← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 215

Sashe 53

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hajiya amna ce tace nazo na duba kota dawo......" "......ta dawo.....amma batajin dadi,kice ta qaraso" Da sauri ma'u ta amsa ta juya tana ficewa a gaggauce. Kaman yana jira ne ma'u din ta fita ya saka hannunsa ya tureta daga jikinsa. Banda yana kusa da bangon daya bata kariya ba abinda zai hanata zubewa qasa. Da wani fusataccen kallo yake dubanta. "Kada ki dauka na yarda ne da abinda kika gayamin......muddin na bincika na samu wani abu na daban saina miki mafi munin hukuncin da baki taba tunani ba......hakanan duk ranar da kika qara gangancin fita koda qofar gidan nan ne ba tare da izinina ba......saikinyi dana sanin sani na........nan din gida ne da aka gina da tsaftatacciyar dukiya ta halas.....ba bariki bane ba ba kuma hotel ko gidan karuwai ba" Daga haka ya juya yana daukan file dinsa dake ajiye saman daya daga cikin kujerun falon yana ficewa da sassarfa. Wani irin kuka ne yakeson qwace mata amma tana hana kanta,don idan har kunnuwanta sun jiye mata daidai amna na gidan,kuma zata iya iskota koda wanne lokaci,dole ta tattaro dukka wani bacin rai tana hadiyeshi,saidai kuma abinda takeji yafi qarfin abinda zuciyarta zata iya dauka,sai bacin ranta ya zabi fita ta hanyar fitar hawaye daga idanunta zuwa saman fuskarta,ta lallaba tana neman kujera daya ta zauna a kai tana dafe da kanta. "Oh god........ damn it....." Abinda ya dinga maimaitawa kenan cikin mota yana saka yatsunsa cikin sumar kansa. Ya manta yaushe ne lokaci na qarshe daya fusata irin haka.....yaushe rabon da yaji zallar bacin rai irin wannan dake ratsa kowanne sassa na jikinsa. Ya alaqanta hakan da tozarta igiyar aure da yake shirin faruwa. Sai ya samu kansa da blaming kansa,me yasa zai daga hankalinsa har haka?,ai duk wanda ya siya rariya yasan zata zubda ruwa. Ransa yaji yana qara baci,sai ya yiwa driver magana ya qara speed na motor din. _An karbo daga abu hurairah Allah ya qara yarda dashi yace,manzon Allah S A W yace,idan miji ya kira matarsa zuwa shimfida taqi zuwa,mala'iku zasuyita la'antarta har gari ya waye_ *_qarqashin wannan hadisin akwai qarin haske,idan a wannan qin da tayi kuma ta samu ciki koda ta rasu wajen haihuwa wasu malamai suna ganin bata samu wannan shahadar da mace me naquda ke samu ba idan ta rasu_* *MAAMAH* Tunda ta cewa zuwaira taje ta duba mata su taci gaba da kiran wayarta ba qaqqautawa don ta matsu taji feedback,saidai kuma shuru ba'a picking wayar. Saita koma kiran wayar laila ita dinma duka sammakal. Kamar ta dora hannuwanta akai tayita rusa ihu haka taji,ta tsinewa zuwaira da laila a ranta batasan adadi ba "Dukkaninku baku da amfani" Ta fada da fushi,sai taji kamar ba zata iya zama ba....wannan karon zata tafi gidan fuad da kanta ne ta dubo meke faruwa ba tare da damuwa da komai ba. Tana taka qafarta kiran zuwaira ya shigo,tayi qoqarin hadiye fushinta tana fatar samun feedback me dadi,saidai amsar da zuwaira ta bata ya kusa sanyata zubewa qasa warwas "Bata gidan ita kanta.....kuma akan idanuna ta dawo ita kadai". Iya haka kadai ya bawa maamah amsar abinda taketa zulumin ya faru. Ta kwashesu,ta tseratar dasu,amma dai bata sare ba,tana da sauran hope,don haka kai tsaye ta fara kiran number huda. Kiran duniya computer ta gaya mata ta kuma jaddada mata wannan layin a kashe yake. Ta laluba wayarta kaf ta rasa number wayar bokanta tana me mancewa da cewa mutumin baya riqe waya,yo mutumin dake rayuwar tsakiyar dajin Allah ina gaya service ma bare waya ta dameshi?,mutumin da yake kewaye da aljanu,suke kai masa saqo kuma ku amso masa ko daga ina ne?,me zaiyi da waya?. Hajja harira ce ta fado mata,ba bata lokaci ta danna number dinta tahau kira. *Hajja harira* Tun fitar laila bata iya tashi daga wajen ba,idan tace ta qulla tunani sama da dubu da kwancesu tsaf a wajen ba zatayi musu ba. Duk wani tunaninta idan yaje ya dawo a waje daya yake cakewa,tun tana neman qaryata abinda take zargi har zuciyarta ta gama yin ittifaqin amsar dai itace "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Ta furta da wani matsanancin tashin hankali. Tayi imani muddin abinda take zargi ne ya tabbata.....to lallai laila zata qare rayuwarta kaf wajen bautar maamah...... Asiri ne da bashi da makari sai mutuwa.....yaci uban bita zaizai,yafi uban tace saidai kafin tace. Ita mariya zata yiwa haka?,wannan shine sakamakon alkhairin da ita tayi mata?. Kamar tasan itace a gaban tunaninta saiga kiranta ya shigo. Kamar kada ta daga amma kuma wani tunani daya darsu a ranta ya sanyata gyaran murya ta daidaita muryarta sannan ta daga din. "Al'amura kamar suna shirin kwabewa hajja.....ina tsoron kada zancan mutumin nan ya fara tabbata......ki taimakeni hajja". Maamah ta fada da tsananin damuwa,damuwar data saka hajja taji wani bangaren na tata damuwar da tashin hankalin suna samun sassauci.....ko banza ba ita kadai ke cikin damuwa ba......ba kuma ita kadai zata ci gaba da zama a cikinta ba,taci alwashin dukka yadda zatayi zata yi don maamah taci gaba da tabbata cikin damuwar ta,waye ya gaya mata yaro yana wasa da kan maciji koda kuwa ya rasa abun wasa?. Yanayinta ta daidaita don yayi dai dai da yadda maamah zataso taji,tana mamakin zallar rainin hankali irin nata. Bayan mummunar sakayyar da tayi mata,kuma wai ta nemeta da tata matsalar tamkar ma batasan me ya faru ba?. "Me yake faruwa?" "Garkuwata ta subucemin......daga yanzu zuwa kowanne lokaci zan iya fuskantar barazana daga wajen abun hari na,kowanne hope nawa kuma ya subuce hajja.....meye abunyi?" Ta qarasa maganar da sigar tambaya cike da damuwa. Iska hajja ta furzar tana dan bubbuga tafin qafarta kadan kadan,a nutse tace da ita. "Bani lokaci mariya nayi tunani......mintuna kadan nake buqata". Jikinta a sanyaye ta amsa mata suna katse wayar su dukka biyun. Wayarta take dan bugawa cikin tafin hannunta cikin salo na tunani. Mariya shegen kai ce,tana da nata matsanancin wayon da kai da kake rayuwa da ita kayi kadan ka fahimci komai idan ba ita taso ba.......saidai kuma a wannan yanayin da ake ciki mariya tana tafin hannunta ne. Bata isa tayi wani motsi cikakke ba ba tare da ita ba,itace ginshiqin.....itace kuma madogarar. To shin batasan abinda tayi mata bane?,batasan me ya faru ba?,ko tsananin iya bariki ce kawai?. "Inaso na samu tabbaci" Ta furta tana daukar wayarta data aje tun daxun ta sake lalubar number maamah din. Bugu daya tak ta daga,ta sanya wayar a kunnenta tana kiran sunan hajja. "Duk abinda zaka daukoshi ko ka matso dashi don biyan buqatarka......kuma ya gaza yin wannan aikin sai nakega bashi da wani amfani,kau dashi kawai zaifi.....me zai hana ta gusa daga rayuwar fuad tun kafin matsalolin da boka ya baki a dunqule su fara bayyana har sufi qarfin shawowarki?....ga laila nan?,umarni na da naki sune zasu zama abun binta,a azata a bigiren da wannan ke kai,nayi Imani da laila......tabbas ba zata sabawa tsarinmu ba......sirrinmu kuma a lullube". Nauyi maamah taji maganar tayi mata,sannan sam bataji maganar ta kama hankalinta ba. Har cikin jininta da zuciyarta takejin laila bata mata ba,kwata kwata bata dace da wannan aikin ba,bata dace ma ta zama matarsa ba koda na minti guda ne kuwa. Tasan wacce hajja farin sani,tana tunanin ita ko yaronta z asu kubuta daga ayyukanta ne?,sai ta girgiza kai a fili tana jin abun bai kama hankalinta ba. To amma dole sai tabi ta takatsantsan kafin ta fahimtar da hajja din,tafi kowa sanin hajjan akan laila bata dagawa kowa da komai qafa. "Aah fa hajja harira,laila ni dake duka 'yarmu ce......ba zamj jefata cikin wannan risk din da wahalar ba......qyale bare dai,wanda idan ya sabawa tsarinmu kowanne mataki zai iya fadawa kansa........kamar yadda itama wannan din MUMMUNAN SAKAMAKO na rantse miki da Allah zai yita bibiyarta......ba zan qyaleta ba,sai na banbance mata tsakanin aya da tsakuwa!" . Turqashi!.....hajja ta fada qasan ranta,kai tsaye a bayyana ko a kaikaice maamah bata qaunar laila ta kafa tarihin zama matar muhammad me jadda.....wannan shine amsar tambayarta kai tsaye idan aka cire kauce kauce. "Ke yanzun wanne shiri ne na gaba kike ganin ya kamata muyi?" Ta mata tambayar tana relaxing kanta don samun bakin zaren daga inda zata dasa nata aikin. "Ki bari tukunna na samu nutsuwa daga wannan,abubuwa su hau kan saiti,zaki ganewa idanuwanki ba tare da nace dake komai ba". Ta fadi mata kaman yadda ta saba. Tana da boye duk wani shiri nata,zai wahala tana kan shiri ka sani,ko a baya wannan ne ya zama SILA da sanadin da LAILA ta shiga DUNIYAR lissafinta,qila data tsaya neman fashin baqi wajen boka kamar yadda hajja taso suji......ba shakka da qila yanzun haka laila bata fada wannan BAQAR MASIFAR ba....dukka hajja ke wannan tunanin cikin ranta tana jin wani bacin rai yana taso mata. Hajjan ta bude baki zatace wani abu sautin kukan laila ya mamayi kunnuwanta daga cikin wayar. Wani abu ya daketa,tayi shuru tana sauraren tambayar da maamah keyi mata kafin kiran ya yanke. "Tashin hankali!" Ta fada a sarari tana miqewa tsaye,ji take kamar ta wuce kai tsaye gidan maamah amma wata zuciyar na jan kunnenta "Sai kinyi kamar baki sani ba......sai kinyi kamar baki fahimci komai ba,saikin maida komai ba komai ba". Wadannan maganganun suka sanyata rusuna ta koma ta zauna wuta naci gaba da balbala a zuciyarta. Daidai sannan nafessa ta shigo da mopper da broomstick tare da sallama a sanyaye cikin girmamawa. "Ubanme kika shigo kiyimin?". Kai ta sunkunyar "Kiyi haquri,haidar ne ya tashi da zazzabin haqori yau shi yasa ban shigo sharar da wuri ba". Duk da jikanta ne bata tsaya ta nuna kulawa ko alhinin komai ba,hasalima bata fahimci gaya mata take baida lafiya ba yaron,sai ta daka mata tsawa tana fadin " Sharar da bakiyita dazu ba sai yanzu ko?,baqar munafuka,fita ki bani waje". Tashi sosai hankalim nafeesa yayi,take idanunta suka tara ruwan hawaye,tana tsoron me zata gayawa d'anta a kanta idan ya dawo,tanason aurenta batason ta kashe mata shi,wannan ya sanya ta sulale tana tsugunnawa ta soma mata magiya tana bata haquri "Ki tashi bani waje kafin na rufeki da duka,sharar ce nace banaso ko ana dole?" A nan ta fahimci bawai iya rashin sharar bane kawai da ba'ayi ba ya sanyata haka,akwai wani abu na daban da ya bata mata rai,wannan ya bata sassauci sai ta miqe tana
Chapter 53 · 0% Book details