Sashe 95
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
K'arfe takwas na dare agogon Maldives ya gama shiryawa cikin wasu lafiyayyun trouser da t.shirt. ta fidda sigarsa sosai da wani sassanyan kyau ke tsayawa a zuciyar dukkanin 'ya macen data Kalleshi. Wani irin mutum ne da zai wahala ka kalleshi ka kauda kai,koda baka furta komai a kanshi ba amma zai tsaye maka a zuciyarka da idanuwanka. Jikinsa yabi ya feshe da turarukansa,sannan ya sanya sau ciki a qafarsa,ya dauki wayarsa da maqulli ya nufi qofar fita daga dakin. Dukkaninsu suna dining area suna cin dinner. Kusan tunda suka iso garin tare suke cin abincin safe dana dare,na rana ne kowa da tsarin cin abincinsa bai yuwu suci lokaci guda. Ire iren wadannan abubuwan sune suke qarawa iyalan anni hadin kai qaunar juna shaquwa tare da fahimtar juna. A kanta idanunsa suka fara sauka,wani irin abu ya tsarga masa tun daga kwanyarsa har zuwa tafin qafarsa. Tun jiya bai sake sanyata a idanunsa ba,suna dakin annin ita da amna. Bazaice ga abinda sukeyi ba,amma lokaci lokaci yana jin muryar amnan da motsinsu,ita kanta amnan bata sake fitowa ba. Ita da amna suna seat din kusa da juna,kaman magana suke qasa qasa,baka iya ji saboda musaddiq da saddiq da suka cika gurin da musunsu da bai gane ma akan meye suke musun ba. Kaman wadda aka umarta,nata fararen idanun da a kwanakin yaga kaman sun qara girma ta daga ta watsa masa cikin rashin sanin shi dinne ya is wajen. Qwayoyin idanunsu suka gauraye da wani irin mabanbantan feeling. Da sauri ta janye qwayar idonta yayin da nata kallon a gareshi ya zame masa kamar wani irin dafi daya sabbabba mutuwar dukkan wasu gabbai a jikinsa. Tsigar jikinsa ta zuba sanda ta soma motsa wadannan siraran lips din nata tana tauna Chip's din dake gabanta. Bazai taba manta abinda yaji daga kowanne sashe na jikinsa ba a ranar farko daya soma tsotsar tausasan lips dinta ba......wani mahaukacin saqo da suka aike masa da baisan inda zai iya adana yawansu a kwanyarsa ba. Yanzun da take juyasu tana tauna sai ya zamana tamkar tsokanarsa takeyi haka yakeji tana aika saqo kowanne sassa na jikinsa. Fitowarsa ya sassauta tashin muryar saddiq da musaddiq din,kowa ya maida hankalinsa jikinsa,kasancewar sunsanshi mutum ne da baison ire iren musunnan nasa. Yakance "Shashanci ne wannan,kuna da abubuwan yi da yawa a gabanku cikin rayuwarku,shi ya kamata ku fuskata" Sau tari musaddiq yakanyi dariya idan bai wajen "Shifa hamma ya dauka kowa irinsa ne.....ba baki nayi mana ba,amma ba zamu iya achieving abinda yayi achieving ba.....we are doing the best,amma ba zamuyi kaman nasa ba". Kujerar dake opposite dintata ya zauna,sam table din baida fadi sosai,wannan yana iya sawa idan ka zura jiki da yawa gwiwarka ta iya taba ta abokin zamanka. Zamansa a wajen sai taji kaman gaba daya ya cika wajen.....kwarjininsa da qamshin sassanyan turarensa gaba daya ya gauraye wajen. Nauyin idanuwansa takeji har tsakiyar kanta,abinda bata taba ji ba a kansa tsahon tarayyarsu. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ _Allah S W T yana cewa "lallai sallah tana hana alfasha da munkari_ _Duk wanda salla bata hanashi qarya ba,zina sabawa iyaye,zuwan gidan boka shirka kenan,cutar da maqota da sauransu,to tabbas ya tuntubi sahihancin sallarsa_ "Barka da fitowa hamma" Amna ta fada wadda sun hadu yau kusan sau uku sun riga da sun gaisa already. "Lovey dovey.....barka da dare" Ya fada cikin wani irin aji kaman me qididdige adadin kalamansa na ranar. Murmurshi amna ta saki qasa qasa. "Hamma.....kada ka saka adda sabreen taji kishi fa.....sunan nan for now ya kamata ace nata ne". Daga shi har ita nauyi maganan ya musu musamman da anni ke a wajen,wadda tayi burus kaman bataji ba tana qarasa shan black tea dinta. Amnan ya kalla sannan a dabarance ya saci kallon sabreen din. Bayajin akwai wani suna daya cancanci ya kirata dashi......har yanzun duk sunan daya bata sai yaji tafi gaban wannan sunan. Daidai lokacin tana jefawa amna harara da fararen qwayar idanunta ne,wani irin kyau yaga ta sakeyi masa,tsigar jikinsa yaji ta zuba sosai har sai daya lumshe idonsa. "Ka maida hankalinka fa.....aiki zaka fita kayi" Wani sashe na zuciyarsa ya gaya masa ganin tana neman dagula dukkanin lissafinsa. "Yi serving hammanku takwarata" Anni data kammala shan tea din ta yiwa sabreen magana. Hakan ya masifar yi masa dadi,sai ya ajiye mug din daya dauko da farko yayi relaxing bayansa jikin kujera yana jin jikinsa yana sake mutuwa gaba daya....wani irin feeling yana taso masa yana sake kashe masa duk wani kuzari nasa. Sai data ji gabanta ya fadi da anni ta fadi haka,amma dole ta ajiye fork din hannunta ta miqe,fork din yabi da kallo,gaba daya ya gama karantarta,bata qaunar abinci ko kusa ko alama....bayajin zai iya bari taci gaba da hakan,dole ta dinga cin abinci me inganci tana qoshi,bayajin indai zata dinga zama ba abincin kirki zata iya dauke lalurarsa yadda yakeso. Shi kansa wani lokaci yana tsoron kansa,tun a lokacin da yake shi kadai ma.....shi da kansa yasan yana da buqatar mace me juriya kafin ya samu abinda yakeso. Faruwar abunnan kuma ya tabbatar masa sa zarginsa,bai taba kawowa ma zata iya dauke buqatarsa.....duk da abinda ya farun yasan akwai aikin gaggawa da kuma rashin sabo a tattare da ita,amma yasan cewa lallai akwai aiki a gabansa,dole sai ya horar da ita yadda zata dace da muradi da tsarinsa. Kwata kwata ya mance ya samu farouq a wajen,ya shagala wajen qare mata kallo ta qasan idanunsa. Zaka dauka sam ba ita yake kallo ba,amma kowanne motsi da zatayi idanunshi suna kanta sanda take zuba masa abincin. A cikin qaramin hijab take,amma shi ba hijab yake gani ba,wannan kyakkyawar surar tata yake gani,kyakkyawar surar da yakejin koda zata shekara a yana ganinta zallarta bazai gaji ba......kyakkyawar surar data kusa qwace kowanne tunani tasa,ta kusa sanyashi manta waye muhammad jadda gaba daya. Wani sashe na zuciyarsa dake danqare da mahaukacin kishinta ya soma masa zafi,gani yakeyi musaddiq saddiq da farouq dake zaune a wajen suma suna iya ganin abinda yake gani.....yana jin kamar duka suma qare mata kallo sukeyi. "Gyara kintsi yallabai.....anni fa na wajen nan kada a tafka abun kunya" Cikin kunnuwansa ya tsinci muryar farouq yana fada. Cikin dakiya ya gyara zamansa yana basarwa,abinda ya kusan sawa farouq ya fashe da dariya. "Shi yasa ake cewa bawa yaji tsoron Allahnsa koda yaushe" Farouq ya kuma fada sama sama. Tunu fuad ya gama karantar abinda yake fada,so amma yanzun baida energy din kulashi. Hannu yasa don karbar mug din da take miqo masa,cikin dabara ya hade da zara zara yatunta da suka ja hankalinsa sosai,ya kuma motsa hannun nasa yana lullube bayan hannunta da tafin hannunsa. "Thank you" Ya fada da wani irin sauti can qasan maqoshinsa yana karbar mug din. Kaman an yarfa mata ruwan sanyi haka taji sanda dumin tafin hannunsa yake ratsa kowacce jijiya ta jikinta,ta koma ta zauna tana jin cikin ta duka ya gama cushewa ta qoshi da chips din,sai ta koma juya cokalin kawai. Tana jin hirarrakinsu amma ita din ta gaza cewa komai,kaman yadda shima ta fahimci jifa jifa yake cewa wani abu. Kanta da idanunta cikin plate din,ta gagara daga idanunta saboda yadda takejin kowanne motsi nata ita yake kallo,ranta ya dinga baci kadan kadan,wannan wanne irin kallon wuce qa'ida ne?. Ta aje kallo a muhallin mazan bariki,wanda yawancinsu suna amfani da wannan hanyar idan sunso dilmiyar dake su afakaki komarsu.....wannan dalilin ya sanya da wurwuri take qarawa namijin da ya fiya kallon wuta. Amma wannan karon nasa kallon sai taji ya banbanta da nasu,don nashi kashe mata jiki yakeyi,ya kuma aza mata wani kwarjininsa sosai da har yake hanata sakewa. Tsoro sosai taji sanda taji ana lalubar tafin hannunta ta qasan kujerar. Ta fidda idanu waje tanason fahimtar waye,saidai ya bata haske ta hanyar cewa. "Miqo min tissue paper dincan please" Da wani narkakkiyar murya. Kallonsa tayi ya kashe mata ido daya,ta janye dubanta da sauri tana tura masa tissue din,ya dauka ya aje gefe yana ci gaba da cin abincinsa tabbacin ba amfani zaiyi da ita ba kenan. Tana ji tana kuma gani yaci gaba da murxa tafin hannun nata ta qasan table din,lallausan tafin hannunsa yana saukar mata da wata irin kasala da kuma tsoro,bai bata dama ba ballantana ta miqe ta nesanta kanta dashi,ba kuma zata iya nunawa kowa abinda yake faruwa ba. "Amman adda.....you look familiar,tun randa kuka iso Maldives naji kaman na taba ganin face dinki......kin taba zuwa asibitin SAMHG?" Musaddiq ya shigo da maganar cikin hirarsu. Duban musaddiq tayi tana qoqarin daidaita yanayinta kada wani ya fahimci akwai abinda ke faruwa under the table. "Eh......kaman sau daya ba......na taba kai wata....." Zancanta kuma sai ya katse,ta maida dubanta kan fuskar anni. Duk tsahon watannin da kwanakin sai yanzu fuskar ta dawo mata fes cikin kanta. Matar nan data fadi wajen sallah asma dinta taso tashi. "Exactly anni itace..." Ya fada yana sakin murmushi sosai gami da ture abincin gabansa. "Anni ya akayi kika samota?.....wannan data dinga mana masifa saboda mun barki ba kowa a wajenki.....wannan dinnan dataqi bayyana kanta bare ki gode mata,bayan ta dawo miki da jakanki ba'a dauki komai a ciki ba". Maganganun musaddiq suma sanyashi daga kai daga abincin da yakeci yana maidawa kan fuskarta gami da matse yatsunta softly cikin nasa,yanason yaji qarin bayani,yanason samun tabbacin da gaske ita ta taba cetar anninsu?. Anni da mamakin duniya ya isheta ta ware hannunta tana sakin qaramar dariyar farinciki "Ban sani ba musaddiq......hammanku zaka tambaya.....duk da shima nasan bai sani ba,tunda bai santa ba" Ta qarashe maganar tana kamo hannun sabreen ta riqe cikin nata "Yau kuwa zan miki godiyar da nayita so nayi miki ban samu dama ba.......sai gashi cikin hikimar ubangiji wadda ta ceci raina ta zama mata ga yaro na......dame zan saka miki sabreen?". Numfashi taja sosai kaman numfashinta zai qwace mata saboda yadda ta qasan table din fuad din ke mata wani irin salo tsakiyar tafukan hannayenta. Ta kasa fadin komai,sai muryar anni data sake ratsowa. "Komai zan miki ban saka miki ba takwara.....lallai kinyimin abinda bazan iya saka miki dashi ba.....wallet dina babu ko sisi da aka taba a ciki,kaman yadda wayata ta dawo lafiya lau.....ubangiji ya jiqan magabatanki ya kyautata makwancinsu.....na gode na gode sosai". Murmushin