Sashe 110
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read
a hankali,abinda ya hadu da sanyin spirit din dana bakinsa ya bada wani abu daya sanya tsigar jikinta zubawa,tanaso ta janye hannun ya hanata,hakanan dole tabar masa hannun tana jin yadda jikinta duka ya mutu. "Ya daina zafin?" Ya tambayana yana dorawa kansa alhakin yankewartata. Kai ta gyada masa a hankali,burinta kawai ya gama yabar mata hannunta ya matsa daga kusa da ita din. Tsaf ya gyara,saida jinin ya tsaya da fita sannan ya kammale komai,ya qwalawa amna kira ta qaraso. "Ki dauke kayan.....ki kula da ita zanje na dawo,zamu taho tare da anni" Kai ta gyada tana tsugunna tana hade kadan gami da yiwa sabreen sannu. Kai kawai ta daga,ita bataga wani ciwo da taji wanda yakai girman sannun da take mata ba. Hannayensa ya zube a aljihun wandonsa yana kallonta,har sai da amna ta gaya hada komai suka wuce dakin annin. Ajiyar zuciya ta subuce masa,yana saqa abubuwa da yawa a kanta,sai sannan ya duba inda yabar farouq a zaune,baya nan,yasan kuma ya fita qilan yana jiransa cikin mota,don haka sai ya fara takawa a nutse yana barin parlor din ba tare da musaddiq daya basu space ya isar da saqon maamah ba. A mota ya samu farouq yayi d'ai d'ai suna shan hira da fanna dinsa. Kusan duka hirarsu yanzu tafi rinjaye ne akan shirye shiryen bikinsu. Baice masa komai ba ya miqa masa hannu ya karbi key din motar ya shiga ya tayar da kansa suka fara fita daga gidan gaba daya. Basuyi nisa sosai ba farouq ya kammala wayarsa,ya ajiyeta gefe yana cewa. "Sai yanzu hankalinka ya dawo kenan?" Ya fada yana kanne ido daya da sigar tsokana. Waiwayawa yayi ya balla masa harara sannan ya dauke kansa,kaman bazai tanka ba sai daga baya yace. "Ina baka shawara kaqi ji ko?.....ina gaya maka ka dauke idanunka daga kan lamarina ni da iyali na amma kaqi ji ko?". Sosai dariya ta zowa farouq,ya kuma soma yin abarsa yana cewa. "Allahu akhbar......dadin abun ma muma mun kusa aje iyalin nan muji abunda akeji......muji ya giyar soyayyar nan take bugar da mutum" Qaramun murmushi ya saki daya sake fidda kyan fuskarsa yana duban hanya. "Kota tashi bugar dakai farouq ba zaka ji abinda nakeji a kan sabrrr ba.....nata son daban yake a zuciyata......ban taba jin soyayyar abu a raina har haka ba.....bansan daga ina wannan qaqqarfar alaqar ke sake gina kanta ba duk wayewar gari zuwa faduwar rana" Yakai qarshen maganar yana furzar da numfashi a bakinsa. Ido farouq ya zuba masa.......tabbas zuwa yanzu ya tabbatar da gaske MAHAUKACIN SO fu'ad din yakewa sabreen,irin soyayyar da bai zaci zata kamashi ba har ibada. Miskilancinsa da komai nasa na dabanne.......amma zuwa yanzu soyayya tana sauyashi zuwa wani mutum na daban,idan ya zauna yana masa magana akan yadda yakejin sabreen din cikin ranshi abun yana bashi mamaki sosai......yana jin kaman ba me babban sunansa ba,wanda komai da kowa basu dameshi ba idan ka cire su da anni. "Inaji a raina da zuciyata......akwai wani abu cikin rayuwarta......akwai boyayyen abu.......i need to know farouq". "Kabi a sannu........da sannu zakasan komai din". Kai ya gyada masa. "Na sani......but am eager to know about everything about her......inaji kaman akwai sauran mutane daya kamata na hukunta bayan wadanda suke hannuna yanzu" Yayi maganar yana jin kalmar karuwa da kowannensu ya taba fada a kanta tana masa zafi har can qasan ransa. "But naji maamah tana nemanka ma...." Farouq ya fadi yana tsoron kada fu'ad din yaji amma yaqi zuwa. "Maamah kuma.......ba wanda ya fadamin" Ya furta haka kawai yaji gabansa yana faduwa. Ba kasafai kiranta ke zama alkhairi ba.....kai zaima iya generalizing cewa kiranta ba wani alkhairi ko abu me muhimmanci da d'a zai iya tsinta a cikinsa. "Musaddiq ta fadiwa.....bansan me yasa bai gaya maka ba" "Yabar parlor din ne......anyway koma meye zamu koma gidan.....saina qarasa" Ya fadi zuciyarta tana son lalubo dalilin kiran amma ya gaza.