Sashe 146
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba anni muddin babu shi a kusa dani.......zan fara lissafin yankewar numfashi daga gangar jikina daga yanzu zuwa fitarsa na qarshe" Ta qarasa maganar hawayen da take tarewa suka gangaro saman kuncinta. Wani abu ya ratsa anni da Alhaji hamza tun daga saman kansu zuwa tafin qarfinsu. Tsahon rayuwarsu zasu iya cewa basu taba ganin zazzafar soyayya irin wannan ba.....soyayya da qauna me wani irin zafi da radadi,soyayya da qauna ta gasken gaske......soyayya ta a mutu da kowanne motsi da yanayi na abokin soyayya ya tsayema dan uwansa a rai. Rasa bakin magana anni tayi,ta daga kanta tana duban Alhaji hamza da shima ya gama sallamawa. Kai kawai ya jinjinawa anni sannan ya dubi sabreen. "Indai don wannan ne ki kwanta kiyi baccinki sosai,daga gobe zuwa jibi in sha Allah zan siya mana tickets na fita taiwan......zakije ki ganshi....amma sai kinyimin alqawarin daga yanzu harmu tafi ba zaki sake damuwa ba......kuma zaki sakeyimin alqawarin idan munje ba zaki daga hankalinki ba.....ko a yaya kika sameshi zaki sawa zuciyarki nutsuwa da kwanciyar rai har ya samu lafiya kamar yadda muke kyautata zaton hakan". Kai ta shiga jijjigawa a jejjere. "Nayi maka alqawari abba.....nayi maka in sha Allah". Kai ya gyada shima,wani irin tausayinta yana kamashi,ya yiwa anni alama da hannu sannan ya juya yana fita. Saida anni ta tabbatar ta kwanta ta kuma nutsu,sannna ta saka mata karatun qur'ani qasa qasa kusa da ita,ta kira mata ma'u suka kwanta tare sannan ta fice. Tana jin fitar annin,saita runtse idonta tana jin wani rauni yana saukar mata,kuka takeso tayi wanda batasan iyakarsa ba,amma kuma sautin qur'anin da yake shiga kunnenta ya bata wata irin cikakkiyar nutsuwa,a hankali ta sake maida idanunta ta rufe,saita dinga jin kaman wani tabbaci take samu daga zuciyarta na samun nasara da sauqi a dukka al'amuranta,ta sake imani da wannan ayar da take cewa. (Ku saurara,da ambaton Allah kadai zukata suke samun nutsuwa). A dan gaggauce anni ta qarasa dakin Alhaji hamza,ta dubeshi,waya yakeyi yana daga tsaye a daren,batasan koda waye yake wayar ba duk da dare ya soma nisa,sai ta zauna tana jiransa ya kammala. Ba jimawa ya kammala din,ya dubeta yana aje wayar "Na saka su dubamin tickets ne xuwa taiwan.....na gobe ko na jibi,ina zaton kuma sai jibi ma za'a samu". "Amma abba.....kana ganin ya kamata mu dauketa mu kaita ta dinga ganinsa cikin engine da tashin hankali?kasan tabbas sai muhammadu yafi son rayuwar yaran nan da nashi rayuwar?,kasan sai yafi qaunar ta kula da kanta da lafiyarta akan tashi?." Dan murmushi ne ya subucewa abban,sai ya zauna gabanta yana dubanta. "Ameenatu.....zuciya da ruhin soyayyarsu ba gama gari bace irin ta kowa.....karatun da na yiwa soyayyarsu shine.....suna sake qaunar juna da tsananin son kasancewa da junansu a sanda jarrabawa ko musiba ta samu daya daga cikin su,sunfi qaunar duk tsanani su kusanci juna akan suyi nesa da juna......sabreena ba zata taba samun nutsuwa ba.....ba zamu taba samun yadda mukeson gani ba muddin bamu sadata da barin ruhinta ba.....xakisha mamaki idan kikaga tafi nutsuwa a can fiye da anan din duk da unconscious yake?" Ya qarasa maganar da tambaya yana duban idanun anni. Shuru annin tayi tana juya maganar abban. Ta jima bataga soyayya me zafi jini da hanta da zuciya harma da b'argo irin tasu ba. Kanta ta gyada a hankali bayan ta gama nazarin,ta kuma yarda da maganganun abban dari bisa dari don itama taga hakan. "Allah yayi mana jagora,ya taqaita dukkan wahala da sharrin masu sharri" "Allahumma ameen" Ya amsa mata yana miqewa. _TAIWAN_ _TAIPEI_ *_Taiwan Taoyouan international airport_* Yammaci ne sosai sanda suka sauka a taiwan,misalim qarfe hudu na yammaci,wanda yayi daidai da qarfe sha daya agogon nigeria. Da yake tafiya ce bata shiri ba,cikin motocin da gwamnati ke ajiyewa saboda baqi da wadanda ke buqatan hayar da zaiyi driving da kansa,ya gama adadin kwanakin ka maida inda ka karbo ita suka karba. Abdulgaffar ke driving din,yana yi yana duba map da address din da ya samu da zai sadashi kai tsaye da asibitin. Duk yadda garin yakai ga kyau tsaruwa da daukan hankali ba wannan bane a gabanta,bama kasafai take iya fahimtar inda suke wucewar wa,burinta kawai.shine su isa asibitin,burinta kadai shine ta ganta a gabanshi,burinta ta ganshi a gabanta ta daina jin cewa yayi mata wannan nisan da kowacce rana zuciyarta da gangar jikinta suke jiye mata. Tafiyar mintuna arba'in suka fada ainihin titin asibitin,ba wani wanda yake iya cewa da danuwansa komai. Saddiq musaddiq abba da anni......ballantana sabreen da take ganin kaman laqai laqai kawai abdulgaffar yakeyi bawai tuqi ba,kaman tafiyar kunkuru yakeyi,kamar ma bayason ya sadasu da asibitin. Mintina sha biyar map ya nuna musu suna daidai asibitin,suna shiga titin shine gini na farko daga hannun dama. Idonta ta daga a hankali tana kallon tsararre kuma ajiyayyen ginin asibitin,wanda ko ba'a gaya maka ba kasan cewa gurine me cike da tsari da tsananin kulawa,guri ne kuma da lafiya ke tsaye da qafafunta. Karo na farko data soma yarda da gaske ko a qasashen waje akwai rayuwar masu hannu da shuni akwai ta tsaka tsaki akwai ta talaka. Tun kafin sukai ga shiga asibitin checking nasu da akeyi kadai ya isa ya tabbatar maka akwai tsaro sosai cikin asibitin. Checking da ya sanya ta dinga jin kaman wani salo ne na hanata isa garesa.....kafin yafi tsaye mata a rai sama da zaman da sukayi cikin jirgin kafin isowarsu taiwan. A muhallin da aka tanada saboda ajiyar motoci abdulgaffar ya tsaida motar sannan ya kasheta. Ta daga idanunta tana jira taji wani a cikinsu ya bude motar da zummar fita amma bataga kowa ya motsa ba. A nutse Alhaji hamza kibiya ya fiddo wayarsa sannan yayi kira,kiran da duka duka bai wuce minti daya ba "Muns parking lot" Abinda ya fada kenan ya yanke kiran yana dubansu. "Muje ko.....ga Jordan nan zuwa". Kiran sunan Jordan kadai ya sanya jikinta ya fara rawa,a kasalance ta sanya qafafunta waje tana ambatar sunan Allah bayan musaddiq ya bude mata murfin motar,sai taji jikinta kamar yayi nauyi ta dafa murfin tana fitowa. Komawa gefenta anni tayi tana saka hannuwanta cikin nata,ta daga kai suka hada ido da anni. "Karki manta alqawarinmu,kada ki sabashi......be strong please ameenatu......na sani ke din jaruma ce" Kai ta gyadawa anni,bawai don a yau tana jin wannan jarumtar ba,ta dade da sani da kuma fahimtar indai akan fu'ad dinne bata da wani sauran jarumta daya rage,ita din raguwa ce ta qarshen qarshe. A hankali suka fara takawa suna dosar main entrance na asibitin,wanda basuyi taku goma cikakke ba saiga Jordan din,sukayi kacibus dashi a hallway din yana fitowa daga elevator. Kallo kawai sabreen take qarewa Jordan,abinda bata taba yi ba,saidai koda bata taba qare masa kallo ba amma ta sani yana da qiba da kuma tsaho gami da murdewar jiki,amma a yanzun abinda idanunta suke iya gane mata shine zubewar da yayi. Ya rame sosai duk da har yanzu wannan kuzarin yana tattare dashi,abinda ya sanya dukka gwiwoyinta yin bala'e'en sanyi tana jin tabbas ko meye ya faru da hammanta ba qaramin abu bane,abun har ya taba jordan har haka?. "Welcome madam" Ya fadi mata yana tsaye daga gefanta cikin tsananin girmamawa tausasawa da kuma kulawa. Bata iya amsa masa ba,sai idanunta data zare daga kansa gudun kada taje ta rasa ragowar qwarin gwiwar data rage mata. Musaddiq da abba da jordan su suka fara wucewa saman,kafin su kuma su kuma da saddiq su kira wani elevator din suka shiga suka bi bayansu. Farouq ne mutum na farko data fara hangowa yana fitowa daga wani balcony na daban bayan doguwar hanyar da kebantattun amenities suke. Faduwar gabanta ya sake tsananta saboda ganin irin zubewar da jordan yayi akan fuskar farouq. Ta kasa dauke idanunta a kanshi,kaman yadda ta lura shima din ita yake kallo. Suna takawa zuwa inda yake shima yana matsowa garesu,har suka riski juna a hanya. "Adda......haka kika koma?" Farouq ya fadi a raunane yana jin wani irin tausayinta yana ratsashi. Karo na farko da yaji yarda dari bisa dari yau yayi ido da ido da salon soyayyar da yakeji a ransa a baya cewa babu irinta a duniyar zahiri......saidai a duniyar litattafai da kuma fina finai. Kanta ta dauke tana qoqarin hadiye wani abu daya tsaya mata a wuya.....tambayarsa kulawa ce ta kawota.....amma da zaiyi mata wani abu da yafi wannan tambayar faranta mata rai. Ya sauketa da labarin halin da hamma fu'ad yake ciki.....ya gaya mata yanayinsa shi zaifi komai mata dadi. "Kaima bakaga yadda ka koma ba BB?" Ta qarashe tambayar tana kallon fuskarsa kai tsaye muryarta tana rawa,tana fatan ganin wani mode da zai bata haske akan yanayin da fu'ad din yake ciki. Wani busashen murmushi yayi yana kada kansa,sannan ya maida dubansa gasu anni. "Sannu da zuwa abba.....anni sannu da zuwa". "Muje farouq ciki....muje dakin" Anni data kasa haquri ta fada tana yin gaba sabreen kuwa ta sanya qafafunta ta rufa mata baya kai tsaye xuwa dakin da sukaga farouq din ya fito. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ 126 *_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_* *_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_* *_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_* *_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_* *_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_* *_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_* *_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_* *_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_* *_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_* *_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_* *_HAIHUWA KIKAYI?_* *_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_* *_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_* _Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_ 08104553105 08127084190 *_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_* *_BGAWO'S KITCHEN_* *MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU* 126 Daga balcony din ma'aikatan lafiyar wajen suka tsaidasu,kowanne aka bashi riga da hula ya sanya,sannan suka musanya takalman qafarsu zuwa wasu ajiyayyun tsaftatattun fararen Crocs da suke wajen. Lafiyayyen parlor ne wanda aka tsarashi cikin wani irin yanayi da zai bawa me jinya dama wanda ake jinyar yanayi me kyau,bisa wadatacciyar iska