← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 215

Sashe 132

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sau uku tana juyawa tana qare musu kallo cikin daren,idanunta duka suna tsakanin huda nadra da haneefa da kuma momma bahijja dake kwance saman nata gadon. Tashi tayi ta zauna sosai,zazzabi takeji yana sake qaruwar mata,ko amai din sai data sakeyi dazu amma bata bari kowa a cikinsu ya gani ba,saboda wannan farincikin da wannan walwalar take so taci gaba da gani saman fuskarsu,batason ganin komai da zai bata wannan yanayin. Hadewa jikinta tayi waje daya tana jin sanyi,yayin da can qasan ranta ya cika da ambatonsa. Tana ji ya gama yi mata komai na rayuwa.......tanaji ya gama mallakar komai nata... ..gangar jiki da kuma zuciya,tana jin ya sayi wani babban gurbi a rayuwarta da rufe babinsa ba abu bane me yuwuwa. A yanzun daya qarasa cika mata burinta..... Sun gaya mata abubuwa masu yawa da ya yiwa rayuwar su wanda bata taba kawowa mafarkinta hakan zai kasance ba. Wani irin gini da ya yiwa rayuwarsu har ya zarta nata mafarkin a kansu.....ko yanzu ta fadi ta mutu ta godewa Allah......tana da dukkan tabbas da yaqini akan rayuwarsu. Haka kawai takejin kaman yayi tsaho ace ta jirayi gobe kafin tayi masa godiya.....sai takeji ya cancanci ta abokanceshi a wannan daren. Tafi kowa sanin yadda waje yake masa qunci idan ta matsa......tafi kowa sanin yadda yake qulafucinta da son kasancewarsu tare. Tun saukarsu bai nemeta ba ko a waya,tasan kara kawai yayi mata bawai don hakan yakeso ya kasance ba. Zazzabinta da komai da takeji ta hadiye,ta shiga bandaki ta sake wanka,ta dawo cikin dabara tana tunanin inda zataga luggage dinta. Ba luggage amma akwai wani bag daban data shigo dashi,kusan duka sabbin kaya ne a ciki,saita samu kanta da neman rigar da tasan zata dace da yanayin. Tsaf ta gyara sumarta cikin hair mist dinta,ta kuma tajeta ta saketa a gadon bayanta. Yadda farar tattausar rigar maras tsaho ta zauna mata a jikinta ita kanta ya burgeta,komai ya fito das das a jikinta da wani irin salo me daukan hankali,saita nema dogon hijabin daya rufe mata jikinta ruf ta aza saman rigar,ta dauki wayarta ta taka a hankali tana fita a dakin. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ 113 113 Waiwaye ta dinga yi don ta tabbatar da kowa bai ganta ba,ta qarasa qofar dakin a nutse tana fatan samunta a bude. Taci sa'a kuwa,don tana murdata ta bude din,sai ta tura ta shige a hankali. Abinda bata sani ba tayi shuka idanun makwarwa,daidai sanda maamah ke fitowa daga dakinta da zummar sauka floor din qasa ta rage zaman kadaici koda cikin reception ne. Dif wuta ta dauke mata,wata qaqqarfar guduma ta saukar mata. Lalubawa tayi ta nema kujerun da suke ajewa jifa jifa ta cikin hallways din ta zauna ganin duhu yana nemam giftawa idanunta tana maida numfashi,maganar da sukayi da ita ta qarshe ta dawo mata. "BANA SONSHI....BAZAN KUMA TABA SONSHI BA.....BANMA SHIRYA ZAMA DASHI BA.....AKWAI LOKACIN DA XAN TAFI.....AMMA ZAN TAFI NE KAWAI SANDA NI NA TSARA NA TAFIN,BAWAI SANDA KE KIKA SHIRYA FARUWAR HAKAN BA". kai ta jijjiga tana sake dilmiyewa cikin mamaki. Wato ita yarinyar take rainawa hankali kenan?,ita takewa wasa da hankali?,wai ya akayi kaman ita mariya yarinya 'yar cikinta wadda inda fuad mace ne yaci ace jikarta ce amma take wasan kura da hankalinta haka?. Dukan kujerar tayi ta miqe tana komawa cikin dakin,zata kasa ta tsare taga iya awannin da zata dauka kafin ta fito a dakin. Matsakaicin haske ne a dakin,da alama ya kashe kowanne qwai banda side lamp din dake gefen Kujerar data hangoshi kwance samanta. Yana kwance sosai ya miqe dukka wannan tsahon nasa,hasken fitilar ya haske fuskarsa sosai. Qur'ani ne a bude kife a qirjinsa,da alama yana tsaka da karantawa bacci ya daukeshi. Baqar sumar nan dake habarsa da qasan hancinsa girarsa da zara zaran eyelashes dinsa sun sake qawata fuskarsa da wani irin annuri. Ita kanta saita samu kanta da qare masa kallo,har zuwa sanda ta isa gabansa cikin sanda. A hankali ta tsugunna a gabansa tana sake matsawa dab dashi,qamshinsa ya taso ya daki hancinta,abinda ya sakata lumshe idanunta ba tare data shirya ba saboda dadi da nutsuwa da qamshin ya saukar mata. Cikin takatsantsan ta miqa hannunta tana zare alqur'anin da yake rungume dashi,ta daga tana duba wacce surar yake. Alama ce saman ayar muhammadur rasulullah bisa dukkan alamu nan yake karantawa,ta motsa bakinta a hankali ta furta. "Sallalahu alaihi wa sallam" Ta sanya bakinta kan ayar a nutse tayi kissing nata sannan ta rufe qur'anin ta adanashi. Sake dawowa tayi ta tsugunna saitin fuskarsa tana qare masa kallo. Karon farko data karanci ainihin sassanyan kyau da Allah ya masa baiwa dashi. Ba banza ba yake da wani irin kwarjini da ba kowa ke iya saka idanunsa kan fuskarsa zuwa cikin idanunsa haka kai tsaye ba,labbansa sukayi mata kyau sosai,ta miqa hannu tana taba dogayen eyelashes dinsa sannan ta sauko zuwa labbansa masu kalan red tadan taba. Motsawar da taga yayi sai ta janye hannunta da sauri zuciyarta tana bugawa,dan gyara kwanciyarsa yayi kadan zuwa hannun damansa,abinda ya bashi daman fuskantarta sosai itama ya bata daman ganin fuskarsa sosai. Hannunta ta sake miqawa ta kama yatsunsa,a hankali ta motsa labbanta. "Ka dage sai da ka farauci wannan sabuwar zuciyar......ka dage da qarfin zuciya dana damtse sai daka fanshi wannan ruhin da baisan soyayyar kowa ba saita 'yan uwansa......ka nuna sadaukantaka da jarumta har sai daka yaudari zuciyar marainiya ameenatu......wallahi na sallama......sabreen ta sallama maka,ta mallaka maka......ta kuma miqa wuya.........na baka dukkanin soyayyata dari bisa dari......ka cinye yaqin.....kayi nasara......na karbi faduwar ta wannan bangaren muddin wannan shine faduwar......ka mamaye DUNIYATA ka sabuntata da irin DUNIYAR kowanne mutum.....nima kaine DUNIYA TA" ta qarasa fada tana kallon zara zaran yatsunsa masu farare qal din farce kaman baya taba komai dasu. Motsin da ya dan sakeyi ya sanya gabanta faduwa "Idan yana jin duk abinda kika fada fa?" Wata zuciyar ta gaya Mata,saita fidda idanunta dukka waje tana miqewa da hanzari a ranta tana cewa. "Da na gama jin kunya". "Ina zaki tafi kibar zuciyar da kika gama lugiguitawa?" Muryarsa ta daki kunnenta me dauke da alamun bacci yatsunta na cikin wanda yaci nasarar cafkesu sanda take juyawa zata fice. Zare idanunta dukka tayi gabanta na harbawa,kada dai ace yana jinta?. "Zan iya cewa kunnuwana sun manta dajin wata kalma me dadi a rayuwarsu irin na yau......karki tafi ki barni cikin wayen wadannan kalaman" Yayi maganar yana saukowa daga kujerar sannan ya sakar mata hannum yana takowa bayanta. Kane kane yayi a bayanta yana rungumota ta baya ta hanyar aza hannuwansa saman ruwan cikin ta. Ya cusa hancinsa ta wuyanta yana zuqo daddadan qamshinta daya soma aike saqo sassan jikinsa da wani irin hanzari (Karki raina turare,kada ki rabu da turare amatsayinki na matar aure,duk yadda zan gaya miki rawa da muhimmancinsa a wajen matar aure ba zaki gane ba......amma hatta da sha'awa turare yana tayar da ita,musamman irin masu sanyi da laushin qamshin nan,amma ki lura,akwai inda za'ace ki kama kalar qamshi guda da mijinki xai ganeki dashi,tom wani.namijin ba haka yake ba,wani yafison kullum da kalar da zaiji a jikinki,bayason kala dayar nan,saiki fahimci mijinki wanne iri ne). "Sabrrrrr" Ya kirata a rikice yana jin wannam feeling din da yakeji a kanta yana taso masa. "Hamma" Ta amsa masa itama idanunta a lumshe tana jin yadda saukar hannunsa a jikinta yake haifar mata da wani irin yanayi me wahalar fassara. Magana yakeson sakeyi mata amma ya kasa,sai kawai ya fara tattara hijabin zai rabata dashi. Hannunsa ta riqe sannan a hankali taja baya,ta tattare hijabin da kanta ta zameshi daga jikinta ta wurgar dashi gefe daya. "Ya subhanallah" Ya furta bakinsa yana rawa. Zai iya cewa bai taba ganin sanda tayi masa kyau irin yau ba,tayi ado sosai da gashinta irin yadda yakeso ya gani. Kowacce boyayyar sura ta jikinta ta bayyana yadda yake da muradin ya gani,kafin ya qara kowanne motsi ta qara sanda bashi mamaki ta hanyar balle hannuwan rigarta suka zame ta saka hannunta da kanta ta zare rigar zuwa qasa sannan ta fara takowa har inda yake ta iskeshi. Wani irin mahaukacin tarba yayi mata cikin tsananin yunwarta,yana jin kamar yau ne rana ta farko daya fara sanyata cikin idanunsa,martanin data soma maida masa ya sanya yaji bashi da wata jarumta sam,yana gudun suci gaba da tsaiwa tsaf zasu iya zubewa,sai ya sauqaqa musu ya dauke abarsa ya qarasa da ita inda sukafi wayo. Kirif ya rufe musu fuskokinsu da mayalwacin gashinta dake fesar da qamshin hair mist dinta. Gaba daya ya shiga wani rudani da bai taba shiga irinsa ba tsahon kasancewarsu tare. Komai yayi mata saita maida masa martani,duk inda ya nufa kafin ya qarasa tayi masa jagora,sai yaji kaman ya kurma ihu ko xai samu sassaucin dimuwar dame yawo cikin kwanyarsa. Yanaso ya gaya mata ta sassauta saboda kada ta jashi yayi mata babban aiki,don yana iya jin dumin dake jikinta,amma inaaa ta qarasa dimauta kowanne tunani nasa,ba abinda bakinsa ke iyayi banda furta sunanta a jejjere da bada zazzafan kiss da karbar martani daga gareta. "Ki soni sabbrrrrr......na rantse da Allah ni kadai nasan me nakeji a kanki......ki soni,zan miki komai....zan zame miki komai.....zan mallaka miki komai". Fuskarsa ta riqe sosai cikin hannuwanta tana dubansa,gaba daya kamanninsa sun sauya ya birkice sosai. "Muhammad" Ta kirashi "Fu'ad" Ta maimaita "Muhammad jadda......ameenatu ta yarda ta soka......ameenatu ta yarda ta mallaka maka kanta da rayuwar ta,ameenatu ta zama taka har gaban abada....dakai da ameenatu yanxu duka abu daya ne.......ka gayawa kowa wannan cikin alfahari taqama isa da samun tabbaci" Ya riga ya sallama,gaba daya ta gama susuta qwaqwalwarshi......yasan a yau kam duk wanda yayi kusa da yawa da dakinsa zai iya jin motsin da xai saka zargi a ransa,baisan me yake yi ba kaman yadda ya manta wayeshi. A lokaci ji ya dinga yi inama akwai wata duniyar ta daban da zai iya maidasu shi da ita?,duniyar da babu kowa saisu kadai?,wannan albishir daya samu daga bakinta......daga gari me tsarki yafi komai masa dadi da zame masa tarihi cikin rayuwarsa. Wani irin dare suka raya,daren data sakar masa dukka ragamarta,ta cika masa mafarkinsa ta hanyar bashi kowacce gudunmawa da cikakken hadin kai,saiga muhammad fu'ad din yana mata kuka sosai kaman qaramin yaro. Kukan daya sake susutata
Chapter 132 · 0% Book details