Sashe 172
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A nutse ya shafa addu'a daga sallar asubar da suka idar shida fanna din tasa,koda bai kalli madubi ba yana iya jin yadda qwayar idanunsa suka tasa,wanda bana komai bane saina kukan farinciki daya dinga yi a daren jiya. Yaso yayi haquri ya kauda kai saboda walimar da za'a gudanar a yau,amma inaaaa.......ya gaza jurewar,har sai da yakai ga inda zuciya ruhi da gangar jiki suke muradi. Juyowa yayi gaba daya gareta,tana zaune a takure,kanta a qasa tana duban yatsun hannuwanta. Ita dinma fuskarta duk ta tasa,saboda kusan tare akayi kukan,tana yi yana tayata. Idanu ya lumshe ya budesu yana jin nishadi yana saukar masa. Kullum cikin zulumin yadda zai taddata yake,saboda ya sare da halayen 'yammatam yanzun duk da cewa yana da cikakken yarda da dabi'unta,to amma wani lokaci abun ba'a kama bane ko siffa. "Taho nan flower" Ya fada da sassanyan muryarsa yana miqa mata hannunshi. Bata wani musa ba ta miqa masa nata,don tana buqatar inda zata jingina taji dadin zaman. Jawota yayi zuwa jikinsa yana rungumeta tsam,yana jin wata shaquwa tana tsaga jikkunansu,yana jin kamar ta tabbata a rungume a jikinsa kaman haka. Qoqarin gaidashi takeyi,ya amsa mata yana shafa kanta ya amsa cikin kulawa. Sosai ya dinga jero mata addu'o'i,kanta a qasa tana amsa masa da matuqar alkunya. Mintuna kusan goma sha biyar suka debe a haka kafin ya gyara mata zamanta,ya ciro alqur'ani guda biyu ya bata daya ya dauki daya. "Ko na minti biyar ne flower,saboda mu bude wunin rayuwarmu na farko da neman albarka". Ya fadi yana miqa mata. Rainon anni ne wannan ta saba musu da farawa da qur'ani,kaman yadda yasan itama fannah din 'yar gado ce wajen iya sarrafa harshe a qur'ani. (Ina kira a gareku iyaye,kiyi qoqari a mazauninki na uwa ki wadata kwanya da harshen 'ya'yanki da qur'ani,su zama gwanaye wajen karanceshi daga bango zuwa bango,idan da hali suna karantawa suna fahimtar ma'anar,saboda hakan yana taimakawa wajen zaunar dashi a kansu yana kuma taimakawa wajen sake jin asalin gard'insa da dadinsa. Allah ya sani ina mamaki naga babban mutum babbar mace ko sangamemiyar buduwa musulma,amma ba zata iya karance miki qur'ani daga bango zuwa bango ba,ko ba zata iya biya miki wani adadi me yawa ba,don kwanyar da aka horata da qur'ani zaka sameta da kaifin basira da fikira me tarin yawa,Allah ya bamu ikon tarbiyyantar da yaranmu akan hakan,ya shirya mana zuria kafatanin musulmi Allahumma ameen). Suna kammalawa kira yana shigowa wayar tasa. Fannah ce ta miqo masa da hannu biyu ya karba yana murmushi "Allah yayi miki albarka" Saidai sunan daya gani mamaki ya kamashi,baiyi zatonma zaa kirashi da safe da wuri haka ba shi yasa ya bude wayar. "BB ba'a ga amna ba tun daren jiya......ga musaddiq nan ya rikice mana,kaman yanason rasa nutsuwarsa,ka sanar da hamma don Allah" Abinda saddiq ya fada kenan yana katse Kiran. Innalillahi yakeso yaja,amma kuma bayaso yayi abinda zai tashi hankalin fannah daga wayewar garinta a rana ta farko,ballantana yasan mata da rudewa qwarai,dan qanqanin abu sai su maidashi babba,don haka ya miqe tsam da wayar a.hannunsa yace. "Ina zuwa" Ya soma takawa yana fita a dakin. Tadan bishi da kallo kadan,sai kuma ta miqe tana ninke abun sallar da suka idar. Wani dakin daban ya bude ya shiga,sannan ya fara qoqarin kiran fu'ad yana kuma laluban kayan da zai sauya a jikinsa,idanunsa akan agogo yana duba qarfe nawa. Su dimma rufe alqur'aninsu kenan,don a yanzun shine malaminta. Tayi sauka tun kafin rasuwar mahaifinsu,tana da tilawa a kanta,amma sai yanayin karatunsa da qira'arsa suke mata dadi,wannan ya sanya ya zame mata malami duk bayan sallar asuba suke tilawar abinda ya sawwaqa tare. Wani lokaci ido take zuba masa idan yana karatun. Komai Allah ya bashi,duk wata baiwa da take nuna cikar dan adam ya sameta,abu guda daya ne ya masa cikas da naqasu shine MAHAIFIYA. Kashingidar da yayi da wannan damar ta samu ta zame jikinta zuwa kitchen. Wata irin mahaukaciyar yunwa take fama da ita a dan tsukinnan,ko cikin dare ta tashi abinci takeci,ba jimawa kuma take rasa komai,cikinta yake yayewa tasss kaman an mata yasa. A tsaitsaye ta hada oats ta madara tasha,kafin sannan saiga ma'u ta shigo. A mutunce suka gaisa,zuwa sannan ta fara gane inda sabreen tasa gaba na bawa mijinta kulawa da karan kanta. "Me zamu dafa?" "Ummm.....bari muga.....bari na fara dafa masa paw paw tea tukunna" Ta fadi tana nufar tsararren store dinsu. Duk kusan ganyayyakin da yakesha akwai a ciki,busassu anyi packaging nasa cikin wani leda ta musamman da ake kawowa daga china. Packet na Paw paw leave din ta dauko ta dawo,ta wankeshi da kyau ta tafasa ta juye masa cikin wani Traditional English tea set sannan tace da ma'u. "Ki fiddo naman kai bari naje na dawo". Ta shiga daidai sanda ya fito daga toilet yana goge ruwan alwala. Idanunsu suka gauraya waje daya,kowannensu ya sakarwa dan uwansa lallausan murmushi. "Barka da tashi sleepy head" Ta fada cikin salon tsokana. Fadada murmushinsa yayi har fararen jerarrun haqoransa suna fitowa. "Barka kade my super girl" Ya bata amsa yana karbar tea tray din yana ajiyewa saman drawer. Hannunsa ya miqa mata yana jawota cikin jikinsa,saidai kuma sulalewa tayi ta tsugunna tana gaidashi. Amsa mata yayi cikin murmushi kafin ya miqa hannu ya sake jawota ya rungumeta tsam,fitinannen qamshin kabbasarta na incense by kabo daughter daya hautsina har cikin gashinta da kuma lab lab dinta suna tashi da wani sassanyan qamshi daya manne a fatarta. "Fatan shalelena ta tashi lafiya.....addarmu.......matar babban yaaya" Yadda ya fadi maganan ya sanyata tuntsirewa da dariya,ya sake kamota yana qanqameta a jikinsa. "Ina yara na?,fatan sun tashi lafiya?" Ya furta yana qoqarin dage rigar baccin jikinta. Da sauri ta damqe hannunsa tana duban tsakiyar idonsa,sai ya dage mata dukka girarsa yana tambayarta why?,da wannan kallon nasa. "Ba bra a jikina". " Good" Ya fada da hanzari yana daukanta cak ya azata saman drawer din,sannan yasa hannunsa ya dage rigar har zuwa inda yakeso. Da cikin nata ya fara wanda ya fara turo kansa,ya aza dukkanin hannuwansa akai. "Good morning my Angel's" Dubansa tayi. "What?" Yatsansa ya dora saman lips dinsa "Shshshsh" Ya fadi sannan ya maida hankalinsa kan cikin. "Eheeennnnn......hope you're doing well......am eager to meet you my life.......have a nice and great day" Sai ya sunkuya yayi kissing na cikin. Sama ya komar da fuskarsa tsakanin ababen dake matuqar janye hankalinsa,qanqameshi tayi sanda yake cusa kansa a tsakiyar su,sannan ya sakar mata wani kiss din me sanyi kafin ya janye fuskarsa da idanunsa suka fara canza launi. "Mun gama gaisawa.....me kike cewa?. Fuska ta bata. "Son kai hamma.....son kai" "Name?" Ya tambaya yana ware hannayensa. "Angels hamma?......ni nafison baby boys.....masu kama da kai.....masu quality dinka". Ta fada tana tura baki gaba. Kyau sosai lips dinta sukayi masa,yasa hannu yana taba lips din murmushi na qwace masa,ya motsa bakinsa cikin nutsuwa. "Nafison baby girls masu tausayi irin naki......masu tsananin zumunci irin na ummansu......masu qaunar 'yan uwansu.....kinsan ma haihuwar diya mace falala gareta me girma fiye dana d'a namiji?" Kai ta girgiza "Na sani,idan aka haifi uku aka musu tarbiyya aka aurar dasu zasu zama sanadin shigar mahaifansu aljanna,sannan haihuwar d'iya mace tamkar shigowar haske biyu ne cikin gida,saboda zata jawo wani namijin shima ya zama naku". Tafi sosai ya sakar mata yana murmushi "Bravo alaiki...." Ya furta yana kissing tafin hannunsa ya aike mata dashi. "Duk da wannan?,duk da wannan my world kikeson boys?" Kai ta gyada. "Na rigaka addu'a fa hamma......inaji a jikina Allah ya amsamin.......ina buqatar photocopies din muffin dina" Ta fada tana tsiyaya masa ruwan gwadar ta miqa masa. Karba yayi yana dubansa,sai daya qare masa kallo sannan ya kalleta da lallausan murmushi "Ya akayi kikasan ina sonsa?". Dukka girarta ta dage masa tana nade hannayenta a qirji,hakan ya qara mata kyau sosai. "Kana tunanin idan nace inasonka ina sonka ne da wasa?......duk wanda nace ina sonsa......ina sonsa da gaske.....ballantana kai...." Ta qarasa fadi tana nunashi da yatsa daidai sanda kira ya shigo masa. "Farouq?" Ya fada a mamakance,farouq dinne da kira haka da sassafe?,cikin jikinsa yaji tabbas akwai wani abu daya faru,ya miqa hannu yana daga kiran *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ 144 *_NACE BA......._* *_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._* *_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_* *_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada munga ingancinsa_* *_Da yardar Allah saikin godemin_* *_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR GASKIYA KENAN AHTO_* Golden oud Hawi Sandal balls Sandal flakes Cotton bakhoor Kabbasine mix Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk) Deep crush (luxury khumra). Signature oil Kuleccham Kabbasine spray *_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_* *_PRIME SCENTS(the scents of royalty_* *KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN HANKALI* *SUNA NAN A* *_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road kano_* *BA'A KANO KIKE BA?* *_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a duk inda kike cikin aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_* *DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE* wa.me/+2348103155915 KO KI KIRATA TA NAN 08103155915 Shuru kawai yayi yana sauraren farouq har ya gama gaya masa abinda zai fada din. Satar kallonta yayi sanda take qoqarin zuba masa wani tea din. "Ka kula please dude.....banaso adda taji maganar nan ko don lafiyarta.....itama fanna din ban gaya mata ba,zan wuce gidan yanzu" "In sha Allah" Ya fada yana sauke wayar daga kunnensa. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Shine abinda yaketa maimaitawa can qasan zuciyarsa kafin ya samu ya miqe tsaye yana duban ta. "Adamamin tea din nan,abba ne ya kirani yanzunnan wai ya kusa sauka yanason nazo". Har ga Allah bata kawo komai ba,kawai mamakinta shine abban ke nemansu da safe haka?,kuma shida farouq?. Ba huruminta bane zafafawa kan sanin meye asalin ainihin kiran ba,don haka ta taimaka masa ya sauya kayansa ya fice zuwa ma'ajiyar motocinsa,inda ya taso jordan suka fice tare. "La haula wala quwwata illa billah" Shine abinda yake maimaitawa kawai akan hanya yana murza goshinsa. Wani irin tashin hankali ne yaji yana lullubeshi,duk irin tsaron da ya saka.....duk yadda yake kaffa kaffa amma daga gefe akwai wanda yake fakonsu?. "Su waye?.....su waye?" Ya furta a dan zafafe yana jinjina hannunsa yana duban titi,yana jin kamar ya tariyo daren jiya komai ya wakana a idonsa. "Waye ya rage?,waye yayi saura?" Ya