← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 215 OF 215

Sashe 215

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

daya ko dagata kaman yarinya qarama,saita fara wuntsila qafafunta tana magana cikin kuka. "Ka saukeni......bana buqatarka,kace ka daina sona fa.....kai kacemin na tafi.....na tafi kenan bazan dawo ba,kuma nima na daina son......." Ai bai iya bari ta qarasa ba ya manne bakinsa da nata,wanda cikin second kadan qafafunsa suka soma qoqarin kayar dasu saboda wasu irin taurari da suka soma kewaya jininsa. Sauketa yayi ya hadeta da bangon wani gini dake kusa dasu,ya sake lalubar bakinta ya shigar dashi gaba cikin nasa yana aike mata da wani irin zuzzurfan kiss. Hawaye kawai takeyi,ta kasa hanashi,ta kuma kasa tsaidashi,kaman yadda zafin maganganunsa suka kasa cirewa daga kanta. Sai daya galabaitar da ita gaba daya,ya kuma zare duk wani tasirin fushi da yake iya hanga sannan ya zare kansa daga gareta. Hannunta yaja ya zaunar saman wata concrete chair dake wajen shi da ita duka suna sauke numfashi kaman wadanda sukayi tsere. A madadin ya zauna,sai ya zame yana tsaiwa saman gwiwoyinsa. Hannunta ya kamo ya sanya tsakiyar nasa hannun. "Sabrrr" Ya kirata da wani irin taushi daya sanya taji wani sanyi ya sauka tun daga tsakiyar kanta har tafin qafarta. "Sabrrr" Ya sake kiranta wannan karon saita lumshe masa kyawawan idanunta kawai da suka sanyashi yaji kaman ya hadiyeta ya huta "Ki amsamin don Allah.......kice na'am hamma idan baso kike na zauce miki ba". " Hamma" Ta furta tana ware idanunta da suka wani zuge saman fuskarsa. Sosai yaji abun ya sokeshi,me ya shigeshi ne haka jiya?. "Please forgive me my world......forgive me.....am mad duniyata.......i hurt your feelings......ki yafemin......bazai sake faruwa ba,ke na batawa amma ni na karbi hukuncin,'ya'yanki da iyayenki da qannenki dukka sun zuba mini ido ja fiddo musu madame dinsu......in fact ni kaina zuciyata da kanta fushi take dani,don na haramta mata ganinki.....na haramta mata kasancewa dake". Yayi dukka maganar yana dora hannuwanta saitin zuciyarsa dake fama gudu. Hannunsa guda daya ya zame a nata,ya danganashi da saitin ka'aba sannan ya fara magana. "Ni muhammad fu'ad......daga rana irin ta yau nayi alqawarin bazai sake bari hawayen bacin raina ya zuba a idanun ameenatu na ba.....idan har kuma hakan.......". Da wani irin sauri ta zame daga inda take zaune tana riqe dukka hannayensa biyun tana girgiza masa da sauri. "Kada kayi haka......kowanne zaman aure dauke yake da qalubale.....komai dadi kuma wataran sai an bata ran juna......nima ina bata maka rai fa hamma......sau nawa ma......amma saika dinga yi kaman ma ban bata maka ba......kawai abu daya ne banaso ka sake fada don Allah". Ta fadi hawaye yana silmiyo mata,da alama maganan ita daya tayi mata ciwo fiye da sauran komai. Kafin ma yaji abinda zata ce din ya dora kanta saman qirjinsa yana lallashinta "Mene ne?,me na fada sabrrrr?". " Kada ka sake cewa zaka iya rayuwa babu ni......don wallahi ni bazan iya rayuwar da babu kai a cikinta ba". Wani abu me nauyi yaji ya sake sauka saman zuciyarsa game da ita,ya runtse idonsa sannan ya budesu. "Sabrrr" Ya sake kiranta a tausashe. "Na'amm hamma" "Adda na" Ya sake kiranta yana jin kaman ya maida agogo baya ya shafe abinda yayi mata. "Muffin" Ta motsa labbansa tana kiransa da sunan da yafison ji a bakinta sama da kowanne suna "Wallahi Allah mugun maqaryacine ni indai akan wannan ne......zan iya rayuwa babu ke?,ko na daina sonki?,babbar qarya ce wallahi wallahi da babu ta biyunta a duniya". Sam sam ta mance da mode dinta sai wata irin dariya data kwashe da ita. Yayi matuqar bata dariya yadda ya taqarqare yake siffanta kansa da siffar da tasan yafi tsana guda uku a rayuwarsa. QARYA YAUDARA DA HA'INCI. "Mijina ba maqaryaci bane......ban taba ganin mutum me gaskiya irinsa ba........a shekara goma sha shida ban taba tuna wata tana daya batamin rai ba koda sau daya kuwa.....don me bazan masa shaida ta cikakken adali ba?,tabbas dana zama cikakkiyar butulu kuwa idan na tuhumeshi akan wannan laifin qwaya daya". Dagata yayi cikin jin alfahari da ita,ya kalli fuskarta sosai ya sumbaci goshinta. "Allah yasa ke matatace har a aljannah". "Haka nake fata ka zama mijina har aljanna.......amma akwai albishi daya" Ta fada tana murmushi. "Wanne kenan?" Ya fada yana dubanta cikin zaquwa. "Allah karimi ne me karamcin da babu irinsa kaf a halittun duniya.......Allah me boye baiwarsa ne ga bayinsa duk yadda yaso yayi hakanne zai faru.......bayan na fito sanda gari ya waye jiri ya daukeni,daga haram suka kaini asibiti don na huta,sunyimin gwaji abun mamaki sun tarar da cikin da ake rigima a kansa a jikina......kasan watansa nawa hamma?" Ta qarasa fada a mugun sanyaye tana aza hannunsa saman cikinta. Kai ya girgiza yana jinsa kaman a duniyar mafarki. "Wata uku hamma amma dukanmu bamu sani ba.....dama haka yana faruwa?" Wani irin rauni ya kamashi,ya daga tafin hannunta ya sanya saman bakinta wai yana qoqarin controlling farincikinsa kada murna tasa ya furta abinda bai dace ya fada ba. Sai bayan wasu wasu sakanni ya iya magana da muryarsa me rawa. "Yana iya faruwa saboda haka Allah yaso ya kasance.......astgafirullah......Allah ka yafemin bisa gaggawa da shishshigin da na yiwa lamarinka......tashi na maidaki cikin ahalinki don basu da wata madadinki" Ya fada yana dagata zuwa jikinsa gaba daya. "Da alama su suka sanya sabrrrr dina me ma'anar sunan haquri ta zama mafadaciyar qarfi da yaji?" Kunya ta kamata,ta shige jikinsa sosai yana boye fuskarta,ga kunyar albishir din da takeson yi masa. "Hamma two embrayos........ina fata su zama dukka baby girls,abinda na zauna na yita roqa maka kenan......sunan waye da waye zaka saka?". " Sunan maamah.......da kuma nagartacciyar surukar data haifamin wannan DUNIYAR TAWA" Ya qarasa fada yana matse hancinta me kyau. Dariya ta saki har fararen haqoranta suna bayyana,tana wassafa kuma irin soyayyar da yarinyar me sunan umminta zata samu daga gareta. "Godiya ga Allah daya bani DUNIYATA na haqiqa......ya fiddani daga wancan DUNIYAR me cike da rudani" Tayi maganar ne a zuci batasan ta fito ba har sai da suka hada idanu ya kashe mata ido daya,kunya ta sakata cusa kanta cikin qirjinsa tana boye fuskarta gami da shaqo tattausan qamshin nan nasa daya mata wani irin dadi kaman bata taba jin qamshin ba sai ranar,da alama za'a fafata kenan,da alama kuma wannan cikin meson zuminci da babansa ne,don dama tanata mamakin yadda cikin watannin ta sake zama very addicted da lamarin. *_Tammat bi hamdillah_* *_Alhamdulillah alhamdulillah,Allahumma lakal hamdu fil ula wal Aakhira_* *_lallai a rayuwa komai yayi farko yana da qarshe,doguwar tafiya me cike da tarin qalubale masu dadi da sauqi dalilin SUPPORT NA MASOYA_* *_sau tari wata rayuwa na zame maka mabudin alkhairan da bakayi zato ba *_sau tari wasu dalilan ma zame maka falala me tarin yawa cikin hikimar gwani na gwanaye wajen iya tsara rayuwa da dukkan hukuncinsa da iyawarsa_* *_wata DOGUWAR TAFIYA da inajin bamu taba irinta ba ,wadda a zahiri bazai yuwi nayi shuru ban yaba muku ba ku kanku_* *_kunyi yawan da bansan wasu bama a cikinku......masoyan da suka dora dambar bibiyar SAFIYYA HUGUMA badon tafi kowa ba.....ba kuma don tafi kowa iyawa ba,sai don saboda soyayya da qauna data zama SILA_* *_INA MUKU FATAN ALKHAIRI DA DUKKA FURUCIN BAKINA......INA FATAN ALLAH YA SAKE SADAMU A TAFIYA ME DADI IRIN WANNAN CIKIN QOSHIN LAFIYA AMINCI QAUNAR JUNA DA SUPPORTING JUNA_* *_ALKHAIRIN ALLAH YAKAI MUKU A DUK INDA KUKE AREWABOOKS FOLLOWERS_* *_ALKHAIRIN ALLAH YAKAI MUKU 'YAN WHATSAPP.....INA FATAN ALLAH YA AMINTAR DA KOWANNENKU YA YALWATA ARZIQINSA DON ALFARMAR SHUGANA S A W_* *_NAJI DADIN WANNAN TAFIYA MATUQA,NA SAMU SUPPORT DA SHINE QASHIN BAYAN NASARATA A WANNAN TAFIYA DAGA GURIN MABANBANTAN MUTANE,UBANGIJIN AL'ARSHI YA DAFA MANA GABA DAYA_* *_AMANA/GASKIYA/ADALCI/DATTAKO/KAWAICI SUNE TUSHEN KOWACCE NASARA_* *Darasin DUNIYATA* *_KOWACCE RAYUWA AKWAI NATA KALAR QALUBALEN,BA KOWANNE MUTUM BANE ZAKA GANI CIKIN INUWAR DUKIYA KA DAUKA SHIKAM BAIDA MATSALA BA,BA KOWANNE MUTUM ZAKA HANGA KA DAUKA YA SAMU DUKKAN WATA WATA NI'IMA TA RAYUWA BA_* *_KAYI RAYUWA IYA MATSAYINKA......KADA KAYI MIQAR DA ZATA WUCE TSAHONKA,DUK GAGGAWARKA RABONKA SHINE NAKA,BA ZAKA TABA CIN RABON WANI BA_* *_BAWA BAI ISA YA YIWA KANSA ARZIQI BA,SAI ABINDA BUWAYI GAGARA MISALI YA HUKUNTA MAKA_* *_KE UWA!.....BAKI DA KAMAR 'YA'YANKI.....SUNE RAYUWARKI.....KIYI AURE AMMA KARKI YADDA KI FIFITA KOMAI NAKI SAMA DA TARBIYYARSU DA KUMA RAYUWARSU_* *_AIKATA ALKHAIRI KA WUCE ABINKA KA BARSHI AGUN,ZAI CIMMAKA WATAN WATARANA.....KAMAN YADDA IN KAYI SHARRI HAKA WATARAN ZAI DAWO MAKA_* _Kusakurai da aka samu a ciki da abinda bai kammalu ba ayimin haquri,na rubutu matuqa har naji rubutu ya ginsheni _wanda na batawa ya yafen,na yafi kowa,kuskuren ciki ubangiji yayi afuwa,ya tattaramu a ladan,ya bamu ikon daukan me kyau a labarin mu watsar da shirme_ Every conclusion sparks a new inception Nothing lasts forever Every dawn has a dusk Ending are part of beginnings in sha Allah _subhanakallahumma wabi hamdika ashahadu an la'ilaha illa anta,astagfiruka wa'a tubu ilaika_ _Allahumma salli wa sallim ana nabiyyurrahmati_ S A W 08187255862 %*&,&.& 2v3x3z3 5x6z6|6 9R:T:V: :P;R;T; %,&.& 2x3z3 5z6|6 9T:V: :R;T; Times New Roman Times New Roman Symbol Arial Arial Calibri Calibri SimSun Cambria Math Cambria Math !%),.:;>?]} $([{ SummaryInformation DocumentSummaryInformation WpsCustomData TECNO CC7 TECNO LD7 WPS Office 9caefecc7ebc49d9995277d8f95907c1
Chapter 215 · 0% Book details