← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 215

Sashe 39

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

suka aurar da ita ga maza mabanbanta a lokaci guda,to ita din mallakin na farkon ce(wanda aka fara daura mata aure dashi)_ 34 Minti daya biyu uku har zuwa biyar bataji motsin komai ba,wannan ya sanya tayi tsammanin yabar falon ne,don haka ta juyo a hankali tana sake zube idanunta a wajen da yake. Haushi takaici da bacin rai suka hadu suka lullubeta ganin aikinsa yake hankali kwance,sai ta gyara tsaiwarta sosai tana fuskantarsa ganin ya lullube wannan faffadan qirjin nasa,wannan ya dan rage mata kaifin abinda takeji,duk da cewa cinyoyinsa dake a waje nason sakata a razani da tsoro. Rasa ta yadda zatayi calling attention dinsa tayi,sai ta danyi gyaran murya kadan cikin qufula da fusata. Minti guda kaman baisan tana wajen ba kafin ya motsa,ya daga kansa da idanunsa daga kan hasken system din yana zubesu a kanta da wani irin kallo na qurilla. Karo na farko yadda ya tsareta da ido taji kaman yanaso yayi mata nauyi,jajayen lips dinsa hasken fararen qwayar idanunsa wani abu ne da bata taba gani wajen wani d'a namiji ba sai a kansa,akan nasa ma a yau data masa kallo itama nakai tsaye. "Wayoyina nazo karba saboda ina da buqatarsu....... Akwai mutane masu muhimmanci a rayuwata da nake da buqatar na dinga magana dasu" Ta fada tana tsuke girarta da kyau tana kuma tura dan qaramin bakinta gaba wanda sam batasan ma tanayi ba,saboda zuciyarta cike take da haushi. A hankali ya sauke idanunsa zuwa saman qaramin bakin nata data tattara lips dinta duka ta turasu gaba. Wasu irin siraran lips da sai kayi tsammanin jambaki ta shafa musu. Tsigar jikinsa ta zuba kadan saboda bayyanar daya daga cikin abinda ke burgeshi a jikin mace yake kuma lissafin ya sameshi kenan,wato cute lips masu nau'in light pink ko red me haske irin nasa. "A hakar kamar cikakkiyar mace" Ya fada qasan ransa yana jan tsakin da baisan ma ya fito sarari ba. A duk lokacin da zai kalleta sake raina shekarunta yakeyi,hakanan a duk sanda zaya kalletan sai mamaki ya sake cikashi game da yadda ta samu cikakkiyar shaida da certificate din zama KARUWA. shi kam gaba daya ma baisan me yahau kan mazajen dake mu'amala da ita ba,a bisa qa'ida da yanayin halittarsa ta masa yarinta da yawa. Yanason macen daya tabbatar zata iya dauke lalurarsa komai girmanta,ire iren sabreen din guda goma yana ganin yafi qarfinsu nesa ba kusa ba,baima san abinda mazajen da ta dinga tatsewa me suke tsammanin samu haka daga gareta ba da har ta samu tasirin gusar musu da hankali. "Labari kike bani?.....ko tambaya kike?,ko daukan excuse?" Yayi maganar a nutse yana dage mata dukka girarsa guda biyun bayan ya dora qafarsa daya saman daya,ya kuma yi relaxing jikin makarin sofa din. Duk sai ta ji ya muzantata,akanme zai dinga mata tambaya akan abinda ya gama fahimtar inda ta dosa?. Tsaiwarta tadan gyara tanason hana kanta jin nauyin idanuwanta. "Amma dai cikin zamanmu ba sharadin tabamin waya.....wayata sirrina ne,bana tunanin akwai abinda ya shafeka a ciki" Ido ya zuba mata kamar bazaiyi magana ba,yanaso yaci gaba da karantar bayan karatun da yayi mata na binciken da yayi a kanta. Ya fuskanci akwai burbishi da tasirin rashin kunya tattare da ita. Yarinyar da ko saddiq ba sa'anta bane ballanta musaddiq ko farouq.....amma tana da zarrar tsaiwa ta fadi mishi magana yadda takeso. Wannan wani abune da ba wata diya mace data iya fuskantarsa dashi....kai koda dan uwansa namiji yana matuqar shakkar hakan. Uwa uba akwai tasiri na girman kai da rashin tsoro tare da ita,yanaso yaga ya zatayi handling wadannan attitude guda biyun da wadannan shekarun nata?. Kaman zaiyi magana sai wayarsa ta dauki tsuwwa,manhajar da yakanyi amfani da ita wasu lokuta da zata gaya masa cikakken sunan wanda ke kiransa koda bashi da number wayarsa ta karanto masa sunan fareeda Khaleed mustapha. Kusan a tare suka kalli wayar shi da ita,a nutse ya cire hannunsa ya kashe wayar gaba daya bayan yayi rejecting call din,amfanin manhajar kenan ta gaya masa wanda ke kira,basai ya saki aikinsa ya dauka ba ya zamana me kira baida wani muhimmanci har haka,saboda mutum ne shi mai darajta lokaci. Agogo ya kalla sannan a nutse ya maida dubanshi kanta bayan ya sauke qafafunsa duka qasa,abinda ya sanyata sake kame ganinta gudun kada idanun nata su gano mata abinda yafi qarfinta,don ta lura kamar bayajin nauyin zamansa a haka. "Kin tsallake iyakarki,kin shigomin part ba tare da Neman izini ko sallama ba......and kin tsaya kina ban labari akan abinda bai shafeni ba.......wai...." Ya fada yana tsuke fuskarsa sosai gami da maida qafafunsa saman table sabanin dazu dake kan sofa "Meye amfanin zamanki a gidan nan?.. Kina zaton na kawoki ne don na killaceki waje daya kiji dadin rayuwa?,ki samu tsaro kiji dadin ci gaba da qwamushe asusun mutane?,ko na kawoki ne don kizo kicinye min abinci na?,ko kin dauka na daukoki ne don wani abu daban?,thought ma dai nasan ba zaki taba mafarkin wannan shirmen ne wato SO ya sanya na kawoki ba....." Wani radadi takeji yana taba zuciyarta,abu daya da zata iya yabonsa akai takuma san ya qware akai shine baqar magana kamar tsohon mahauci,idaninta da suka fara canza launi takai kansa,ya gyara zamanshi sosai yana hade yatsun hannunsa guri daya yana maida dubansa kanta. "Kina magana akan sharadi yarjejeniya da sauransu......for now ma yakamata kisan me ya shigo dake cikin gidan nan.......Initially don ki gane me ake kira da respect........attitude dinki su koma irin na kowanne mutum.....secondly kuma..........ki maida min dukka kudina da kika debe.....don ban nema kudina saboda mata irinku su mora ba......" Wani kallo harrr ta bishi dashi,sai ya daga dukka girarsa sama "Yes......duk wanda zayaci kudina to yana da cikakkiyar hujjar da zata bashi daman cin in a polite way.......da naso a ranar da kika diba a ranar zan saka a kawomin ke har nan..... " Idanu ta zubawa Kyakkywar fuskarsa yadda yake bayani a nutse hankalinsa kwance. Ashe shi din ma mayen kudi ne?,kallon kitse akewa rogo?. Eh tasan tabbas ta cire kudade masu nauyi da yawan da ita kanta sai data girgiza,amma kuma bata dauka har xai sanya qulafucinsa akan kudin daya tsere musu ba har haka. "Baki da hanyar da zaki biya Muhammad jadda kudinsa?......zan taimakeki tsill dai don kada kiyi prison a banza.........daga yau ya daukeki aikin shara da gyara masa bedroom da kuma wanke masa toilet dinsa......zan biyaki kaman yadda yake biyan kowanni ma'aikaci dame aiki a qasansa.......but.....i will not pay you anything.......zanyi writing down komai har ki kammala biyana" Yakai qarshen maganar gaskiyar abinda yake fada tana fita daga cikin idanunsa. Soma tattare takardunsa yayi "You can go" Ya furta cikin halin ko in kula. A lokacin tana jin kamar ta qarasa gabansa ta amayar masa da dukka abinda ke zuciyarta,tana jin kamar ta isa gabansa ta nuna masa wace real sabreen,amma kuma wani sashe na zuciyarta yana kwabarta tare da gaya mata any mistake idan tayi itace a ciki. "Ya soma cin abincinki shine abinda ya kamata ki damu dashi bawai maganganunsa ba......if kikayi abinda zai sake sanya masa shakkan sakewa da gidan dukka ayyukanki zasu koma baya.... Sisters dinki zasu ci gaba da zama qarqashin hadari" Maganganun da suka fito daga qasan zuciyarta kenan,suka kuma sanyata tsaiwa cak daga takun data fara don matsawa zuwa gareshi. Remote din ya dauka ya bude mata qofar yana ci gaba da abinda yakeyi "Hey" Taji ya sake fada sanda ta sanya qafarta daya a waje,saita dakata ba tare data waiwayo ba "Mind you....banason qazanta,i don't want it,ki kiyaye". Da sassarfa da kuma hanzari ta soma sauka saga stairs din har kamar zata fadi. Kuka ne yakeson qwace mata amma bataso yaji ko ya gani,don ta yiwa kanta alqawari ba zata taba bari yasan lagonta ba. Baqincikinta yadda ya fadi mata dukka maganar da ke ransa,nata zuciyar da ruhi cike maqil da maganganu amma TARKON da take ciki yasa bazaiyuwu ta fiddasu ba. *_Washegari_* Tun shida na safe zuwaira ke kai kawo tsakanin shiyyarsu zuwa ainihin falon da kuma kitchen din. Jin shuru ba alamun tashi sai ta fara aikin gyaran dukka falukan da kuma kitchen din. Duk wani motsi da zataji hankalinta yana kai,tanaso ta samu cikakken bayani akan komai yadda zata zama cikakkiyar informer na maamah. Tanason bata duk kalar bayanan da takeso don tana son ta doke matsayin hajja harira wajen maamah. Ta kowacce fuska da kuma yanayi tanason ta taka matsayin da zata zama aljihun daman maamah a sanda burin maamah ya cika din. Itama tata zuciyar da ruhin cike suke da nata kalar burin da take fatan zuwan ranar wanzuwarsa. Wani irin qarfi ta sanya ta danne zuciyarta ta fito shirya masa breakfast,duk da asara akayi daren jiya na dukka girkin da sukayi,sai tashi tayi tsakiyan dare ta kwashesu ta zuba a inda ta saba zubawa. Yau din cikakkiyar shiga tayi,ta rufe jikinta sosai tunda ta fahimci ba ita kadai bace cikin gidan. Idanunta duka sunyi nauyi saboda kuka da rashin cikakken bacci. A hankali take ratsa falon hankalinta yana qofar kitchen din. "Barka da fitowa ranki shi dade" Taso ta tsorata kadan,don gaba daya ta manta da wata baba zuwaira a gidan. Ta sauke dubanta a kanta sanda zuwaira ke qare mata kallon qwaqwaf. A jiya batayi cikakken bacci ba sai data gama fahimtar inda kowannensu yake kwana ita dashi. A gaban idanunta ta sauko daga samanshi a gaggauce cikin bacin rai ta fada dakinta,abincin dataxo ta kwashe kuma baici ba,a daren itama bata kwanta ba ta sharhantawa maamah komai. "Ya zama dole na matsa mata lamba ta yaudaroshi ya zama a tafin hannunta" Abinda maamah ta furta kenan,tsoron taurin kai irin nasa yana damunta. Tasan halinsa da kafiya akan abinda baida niyya baiyi masa ba......amma zata sake yin amfani da qarfinta a matsayinta na uwa karo na biyu. "Barka kade" Ta amsa mata a taqaice ba tare data sake dubanta ba tayi kitchen "Nace ba,ba abinda za'ayi kuma?" "Babu....kije saina nemeki" Ta amsa mata a taqaice,don kwata kwata batason doguwar magana gaba daya. Da kallo zuwaira ta bita har ta shige kitchen din,sai ta saki murmushi tana ji a ranta ya kamata taci tudu biyu fa......bangaren maamah din da bangaren yarinyar.....abinda ta kwana kenan tana tunani akai,gwara tayi amfani da damarta,ta yadda koda gaba kome ya
Chapter 39 · 0% Book details