Sashe 186
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Kan hannun nasu idanunta suka fara sauka,wannan karon yunqurin miqewa tsaye tayi ta gwada tata jarumtar na UWA kuma wai MAHAIFIYA,saidai kuma kash......ba wani abu nata daya motsa balle akai ga batun tashin. Gumi sosai ya dinga karyo mata saboda abinda takeji a zucoyarta,bala'i da masifa ne fal idanu da zuciyarta,donme musaddiq din zai debo mata diyar alhaji hamzan yazo mata da ita?,auren da sukayi kadai bai ishesu ba?,har sai sun qara qunsa mata baqincikin ganin kasantuwarsu a tare?. "Akwai buqatar ki saka nutsuwa da kauda duk wani bacin rai daga zuciyarki don a samu a ceto lafiyarki yadda ya kamata" Likitan ya furta yana dubanta,gumin dake fita a fuskarta kadai ya gaya mishi akwai wani abu daya motsa zuciyarta,duk da baisan ainihin meye ba. Tana labe a bayansa suka qarasa gabanta,ya gaidata gami da yi mata sannu. Leqowa amna tayi daga bayansa tana mata sannu itama,suna hada idanu ta koma bayan mijinta ta lafe. Ko kusa ko alama bata qaunar ganin matar,anni ce ta kirata ba tare da sanin musaddiq din ba tayi yaqi da ita akan ta bishi idan zaije ta dubata. "Komai lalacewar tuwo ba'a sauya masa suna.....musaddiq baida wata uwa bayan mariya,koda ya nuna miki baya sonta wannan wani yanayi ne ya kawo haka.....batun abinda tayi miki kuma darajar addu'a bata samu galabar komai a kanki ba,sannan kuma hakan ya zame mata wani sanadi ne na tonuwar kowanne sirri....kina tunanin ke kika yiwa kanki haka?,ko kadan,darajar addu'a ce da duban zukata da Allah S W T yayi". Wannan maganar ita ta sanya amna yin qundumbala ta biyoshi. "Any progress?" Fu'ad ya tambaya yana duban likitan. Ajiyar zuciya kawai ya sauke sannan yace. "Idan zai yuwu muje muyi magana daga office ko?" Juyawa fu'ad yayi ya yiwa musaddiq inkiya,shi kuma ya waiwaya yana duban amna. Muryarsa can qasa cikin sigar lallashi ya fara magana. "Calm down dear......ga adda sabreen ku zauna tare da maamah......ba abinda zai sake faruwa,yanzun zamuje mu dawo.....okay?" Ya fadi yana dage mata dukka girarsa gami da riqe fuskarta tsakanin hannuwansa. Kai ta gyada masa,sai ya sake mata murmushi yaja da baya yana juyawa gami da bin bayan fu'ad. Saura kadan numfashinta ya qwace mata,wani tashin hankali ya sake sauko mata. "Shima musaddiq din haka yake?" Maamah ta tambayi kanta. Wani irin yanayi ne da batasan musaddiq dashi ba,soyayya muraran da mace a gabanta?.....wacce irin baqar rana ce wannan take gani?. Dukka yaranta guda biyu da iyasu ta mallaka a duniya,kowannensu ya dulmiya cikin soyayyar wata diya macen daban ba ita ba?,wani irin so me zurfin da bataga kwatankwacinsa a kanta ba a cikin idanunsu?. Shuru dakin ya dauka,sabreen tayi qarfin halin sakin murmushi ta kalli amna. "Ga guri ki zauna amarya.....kada angonki yazo ya tuhumeni na bar masa me a tsaye" Ta fadi tana ganin yadda amna din taqi sakewa. Ita kanta ta zama tamkar baquwa a gurinta. Murmushi ta maida mata,ta tako a nutse ta samu gefan sabreen din ta zauna tana qoqarin sakin fuskarta. Ashar maamah keda muradin narka musu ganin suna hira qasa qasa a gabanta amma bakin yaqi buduwa,game kula kuwa zaiga yadda idanunta suka kada sukayi jajur,daga amna har sabreen ba wanda ya kula a cikinsu,don sabreen din nata qoqarin jan amna da hirar da zata sakata sakin jiki. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 "Shekararta nawa tana fama da hawan jinin nan sir?" Likitan daya gaji da ganin abun mamaki tsakanin kwanaki ukun ya tambayi fu'ad. Kafadunshi duka biyun ya dage yana son gano dalilin tambayar. "Ba wasu shekaru bane,idan ya dade wata daya....." "Hamma duka baifi sati uku bafa" Musaddiq ya fadi yana duban fu'ad. Dauke dubansa fu'ad yayi ya maida ga likitan alamun "Kaji amsar tambayarka?". Kai ya jinjina cikin matsanancin mamaki. Tunda yake kaf a tarihin aikinsa bai taba ganin mutumin da jininsa yahau har haka kuma yake iya ci gaba da rayuwa ba. Matakin hawan jininta yakai mataki na qarshe,wanda daga wannan stage din saidai mutuwa bama stroke ba.....uwa uba kuma tun a kwanakin da aka kawota yake ta qoqarin ganin jinin ya sauka amma yana nan a inda yake,ba wani ci gaba. Ya gwada duk wata basira tashi da dabarun aiki amma abun ya cimma tura. "Sir......munyi mata dukkan abinda ya dace amma ba wani ci gaba ko nasara koda alamunta kuwa,abinda yafi bani mamaki shine......yadda hawan jinin yayi mata wata mummunar rafkiya karo daya,nayi zaton tsohon ciwo ne ma,sa'annan duk wani hanya na sauke jinin wallahi yaqi sauka,abinda yake dada bani tsoro shine,ci gaba da qin saukar nasa zai iya zame mata sanadin matsaloli kala daban daban,don a yanzun haka tsoro nake kaman qodarta tana son harbuwa,bansan me yake faruwa ba,nidai ban taba cin karo da case me kama da nata ba tsahon shekarun dana dauka a bakin aiki.......amma abinda nake tunani.......anya ba wani abu babba data sanya a ranta?,ko wani goal da takeso ta cimma a rayuwarta?,wani matsala dake bata mata rai?". Wani murmushin takaici ne ya qwacewa fu'ad,wanda tunda suka shigo office din yana tsaye kawai hannayensa zube a aljihun wandonsa. Likitan yayi tambaya a muhallinta,duk duniya shike da amsar wannan tambayar tasa,saidai abune da bai shafeshi ba,koda ya shafeshi ma labarin zai zame masa wani baqon labari da ko a duniyar hikayoyi bai taba jin irinsa ba. Uwa nason mallakar d'a kota mallaki abinda ya mallaka kota halin qaqa?,uwa nason tarwatsa rayuwar 'ya'yanta ta hanyar rabasu da abokan zamansu?......rabo na jikokinta dake manne a mahaifar surukarta kuma fatanta yabi rariya?,BURIN UWA TARWATSA RAYUWAR 'YA'YANTA ta rabasu da uwa da uban goyonsu da suka zamewa rayuwarsu suttura?,wacce irin uwa kenan wannan?,baya ga wasu boyayyun al'amura da fadinsu ma baida dadi koda a baki ballantana ga kunnuwa?. "Me take buqata?,me ya kamata ayi?" Ya yankewa likitan dogon tunani da zallar mamakin daya fada "Tana buqatar kulawa ta wurwuri......kulawa ta gaggawa saboda gudun rasa wasu bangarori na jikinta,kamar idanunta kunnuwanta ko qoda ko kuma hanta". "Yanzu me kake gani za'ayi?" Ya sake tambayar likitan,yana jin wani tsoron girman Allah yana kamashi. Amsa kuwwar muryarta yakeji a shekarun baya yanzu haka. "Shi hawan jini ai baka rabuwa dashi sai ya lalata maka ji gani qoda ko hanta.......kai kam gaskiya kaman bakayi sa'ar rayuwar duniya ba?,daga wannan sai wancan?" Tayi maganar tana tsaye a kan abban nasa sanda duniya tana tsaka dayi mata zaqi da gard'i. A lokacin shi kuma yana tsugunne a gabansa yana qoqarin ballo masa magungunansa saboda hakin daya sarqeshi ba qaqqautawa. "Ina ganin me zai hana ku fita da ita waje?,suna da kayan aikin damu bamu dasu,zasu sake bincikarta sosai ko akwai wani abun daban da yake jawo wannan matsalar bayan......." "Kayi magana da dukka asibitin daya dace ace an kaita din,ka tura adadin abinda za'a buqata daga dawainiyar asibitin da komai ka sanarmin ta waya" Ya fada kawai a gajarce. Yana ji a jikinsa komai daya kama na neman lafiyarta zaiyi mata shi,bayan ya tanqwara zuciyarsa wadda kowanne taqi tana tuna masa da yanayin nata action din akan mahaifinsa sanda yake jinyar ajali. Ya sani idan zai biya ta wannan ko paracetamol maamah bata cancanci tasha ba ta hannunsa.....to amma har yanzu huduba da tarbiyyar anni tana yawo a jininsa. "Uwa uwa ce fu'ad,duk lalacewarta ba wata madadinta" Wannan maganar ya jima da haddaceta daga bakin annin.