a jikinsu,abinda ya tashi kowacce tsiga ta jikinsa kenan,kowacce kafar jikinsa ta soma fidda zufa,ya kuma jawota ya qanqameta da kyau yana cusa fuskarsa tsakiyarsu kaman me neman taimako. Wani birkitaccen salo takeyi masa,wanda ya taimaka wajen fitarsa a hayyacinsa,ya kuma juyeta saman sun lounger din da yake kai,take al'amura suka fara kankama tsakaninsa da ita. Karar fadawar wani abu ruwan dake gabansu shi ya farkar dashi har a zahiri. Idanunsa ya runtse da qarfi yana jin wani abu yana yawo a sassan jikinsa. Yana jin tamkar a yanzun idanu biyu komai yake faruwa,wani irin zazzafan yanayi da ya jima bai tsinci kanshi a ciki ba saboda yadda yake yawaita yin takatsantsan. "Why?,why?" Ya tambayi kansa da kansa muryarsa can cikin maqogoronsa. Me yasa zata biyo shi har baccinsa?,ba zata qyaleshi ya huta ba kenan?. Ko a baya da yake fuskantar irin mafarke mafarken nan......babu guda daya daya taba ganin ainihin fuskar ko gangar jiki,wannan shine na farko da komanta ya bayyanar masa a zahiri. Fitowarta daga toilet shi ya sanya ya ware rinannun idanunsa a kanta. Duk da bata iya ganinsa sosai amma taga alamun ya farka daga baccin. Dama ya kamata ace ya farka din,tunda agogo ya nuna mata lokacin magariba yayi,amma kuma batasan yadda zata tayar dashi ba,to ya samawa kansa lafiya daya farka din. Dakin ya mata duhu saboda yadda duhu ya soma mamaye garin,saita laluba har ta dace da makunnin ta kunna qwan dakin,take haske ya gauraye ko ina tarwai. Idanunsa ya lumshe yana cusa shi cikin pillow "Oh shit" Ya fada qasa qasa. Qoqarin tashi yake kafin hakan takai ga faruwa sai gashi ta rigashi kunna hasken dakin. Ta yaya zai iya tashi ya miqe ya wuce zuwa bandaki a yanayin da yake ciki?,tambayar dashi kansa baisan amsarta ba. A nata bangaren ta gama gajiya da zaman dakin,burinta kawai ya budeta ta fita,bataga wani alfanun zamansu suna musayar numfashi ba idan ba tsabar muguntar nashi bane ya motsa. Ta duba luggage dinta ma sam bata ga hijab ba,sai mayafai ta hada kusan uku dasu zatayi sallar. Ba ita ta hada kayan ba,zata iya cewa batasan ma meye a ciki ba,anni ce ta musu siyayyar duk da uban lodin kayan da suke da wanda ita kanta batasan adadi ba,amna kuma ta shirya mata tace basai ta buda ba ta saka mata komai,ta kuma biye matan bata duba ba. Bashi da wani sauran abinda ya rage illa dole ya tashi din,don haka ya tattara uban duvet din ya nadeshi a jikinsa ya sauka yana wucewa toilet din a gurguje. Ta danyi mamakin shigarsa toilet fa duvet,amma sai kuma sai ta kauda abun daga ranta ta shimfida abun sallah tana jiran lokaci ya qarasa cika. Ya jima a toilet din yana qoqarin ganin yanayinsa ya daidaita,yasha azaba qwarai har ya dinga tunanin anya yau zai tsallake kuwa?. Kowanne jijiya ta jikinsa aikawa take da saqo,sai bayan kusan minti talatin ya samu yanayinsa ya dawo daidai,amma abinda yakeji a jikinsa bai sauya ba tunda jikin bai samu abinda yakeso ba. Dukka jikinsa ya wani mutu qwarai da wata irin kasala data sakar masa da nauyin jiki,haka yayi wanka ya daura alwala ya fito. Sauqinta daya data samu tana sallah sanda ya fito din,don da alama a yanzun ma gaba gadi ya fito abinsa,ya buda kayansa ya shirya cikin Moroccan jallabiyya black me adon golden din zare,ya saka qaramae gold din hula ya feshe jikinsa da turare sannan ya dauki key ya bude qofan ya fice don zuwa su hada jam'i dasu saddiq kaman yadda suka saba duk sanda sukayi tafiya a qasashen daba masallaci a kusa da masaukinsu. Fitarsa sai taji kaman ta samu 'yanci ne,ta kammala sallarta ta fada wanka. Koda ta fito lokacin isha'i yayi,tasan qwarai tana da nauyin wanka,amma na yau ya haura na kullum saboda ba qaramar wahala tasha wajen gane yadda zatayi amfani da kayan bandakin ba. Da karsashinta ta isa ga luggage dinta,saidai kaf ta cajeshi babu wata suturar arziqi da zata iya sakata ta fita,sai uban lingerie data zuba mata kaman karuwar dake neman customer. Takaici ya sanyata komawa ta zauna ta rafka tagumi,kusan mintina ashirin ta kashe a haka kafin ta jawo akwatin ta sake birkiceshi ko zata dace. Baqinciki ya sanyata daga lingerie din daya bayan daya tana qare musu kallo. Kaya ne na rashin kunyar da ita kanta kunyar wasu a ciki takeji idan ta daga "Amna kin kwafsamin.....kin kasheni......shi yasa kikace kada na duba kayan" Ta fada a fili daidai sanda ta daga wata lingerie din da aka yiwa wani yanka na wulaqanci,aka fidda gidan mama daga qasa kuma aka mata wata huda. Shigowarsa da sallamarsa duka lokacin guda ne,ta saki rigar da sauri ya bita da kallo,ta miqa hannu da gaggawa ta tattareta ita da sauran tana zubawa a akwatin sannan ta miqe. Tanason masa maganan ya turo mata amna amma batason halinsan nan,ya kammala abinda yakeyi ya doshi hanyar fita "Idan kin gama abinda kikeyi din ki fito za'ayi dinner" "Don Allah ka turomin amna" Ta katsi numfashi tana fadi da sauri har sai daya waiwayo ya kalleta,karon farko da magana ta nutsuwa da respect harma da begging a ciki ya taba hadasu,sai baice komai ba ya fice abinsa. Harara ta ballawa qofan tana jin baiken kanta,me yasa ma ta roqeshi?,gashinan ya yarfata a banza,dama me hali ai baya fasa halinsa,ta tsugunna tana hade kayan cikin takaici. Saidai ko gamawa batayi ba amna tayi sallama,ta tsaya daga qofa tana leqowa a darare. "Ki shigo malama" Ta furta tana jifanta da harara. "Shigowa makwancin hamma din kai tsaye haka hadari ne" Ta fada tana shigowa kaman yadda ta buqata. Tana mamakin irin tsoronsa da sukeyi da yadda suke kiyayarsa qwarai. "Yau fada zamuyi dake har anni saita shigo sasanci" "Me nayi adda?" Ta tambaya tana waro idanunta gami da dafe qirjinta "Kayan da kika zubamin dama kenan amna?" Ta tambayeta tana dan kama kunnenta. Dafe kunnen tayi dariya tana kamata,duk da riqon babu zafi amma tace "Wayyo kunnen autar anni......aradu anni ce tace duka na zuba miki su,ni kuma da naji tace haka saina kwashe wadancan......bansan mix ya
Chapter 80 · 0% Book details