← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 181 OF 215

Sashe 181

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

suna kallon ita din uwar kowa ce da take riqon yara turmus,don haka ta daga kanta kawai tana cewa. "Eh haka ne". "Yauwa.....mun samu cikakken labarin qawancenku......yadda kikayi silar hada auren d'anki da matarsa ta yanzu sabreen da dukkan wasu hujjoji na riqe qannenta a bisa cikar wannan buri naki.....kidnapping diyar alhaji hamza da kidnapping tata d'iyar wato laila da a yanzu kika bamu tabbacin kuna tare....". Wani jibgigen abu ne taji ya saukar mata tsakiyar kanta wanda ya sanya numfashinta yaso riqewa iya wuyanta. Ita hajja zata yiwa haka?,ita hajja zata wulaqanta?,ita hajja zata jajibowa taron manema labarai?,ita hajja zata tonawa asiri?,ya akayi ta manta da ita bata sanyata mutum ta uku daya kamata ta shafe labarin su ba,me yasa bata b'atar da ita ba?,me yasa ta barta taci gaba da shaqar iskar 'yanci?. Juyawa tayi kawai don komawa ciki,saboda tana jin bai kamata tace komai ba gudun tonuwar asirinta gaba daya wanda ta fahimci fiye da rabinsa ya yaye. "Ranki ya dade ya zaki koma kuma?" Zaqaqurin dan jaridar ya fada. Waiwayowa tayi ta zube masa wani kallo. "Ni ba uwar qaramin mutum bace,bani da lokacin magana daku kai tsaye haka.....idan ka matsa kuma kasan waye d'ana,ba aikinka kawai zaka rasa ba.....har....." Sai kuma ta dakata tana kwabar kanta duba da irin cameras din dake fuskantarta. Kallon kallon suka farayi tsakaninsu,don kowa da abinda ransa ke raya masa da yanke maganar da tayi bata qarasa ba. Ganin ta dauke musu wuta gaba dayansu saita taka tana komawa ciki cikin jan qaqqarfan tsaki. "Akwai batun aika b'ata gari da kikayi gidansa don yiwa matarsa fyade da sunan baki sonta.......wannan batun gaskiya ne?". Wani irin suka maganar tayi mata a qirjinta,har batasan sanda ta saka hannu ta dafe saitin zuciyarta ba. Haki ta soma yi tana jin kamar qafafunta ba zasu dauke ta ba,dole ta fara kiran sunan laila saboda tasan duk 'yan aikinta yau basunan cikin mancewa da tarin 'yan jaridar da suke neman tabbacin lailan tana tare da ita kaman yadda cikin rashin sani ta basu tabbacin. Kome takeyi,komai girman bacci ko uzurinta muddin maamah ta kirata saita bar komai. Kaman yanzun da take zaman cin abinci haka ta watsar dashi ta kwaso da gudu. Fitowar tata ta sake maida hankalin mutane kan laila din da dukkanin kamanninta da hajja harira da suka fito. "Lafiya maamah?,me sukayi miki?,me ya faru?". "Kamani muje ciki" Ta bata umarni a tsawace,abinda ya sanyata kamata dukka jikinta suna rawa. "Da gaske kece diyar hajja harira?" Wata cikin su tayi caraf ta jefa mata tambayar sunason tabbatar da maganar juya mata hankali da sukayi. "Eh 'yarta ce......amma yanzun daidai nake da baiwa wajen maamah......yadda takeso take buqata haka zanyi,koda ya kama na rabu da ita hariran" "Ke laila kama bakinki mu wuce ciki!" Maamah ta fada da hanzari gudun kada tsananin mallaka ya sanyata nunawa duniya abinda zai sake zame mata abun fada. "Laaaaa haila ha'illallahu.....muhammadurrasulillahi" D'aya daga cikin mata 'yan jarida dake wajen ta kasa daurewa abinda ya farun ta saki kuka tana tafa hannu. "Wallahi 'yar hajja harira ce,da gaske ne,da gaske aikin juyar da hankali tayi mata bayan tayi kidnapping nata......da gaske ne,gashinan diya tana neman mancewa da uwarta?" Wannan kalaman sun sauka daidai kunnen maamah,wanda hakan ya sanyata runtse ido,tsananin jin zafin hajja yana sake ratsata tare da alwashin daukan fansa a tare da ita. "Ki gayawa malam sa'adu ya fidda mutanen nan,idan ba haka ba zai fuskanci fushi na" Umarnin data bawa laila kenan,ta kuma saka kunne tana jiran daina jiyo hayaniyarsu daga nan inda take. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ 151 *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX Tsahon mintuna talatin ta sauke idonta akan takardar da fu'ad ya ajiye mata,ta zubawa littafin idanu tana lissafa adadin yawan shafukan da yake dasu. Ya fadi cewa zata iya cika littafin harma ta qaro wani....tayita rubuta dukkanin abinda takeso.......wannna babbar dama ce a gareta kenan na zama Mulitibillonier?. Murmushi ta saki ta soma yunqurin daga hannunta ta miqashi don dauko littafin,amma abun mamaki sai taji hakan ya gagara. Ta sake yunqurawa a karo na biyu da zummar gwada daukar nan ma shuru ne hannun yaqi sarrafuwa. A zabure ta maida dubanta ga hannun nata cikin wani irin kidima da dimuwa tana kallonsa. Hannunta ne dai......hannunta ne data sani shekara da shekaru......hannunta ne da ba wani abu daya canzashi.........amma meye ya kawo qin daguwarsa?. A karo na uku ta tattaro dukkanin qarfinta zata dagashi ya sake motsuwa koda wasa,a birkice ta maida hankalinta kan daya hannun tana qoqarin motsashi shima. Still shima abinda dan uwansa yayi shi yayi mata. Matuqar qololuwar tashin hankali taji ta shigeta,wani irin mahaukacin gumi ya yanke mata. "Me hakan yake nufi kenan?,wani ne yayi min asiri?,ko wani ne yayi min tsafi?" Ta tambayi kanta da kanta. "Kai inaaaa.....a irin wannan lokacin?,a lokacin da dama tazomin?" Ta sake tambayar kanta a fili kaman wata tababbiya. "Bazai yuwu ba" Ta fada tana qoqarin miqewa don ta gani ko qafafunta suna aiki?. Miqewar datayi aniya jikinta ya gaya mata bashi da wani sauran motsi me qarfi,qafafun suma suka shaida mata basu da wani sauran qarfin da zasu dauki nauyin gangar jikinta ta hanyar warbar da ita ta zube a qasa tana kifawa saman fuskarta. Wani irin matsanancin ciwon kai yakeji,wani irin yanayi da yakejin kamar jikinsa yana dab da gazawa. Yana dafe da kanshi tsahon mintunan da suka dauka suna tafiya a motar,har zuwa sanda ya buda bakinsa a hankali yayi magana da driver din "Badawa zaka kaini......ba gida ba" A yanzun ba abinda yafi buqata irin ya kebe,so yake ya kebe shi daya,bayason magana da kowa bayason kuma hayaniya. Karya kan motar yayi suna komawa daya hannun. Tafiyar mintuna ashirin ta kaisu m,already yasan gidan,gida ne madaidaici daga waje,saidai kuma daga cikin yana da yalwa da wani irin yanayi da aka tsara me tsananin burgewa. Yakan jima baizo gidan ba,yana ma mantawa dashi sau tari,saidai duk sanda yake buqatar ya kebe ko ya huta a nan din yake zama har zuwa sanda ya gamsu da yanayinsa ya koma normal mode dinsa. Tun a parlor din ya zube,karo na farko da yaji yana buqatar yayi kuka,karo na farko da ya buraci inama ace shi din yana cikin sahun mutanen da hawaye ke fita a fuskarsu da wurwuri?. Hawaye yake da buqatar ya zubar sosai saboda qirjinsa dama zuciyarsa sun gaji da daukan abinda suke dauka din. Koda zai iya hana kanshi fitar dasu to ba a irin wannan lokacin ba,a yanzun kuka yafi buqatar yayi bawai yaci gaba da nuna jarumtarsa ba. "Astagfirullah ya Allah......astagfirullah" Shine abinda labbansa dake motsawa suke maimaitawa yana jin yadda qirjinsa ke sake suya idanunsa suna sake d'aurewa da wani irin zafi da kuma radadi. Wani sabon babi ya bude na tariyar rayuwarsu,tun daga sanda ya bude idanunsa ya zama mutum cikakke zuwa yanzu. Bai tsinci komai tattare da maamah ba banda haihuwarsu da tayi......ko a sanda take rayuwa tare dasu,yadda take mu'amala dasu haihuwarsu ta zame mata kaman wani nauyi wahala ko dawainiya.....abbansu kusan shine komai nasu......abbansu shine duk wata wahala da dawainiya tasu,abbansu shine wankansu abincinsu,shirin makarantarsu da komai na dawainiya......yayi a gida ya fita yayi a waje ya kawo musu. Zuwa yanzu baisan sadaqaul jariya na abubuwa daban daban dubu million nawa yayi saboda shi ba......yana fatan ko a ina yake ya bishi cike da samun salama cikin kabarinsa da rayuwarsa ta barzahu. Da taimakon ambaton sunan Allah da yakeyi ya samu nutsuwa ta fara dawo masa. Yayi amfani da wannan damar ya miqe ya shiga toilet ya daura alwala. Dawowa yayi ya kunna ya kunna TV din dake kashe,ya lalubi tashar saudi qur'an ya qaro volume din ya karade parlor din gaba daya. Cikin kujera ya nutse,idanunsa a lumshe yana sauraren karatun gami da bin ayoyin tare da shaik abdurrahman assudais. Yana karatun yana fahimtar ma'anar ayoyin,abinda ya sake taimakawa wajen bawa zuciyarsa da ruhinsa nutsuwa. A nan gurin yayi sallar la'asar,magariba ma ta ruskeshi duka ba tare da ya sani ba. Itama magrib din a nan yayita,ya jima saman abun sallah yana addu'o'i har baisan adadin lokutan daya shafe ba,yadai duba ya tarar da lokacin isha'i har ya shiga. Isha'i dince ya fita a daddafe zuwa masallacin dake cikin layin cikin shiga ta bad da kama,baya son kowa ya tsaidashi don bazai iya dogon magana ba. Ana idarwa ya taso shida jordan sukayo gida,jordan din ya dan dubeshi cikin matuqar jin tausayinsa qauna da kuma kulawa. "Sir......ko za'a aika a karba maka abinci gurin madam?,if not a maka order daga wani eatery din?". Kai ya girgiza,a halin yanzu bayajin yunwa,still kuma bayaso ma sabreen ta ganshi a yanayin da yake ciki. Tashin hankalin da take fuskanta ita kanta yayi yawa,tunda ta dauki cikin nan bata huta ba,tana stressing kanta da yawa akan duk abinda ya shafeshi......is over,ya kamata ta huta hakanan,ya kamata ta samu peace of mind......yana shawarwarin yin nesa da ita har sai abubuwa sun lafa,shi kansa yana jin zaya dauki hutu har sai komai ya koma daidai. "Sakamin order lite abu please" Yace da jordan din yana wucewa cikin gidan. Saman sofa ya zauna,ya dauki wayarsa dake yashe a wajen wadda sam yama mance da ita. Saqonni da miscalls rututu,amma duka na sabreen din yafi yawa. Ya saki dan qaramin murmushi bayan ya gama karanta wani saqonta na qarshe.....finally ya samu wata kyakkyawar zuciya data damu dashi da gasken gaske,finally ya samu wani ruhi dake craving for him.......finally ya samu wannan madadin da yake qishirwar samu. _"na kiraka na maka saqo har sau babu adadi amma babu guda daya daka amsamin.....tom.....Even if you're ready to live without me,I'm not ready to let go,ko yaushe zan kasance a tare da kai,koda hakan baida tsada ko daraja a wajenka,bana saba alqawari,forever. Yours mom of triplet"_ Har tsakiyar zuciyarsa yaji saukar da saqon yayi masa. Wata soyayya ta musamman tana sake huda zuciyarsa,qaunar 'yan tayi guda uku dake kwance a cikinta suna sake lullubeshi. _You're the missing piece that makes me whole,without you,life wouldn't be the same,forever with you is where i want to
Chapter 181 · 0% Book details