Sashe 199
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwanansa uku a lagos,kwanan sabreen biyu a Abuja ya dawo kano. Har ya iso gidan baiyi wani tunanin abuja ta tafi ba,sai bayan ya shigo ne yadda gidan yayi masa shuru da yawa ya sakashi ya fara kokwanto. Tun a parlor na biyu ya soma da duba kitchen. Ba alamun dazu ko jiya anyi amfani dashi,kai tsaye kawai ya wuce bedroom dinta. Yadda yaga komai a killace ya bashi amsar cewa ba mutum a gidan,mamaki ya sanyashi zama gefan gadon nata,yana kallon inda aka shirya qananun gado saboda su fauzan idan a dakin zasu kwana. Sai lokacin yayi noticing wani abu,tunda ya tafi shi yake kiranta,idan ya kunna wayar yana tunanin zai samu saqonta ko miscal dinta sai ya tarar wayam,idan kuma ya tashi kiran nata sai ya kira sau nawa ana gaya masa isn't reachable,sai daga baya ya sameta. Jiyama kwata kwata basuyi waya ba,don ya shiga cikin qaguwar kammala aikin daya kaishi ya juyo gida. Ya manta rabon da yayi nesa da ita har haka.....bare su yaran da dama bai taba nesa dasu ba sai a wannan karon. Koda ya ciro wayarsa sai ya rasa waye zai kira?. Anni dai ya tabbatar bada cikakken saninta akan baisan nesa zasuyi ba akayi tafiyar ba........ita kuma sabreen ya kirata yace mata me?. Wani mummunan baci yaji ranshi ya soma yi,zuciyarsa ta soma tafasa sosai,sai kawai ya fara maimaita "A'uzubillahi minashshaidanir rajeem.....innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". A hankali a hankali yaji zuciyarsa tana yin sanyi,gefe guda kuma yana tunawa kansa maganganun malamai da yawa da kuma abbansa,hadisin manzan Allah S A W da yake gayawa maza su waye mata?.....karkatacciyar halitta da aka halicceta da qashi mafi karkacewa na haqarqari,da wannan ya danne zuciyarsa badon ranshi ya daina baci ba. Samansa ya haura yayi wanka,ya dawo ya shirya cikin shigar wani tattausan yadi ruwan sararin samaniya,kawai sai ya dauki key da wayarsa ya fice a gidan,duk da cewa yunwa yakeji. Da kansa yake driving,kanshi cunkushe da tunanin ina zata je?,ina zataje da har bai sani ba?,ya miqa hannunsa ya dauki wayarsa da daya hannun dayan kuma yana riqe da steering ya soma kiran anni. Bugu uku annin ta dauka,yana iya jin maganarta da su nadra,yaran da qiri qiri tace nata ne.....bama tun ya zu ba,tun a baya inda tasan dasu da tuni sun jima da zama a hannunta,dole kowa dake da kwadayin daukarsu ya haqura yabar mata su. "Barka da dare anni" Ya furta muryarsa ba wani karsashi yana rage gudun motar. "Barka kade me babban suna,abban abbobinsa" Ta fada da dan tsokana kadan a muryarta. Duk yadda yakejin muryarsa a jagule saida sabon sunan data sanya masa ya sakashi sakin murmushi. "Mun yini lafiya?" "Alhamdulillah.....ka dawo ne?". Sai daya hadiye wani abu sannan ya amsa mata. " Na dawo dazun,bai wuce awa daya ba". "To ma sha Allah,Allah ya bada abinda akaje nema da nasara me yawa" "Ameen ya hayyu ya qayyumu" Sai kuma ya danyi shuru. "Da wani abune?" Ta tambayeshi,kaman yadda ta saba da saurin gano damuwarsa tun baikai ga furtata ba. "Cewa nayi anni......wanne waje ne su fauxan suka je?" Banbarakwai anni taji maganar "Abuja mana.....ina cewa kun fara magana dama tun kafin ka tafi?". Kai ya girgiza a hankali,ya fahimci inda maganar yanzun ta dosa. Idan ya cewa anni baisani ba hakan bai dace ba,zai zamana kaman ya nunawa anni wani laifi nata da wala'alla zai saka annin jin wani iri a kanta,don haka sai kawai yace. "Ba komai anni......na dauka sun canza booking ne" "Aah abujanne dai,gidan uncle mubarak ko". "Ba matsala.......sai na shigo". "To Allah ya kawoka lafiya" Har zai yanke kiran ta rigashi. "Me kaci daka dawo?" Tayi tambayar ne don bata gamsu da yanayin muryarsa ba,kuma wani tunani ne yazo kanta a sannan. "Ba komai anni....amma zanci". " Ka qaraso ga favourite dinka anyi". "In sha Allah,godiya nake" Ya fadi yana yanke kiran. Cilla wayar yayi seat me zaman banza yana jin wani bacin rai yana taso masa. Duk wani dalili na kiranta yakejin babu shi yanzu a tattare dashi. Gudun na meye?,kaman wadda yake sarar naman jikinta?,ko soyayyar daya bata ne ta mata yawa takeson ta fara karya alqawarinsu,ta kuma fara wahal dashi kaman yadda sauran mata sukeyi a sanda suka samu soyayyar d'a namiji yadda sukeso?. Shikam yana jin bazai dauki irin wannan ba,ya tsare mata dukkan komai,itama ya kamata ta tsare masa. _hausawa sukace zo mu zauna zo mu saba,ran maza ya baci_ _wanne hukunci kuke ganin ya kamata jadda ya yiwa sabreen?_ Karya kan motar tasa yayi zuwa unguwar tasu,yana jin ya kamata ya duba maamah,duk da ko bayan ya tafi kullum sai ya kira yaji ya suka kwana,ya kuma suka tashi. Tun daga gate masu aikin gidan suke gaidashi,har zuwa sanda ya isa qofar parlor din. Takalmansa ya cire,sam bashi da wannan dabi'ar na shiga guri da takalmi,duk da girman daraja da matsayin da Allah ya bashi,ya sanya kansa a parlor din a nutse bakinsa dauke da sallama,duk kuwa da yadda zuciyarsa ke a matuqar b'ace. Muryarsa ta sanyata daga kanta da sauri daga karbar madarar da saratu take bata. Idanunta ta kafe a kansa kafin ta maida dubansa zuwa ga bayansa kaman me neman wani abu. Ita shima yake kallo,yana mamakin yadda taketa kallon bayansa din,kwanyarsa nason lalubo masa dalilin kallon. Bugun zuciyarta yadan qaru,sai taji zuciyarta tana dan washewa daga sanda yayi sallama a parlor din. Can qasan ranta ta samu kanta da fatan Allah yasa tare yake da yaran,Allah yasa tare suke,saidai duk walwalar da taji ta sauko mata sai taji tana komawa sanda ya qarasa shigowa falon,ta kuma fahimci shi kadai ne. "Kawo na qarasa bata" Fu'ad yace da saratu sanda ta gama gaidashi yaja kujera ya zauna daura da maamah din. Amsa masa tayi cikin girmamawa,ta miqa masa hade da dan qaramin towel sannan ta miqe tana basu guri. Duk sanda ya miqa madarar bakinta sai yaga ta kafeshi da wani irin kallo,ya kasa gane abinda yasa take binsa da kallon,saidai yasan cewa lallai akwai wani abun a qasa. Wani irin boundaries takeji tsakaninta dashi,zamansa kusa da ita yana shayar da ita madarar sai taji kamar ana sauyata ana kuma sauya jiki da zuciyarta. Fuskokin yaran guda uku take gani a tasa fuskar,tanaso tace masa ina suke?,tanaso tace masa ina ya barsu?,tanaso tace masa yaje ya dauko mata su amma kuma ba halin hakan,ba kuma bakin hakan a tare da ita. "Akwai wani abu da kike buqata?" Ya tambayeta ganin yadda kallon yaqi qarewa yana kallon hannuwanta. Kai ta girgiza masa a hankali,amma still bata daina kallonsa ba. "Zaki iya rubutu?" Ya tambayeta bayan ya gama kallon hannunta guda daya wanda tun wancan ranar yaci gaba da motsi. Kai ta daga masa a hankali tana jin zuciyarta tana tsinkewa. Kowa da yake tare da ita ya gaza gano mata hanyar fadin abinda yake bakinta amma gashi daga zuwansa har ya gano hakan. Tana ji yana kiran saratu,sannan ya sakata taje ta dauko memo da sticky notes a ajjiye mata koda yaushe a kusa da ita. Sanda ta kawo din sai ya ciri sticky notes din guda daya da a biro ya dora saman cinyarta "Write it down" Ya fada a nutse yana kallonta. Gabanta ne ya fadi,jikinta kuma dukka yayi sanyi tana jin wani yanayi daya haifar mata da fara rawa da jikinta yayi. Sauke biron tayi tana jin ba zata iya rubuta komai ba. Tana jin kunyar tambayarsa yaran duk kuwa da yadda take bala'in son ganinsu......ba abinda ya dawo mata a lokacin sai gamuwarsu ta qarshe,daya ajjiye mata abun rubutu kaman haka,yace kuma ta rubuta dukka adadin abinda takeso zai bata don ta rabu da rayuwarsu har abada,kenan hakan yana nufin inda ta rubuta din sun rabu?,inda ta rubuta din da yanzu ko dan tsako bata dashi wanda zai zauna haka a gabanta ya damu da damuwarta?. Ga dukiyar ga komai tana gani......amma kuma bata wani jin d'andanonta sam a tattare da ita. Lumshe idanunta kawai tayi tana maida bayanta jikin kujera ta jingina,yadan tsaya yana kallonta saiya kalli saratu. "Idan bacci takeji a maidata daki a gyara mata gun kwanciya.....ni zan wuce,sai da safe idan Allah ya kaimu" "To ranka ya dade....Allah ya tashemu lafiya". Kai tsaye gidan anni ya wuce,ya sameta da 'yan matanta guda biyun,nadra da haneefa. Abinci sukeci,kai tsaye nadra ta shirya masa nasa abincin sannan sukayi qoqarin tashi su basu waje shida anni. "Kuyi zamanku" Fu'ad ya fadi yana ganin fuskar haneefa kamar sabreen ce a wajen saboda kamannin da suke da ita. Sosai yayi qoqarin share damuwarsa ta hanyar sakewa yayi hira da anni,saidai suna tsaka da hirar kiran sabreen ya shigo wayar annin. Bai sake cewa komai ba yaci gaba da cin abincinsa,saidai kuma yana iya dauko sound dinta ta cikin wayar. Abinda ya sake quleshi yadda yaji tana hira hankalinta kwance,suka gama maganganun da zasuyi da anni su haneefa suka karba suma suka dora. "Lafiya dai ko Muhammadu?" Anni tace dame babban suna wanda har ya kammala cin abinda zai iya ci ya miqe. Murmushi ya qirqira. "Ba komai anni......" Bata gamsu ba sam sam,saidai daga kiran da sabreen tayi kawai taga fuskarsa ta sake canzawa,amma kuma bataso ta zama me yawan sanya kai akan mu'amalolin gidajensu. Koda matsala ce tafison su koyi kasheta da kansu da kansu,hakan zai koya musu jarumta da kuma dabarun xama da juna da kuma sake samun shaquewa sosai da juna. Ya yiwa anni sallama ya fito zuwa parking lot na gidan farouq ya shigo shida fannah. Fanna ta gaidashi ta wuce ciki,shi kuma farouq din yayi tsaye daga wajen motar fu'ad na daga ciki ya zuro qafafunsa waje. "Inata tunanin kiranka ai" Fu'ad ya fadi yana dan shafa sumarsa,don duk yadda yakeso yayi avoiding damuwar amma har yanzu yana jinta cikin kansa. "Lafiya kake dude?" Farouq ya tambayi fu'ad din. Kaman zaice wani abu sai kawai ya basar,yanason koma meye ya ganar da ita kurenta da kansa,basai wani ya ji ba. "Share kawai......hannu nakeso ka sakamin a nan" Ya qarashe maganar yana miqaqa farouq din. Karbar takardar yayi yana dubawa. Takardar mallakar wani tafkeken fili ne me fadin qafa da tsaho me yawan gaske. Daga kai tukunna farouq yayi ya kalleshi. "Wanne company ne haka zai sake lashe girman filin nan?" Murmushi fu'ad ya saki a gajiye. "Ba