Sashe 87
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bigire ko mataki da ake fargaba saka qafa saboda hatsarinsa....yana fafata da koma waye komai hatsarin dake tattare dashi......yau sai gashi labbansa na sama dana qasa suna haduwa ya gaza koda ambatar sunanta. "Me ka aikata haka fuad?,me ka aikata mata?" Ya fadawa kansa da kansa da qarfi yana sanya tafukan hannayensa dukka biyun yana kama kansa da kyau. Sauka yayi daga gadon da gaggawa yana nufan fridge din dake killace a daya daga cikin corner din parlor din ya bude. Sassanyan ruwa ya fiddo,ya dawo saman gadon yana tattarota cikin duvet din da shi kansa yayi bala'in staining sosai ya azata saman cinyarsa. A cikin tafin hannunsa ya zuba ruwan ya soma shafa mata daga fuska zuwa wuyanta. Sau uku kenan yana yin hakan.....amma ba wani motsi da tayi. "Oh my god!...." Ya fada yana wurgar da gorar ruwan ta fadi qasa ta fata tsiyaya. Fuskarsa ya kafa saman nata fuskan,ya riqe hancinta ya kuma bude bakinta ya soma bata iska ta ciki. Mintuna kadan yaji taja wani irin numfashi da ya tsarga mata har tsakiyar cikinta kafin ta fiddoshi,dagawar qirjinta ya alamta masa dawowar numfashinta,sai ya miqe yana duban fuskarta da tayi wani irin jawur idanunta da suke a rufe suka nuna dagawarsu. "Sabrrrrrr" Ya taqaita sunan nata saboda fitar hawaye daga rufaffun idanunta suka kuma gangaro ta gefan kunnenta. "I was wrong to do that......How can i make it right?" Ya fada yana jin hankalinsa na sake tashi. Bay qaunar kuka sam sam sam,musamman kuka na diya mace. Daya daga cikin abinda ya dinga daga masa hankali lokacin quruciya kukan musaddiq......kukan musaddiq a duk dare sanda maamah ta tafi ta barsu.....kukan abbansa sai ya zama abu mafi tsanani da azaba daya taba gani.....wadannan abubuwan suka sanya ya tsani kuka ainun.....duk da yana da tsananin dakiyar nuna bai dameshin ba. Hannunsa ya dora saman goshinta don cire mata gashin daya sake lullube mata goshin,yana jin kowacce kalma ya debo saita qwace daga bakinsa.......yanajin duk duniya ba wata kalma harshe yare ko lafazi da zaiyi daidai da kunnuwanta idan ya fadesu......shi a karan kansa yakejin kamar ba'a qirqiri wata kalma ta ban haquri da ta dace ko zata dace da girman laifinsa ba. Da sauri ya janye hannunsa yana jin yadda fatar jikinta ke fidda wani irin huci kaman yadda jikinsa ke fitarwa "Ya salam.......ya salam......am sorry,i hurt you sabrrr......Am sorry.....i hurt you,I'll do everything possible to make you feel better" Ya fada yana neman yadda zai gyara mata zamanta a jikinsa. Jinginarta a jikinsa jinta take kaman wani nau'in azaba na daban,batasan yadda wata rai zata fahimci yadda takeji ba.....tana jin kamar zata sake suma ne,don numfashinta sam baya kaiwa hunhunta yadda ya kamata. Tanaso ta gaya masa ya janye jikinsa daga nata amma ba wannan bakin,sai kawai kukanta ya qaru akan nada,abinda ya sake hargitsashi kenan. A zahirin gaskiya baisan yadda zaiyi mata ba don baisan yadda akeyi ba,hasalima shi bai taba zama yayi tunanin zuwan rana irin wanna ba a nan gaba a rayuwarsa bare ya nemi ilimin yadda akeyi ba. Jikinsa ya zame yana jin yadda zazzabi ke dafa qasusuwansa......amma tashin hankalin jinin da yake gani daga jikinsa ya dame wannan. Wayarsa ya dauka,sai ya samu kansa da rasa wanda zai kira.....wazai kira?,wa zai gayawa?,yace masa me?. "Farouq" Kawai shine sunan daya fado masa. Bai damu ba da yadda farouq din zai kalli abun.....abinda kawai ya dameshi yadda zai ceci ranta daga ta'addancin daya tabbatar yayi mata. Idan ya daga kai ya kalli inda jinin ke kwance sai yaji ya aikata baqin fasadi ne kawai yau a daren nan,qaramin kisan kai kawai yakeji ya aikata. "Hello......zamu kwana ne....wajen nan fa yayimin,ina tunanin dawowa nida fannah....." "Am at home" Kawai ya fada da wani irin sound da yaja hankalin farouq din. Aje yanayinsa yayi gefe da wasan dake cikin muryarsa ya bawa fuad hankalinsa "Is something wrong?" Ya fada da tsananin kulawa a muryarsa. Sai daya runtse idanunsa sannan ya budesu yana maidasu inda take kwance sannan yace "Yes farouq......a rude nake.....please help.....i don't know what to do" "You are not alone......am here to help,take your time and tell me what's happening?" Farouq ya sake fadi cikin yanayin kwantar da murya. "We had our first night farouq......i caused her serious injury" Ya fada da tsananin nauyin abinda yake fita daga bakin nasa,saidai kuma ya zama dole yayi hakan,don gani yake kaman tana dab da komawa sumanta. Wutace ta daukewa farouq din. Shima maganan ya masa dan nauyi kadan,duk da ya jima da sanin duk wadda zatayi irin wannan karon da fuad din abun bazai zama da sauqi ba. Don ya bashi relief sai yace. "Relax....ina zuwa". Yana sauke wayar daga kunnensa. Murmushi kadan ga qwace masa duk da qasan ransa tausayin adda sabreen ne fal. Yasan za'a fuskanci hakan daga fuad din,duk da tsananin wayewarsa da sanin lunguna da saqo na qasan duniya.....gogewarsa da mmu'amalarsa da kalar mutane daban daban jinsi daban daban......amma yau saboda tsananin kamewarsa da zame kansa daga dukkan wani batu ko sabga data shafi wannan fannin ya rasa yadda zai taimakawa matarsa. A ransa yaji tabbas ciwon ba qarami bane tunda yaji damuwa sosai a muryarsa. Ya jima yana kallon number wayar anni ta qasar yana kwatanta yadda zai kirata ya gaya mata. Wannan din wani training ne nata data musu. Ko.meye nasu idan ya samesu komai nauyi nsa bata yarda wani ya fara jibantar matsalarsu ba kafin ita bare a nan din baisan waye zai kira ba,dole ya koma ya shiga sms ya tura mata saqo kaman haka. _"Muhammad yana dakinsa......he needs your assistance"_ yana tura mata ya aje wayar,don bayason ta kira neman qarin bayani don wabillahi baisan ya zai mata shi ba. Tsaiwa cak yayi kuma wani abu yana dawo.masa da baya. "Ya akayi first night yazu musu da hakan if ba virgin bace?" Ya raya maganar a ransa,sai kuma yayi saurin kawar da ita don shi ya jima da qaryata duk wani hasashe na fuad tun ba yau ba. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ Sanda saqon ya iski anni dawowarta gidan kenan,tazo ta samu gidan ba kowa basu dawo ba. Daki ta wuce ta sauya kaya ta dauki wayar tana fitowa parlor da zummar kiransu taji me ya kaisu yin dare bayan tayi warning dinsu kan hakan kafin su tafi?. Jiya sam bataga sukuni ko walwala saman fuskar fuad ba,kuma tana ankare dashi,yadda ya kasa ya tsare a falon,bai koma daki ba sai bayan dawowarsu. Tasan yana da zurfin ciki sosai,ba kasafai ka fiya sani ko gane abinda yake damunsa ba,amma ita din uwace,koda wanne yare sukayi magana su dukkaninsu tana iya fahimtarsu. Shigowar saqon ya dakatar da ita daga qoqarin kiran nasu da takeyi "Wani sabon sakarcin ne kuma haka?" Ta fada tana zama saman kujera da gorar ruwan dake hannunta ganin me saqon farouq ne. Sau biyu tana maimaita saqon,tasan tunda ya fada da gaske fuad na cikin gidan,duk da bataji alamun akwai kowa ba a ciki,amma sai kuma saqon yaja hankalinta. Cikin fargabar kada wani mummunan abu ne ya faru dashi ta ajiye gorar ruwan tana maida hijab din jikinta,ta miqe idanunta kan qofar dakin,ta taka a hankali ta isa qofar. Knocking ta fara yi,knocking din farko ya sauka kunnuwan fuad dake tsugunne gaban gadon yana monitoring numfashinta,gani yakeyi ko yaya ya matsa zai iya sauke idanunsa a kanta ya tarar ba numfashi tattare da ita. "Waye?" Yayi namijin qoqarin tambaya "Anninku ce" Ta fada a nutse. Idonsa ya lumshe ya kuma bude duka lokaci daya yana furta "Rabbi yassir wala'ta'asir.....ya salam sallim" Yana jin kaf rayuwanshi idan ka debe rayuwar da maamah ta jefasu y taba shiga tashin hankali irin na yau ba. Baisan ta yaya zai bari anni ta shigo ta gansu a haka ba duk da zuwa yanzun ya saka Moroccan jallabiyya a jikinsa tun sanda ya kira farouq. Ita dince sam jikinta yaqi tabuwa masa,da yakai hannu kusa da ita sai maga ruwan hawayen dake idanunta yana qaruwa,ba bakin magana sam sam a tare da ita,amma duban data masa guda biyu tal ya karanto wani irin fushi da kyara a tattare da ita. "Ki taimaka please.....ki bari ko riga na saka miki" Wani fusataccem fushi ne ya sauko mata,ya saka mata riga bayan ya gama ketata ya kuma keta haddi da duk wani mutunci nata da take taqama dashi,ta kuma killaceshi tsahon lokaci?. Yadda ta maida idanunta ta kulle ba tare data ko motsa ba ya tabbatar masa bata buqatar ganinsa ne gaba daya,ga anni na tsaye a qofa dole bazai yiwu ya barta tanata jira ba,haka ya doshi qofar can qasan ransa yana fadin "Me yasa kayi haka farouq?" Yana qiyasta da wanne idanu zai daga ya kalli anni?. Fuskarsa kawai ta kalla da yadda ya bude qofar cikin rashin karsashi tasha jinin jikinta. "Kana lafiya?" Ta jefa masa tambayar tana tsareshi da ido. A yau dai ko karen hauka ne ya cijeshi baya jin zai iya kallon idanun anni bare ya mata bayani. Ratsewa yayi gefe da alamun bata hanya. Itama batace komai ba,ta maida dubanta ne daga cikin dakin tana hango iya abinda zata iya gani din wanda carpet ne da dressing mirror kawai take iya gani,sai ta maida dubanta kan fuskarsa da a yau yakejin idanun anni tako ina a kansa da wani irin nauyi. Batace komai ba itama ta ratseshi ta soma takawa cikin dakin,wanda taku biyu kacal tayi shi kuma ya fice yana laluben inda zaije ya aje kayan kunyanshi nesa da annin,saidai a taku na hudu idanunta suka sauka akan Sabreen,jinin dake jajur yayi staining jikin duvet da comforter din ya marabceta,cikin qasa da second uku ta fahimci me ya faru. "Subhanallah" Ta fadi tsigar jikinta yana tashi. Tasan ko meye ya faru a wajen artabu akasha ba kadan ba,ko tayi taurin kai yaje mata da dukka qarfinsa,qarfin da sam sam tsakanin nata da nashi baizo daya ba. "Muhammadu......maida qofar nan ka rufe" Annin ta fada da madaukakin sauti sanda yake dab da bakin qofar parlor din. Cak ya dakata da abinda yakeyi din,ya maida qofar ya kulle kaman yadda anni ta buqata,ya dawo kuma a hankali cikin parlor din yana laluben wajen zama. Gangar jiki duka da zuciya sai yakejin kaman ba tasa ba,zafin zazzabi yana