← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 171 OF 215

Sashe 171

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

ganinta ba,ina tunanin tana wajen anni". "Thanks......bari nayi wanka.....get ready zan kiraki ki rage....." Bai qarasa jinsu ba ya yanke kiran,kada suje suyi masa baranbarama a kunne. Still ya sake kiran saddiq. "Ina kunyar tambayar anni please saddiq tambayar min ita" "A nawa?" Ya sake zolayarsa "Ka fadi price dinka" Ya fada yana jin zaquwa. "Bari na kira maka din sai mu tsadance" Ya fada yana yanke kiran. Minti daya kacal saiga kiran saddiq din. "Anni tace suna tare da huda,gashi kuma huda tace tana wajen annin". Gaban musaddiq ne yayi wata irin mummunar faduwa,haka kawai yaji fargaba tana ratsashi. "Ya akayi haka?....amma,ina zuwa" Musaddiq ya fadi yana yanke kiran,sai ya zura flip flops dinsa yana fita a dakin. Kacibus sukayi da saddiq wanda ya fasa wankan shima ya zura tasa rigar. "Ko wani dakin ta shiga bacci ya dauketa" Saddiq din ya fada shima yana jin haka siddan tsoro yana kamashi. "Haka nake tunani" "Muje cikin gidan" Saddiq ya fada yana yin gaba musaddiq da yakejin kaman an sabule masa gwiwoyinsa ya bishi a baya. Harabar gidan ba kowa don kowa ya gaji ya wuce makwancinsa,baqi suna can shiyyarsu a bangaren baqi na gidan,a haka suka kutsa sassan anni. "Kira anni kice ta sauko" Saddiq yace da badawiyya me aikinta,ta amsa da to. Harta fara haurawa saddiq ya dakatar da ita yace ta dawo sai ya haura da kansa. Ya samu annin tana cire dankunnayenta da sarqa,saita juyo da mamakin ganinsa a irin wannan lokacin tana kallonsa. "Ya akayi saddiq?" "Amna fa bata wajen huda anni,kota gaya miki tana wani gurin?,dakunan wajen nan kuma mun duba kafin mu shigo,wayoyinta switched off". Yankewa gaban anni yayi ya fadi,hannuwanta data miqa kunne don cire dan kunnenta sai taji sun mata nauyi dole ta ajesu tana dubansa. "Kun gama duba gidan nan gaba daya?". Kai ya girgiza. "Kusan ko ina dai anni" Hannu kawai ta miqa ta dauki mayafinta ta yafa tana cewa. "Muje". Tare suka sauko dashi,ta dubi musaddiq. "Qarfe nawa ta kiraka kira na qarshe?". "Takwas da rabi anni mukayi waya,tace zataje gidan BB nace ta bari if possible zan dauketa na kaita taga gida mu dawo....idan bai samu ba tayi haquri,na saka wayar charge saida muka gama komai na koma daki na samu miscal dinta me yawa,na kira kuma wayar a kashe take". Wani abune ya tsargawa anni,a jikinta kawai taji wani baqon abu yana shirin faruwa,don amna bata taba irin wannan ba. Koda garden na gidan zata shiga saita gaya ma anni ballanta ace ta fita ko tayi nisa da gida irin haka. "Kiramin duk masu aikin gidannan" Anni ta buqata tana duban badawiyya. Da sassarfa ta juya,ba jimawa sai gasu kafataninsu,annin ta leqa daga qofar falon ta gaya musu,matan su bincike cikin gidan,mazan kuma wajen gidan dama kewayensa,saita koma cikin falon ta zauna kawai tana jin qafafuwanta suna dab da gagara daukarta. Kimanin mintuna biyar matan suka dawo,saidai kowacce abinda take gaya mata shine. "Bamu ganta ba" "Ba kowa a dakunan" "Bata nan". Shuru kawai annin tayi tana jan hasbunallahu wa ni'imal wakil tana dakon dawowar mazan. Jimawa kadan suka kammala nasu duban suma,har zuwa qofar gidan. Kasa tashi annin tayi,don haka tace musu su shigo parlor din kawai. " Mun duba duk inda ya dace ace mun duba din,tun daga cikin gidan nan har street din daga farkonsa har qarshe amma bamu sameta ba,bamu samu kuma komai nata ba" "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,hasbunallahu wa ni'imal wakil" Anni ta fada tana runtse idanunta,fargaba tana kamata. Gaba daya rasa abun yi tayi,hakanan kuma ta rasa abun fada kwata kwata,kwanyarta ta daure tamau kamar bata tunani me kyau ba tunda take. Fu'ad da farouq dukkaninsu suna gidajensu da matayensu,abba kuma baya nan,a yadda sukayi magana a safiyar gobe qarfe takwas zuwa tara jirginsu zai sauka. Kai ta girgiza,ba wanda zata bari ya sani a cikinsu,ba wanda zata dagawa hankali. "Anni ko su yaa fu'ad za'a kira?" Saddiq da tuni hankalinsa yayi qololuwar tashi ya fada. Kai ta girgiza tana miqewa. "Ban yarda ku gayawa kowa komai ba a darennan,don ba abinda hakan zai amfanar saidai ku daga musu hankali,bayan koda sunzo ba zasu yanke abun yanzu yanzu ba,sai wanda ya qaddara faruwar hakan ya qaddara warwarewar lamarin...." Ta fada cike da tauhidi da qarfafa imaninta,duk kuwa da cewa ita kadai tasan abinda takeji. "Kuje kuci gaba da kula da aikinku....kuma ku wuce zuwa safiya ko asuba muga abinda Allah zaiyi" Annin ta fada tana duban kowa. Kowa din ya juya ya fice,amma banda musaddiq dake qame a wajen,tamkar ma baisan abinda yake faruwa ba. "Musaddiq" Anni ta kirashi cikin dakiya. Kansa kawai ya daga ya kalli annin,don yasan baida sautin da zai iya amsa mata. "Kayi haquri kaje ka kwanta" "Kwanciya anni?" Ya tambayeta kaman baya fahimtar hausa. "Ta yaya zan iya kwanciya bansan halin da take ciki ba?,anni ina aka kaita?,waye ya dauketa?,me tayi musu?,me sukeso?,amna ce fa?.....kwata kwata shekararta nawa?,waye ta tsarewa wani abu?" A nutse anni ke karantarsa,ta fahimci kaman abun yanason fin qarfin kwanyarshi ne,don haka ta kira saddiq. "Ko baka kwanta ba kaje kayi addu'a musaddiq mu barwa wayewar gari" Tsam.ya miqe ba tare daya kalli koda saddiq dake jiransa ya tashi su tafi ba. "Ina zaka?" Saddiq ya zaburo yana tambayarsa gami da shan gabansa. "Zan fita nemanta ne,tunda kai baka damu da ita ba" Ya fada da alamun tashin hankali muraran akan fuskar sa. Kai saddiq ya girgiza "Akwai hadari a fitarka musaddiq,tunda ko su waye sukayi hakan bamu sansu ba,bamusan dalilin daya sanya suka aikata hakan ba,bamusan kuma meye manufarsu ko target dinsu ba". "Ko report sai naje na shigar,ba zasu dauke mana mutum.sukutum da guda mu kulle qofofinmu mu kama bacci ba kaman kaza suka dauka" Anni ta fahimci da gaske abun ya soma haurawa tunaninsa ne,don haka ta tako gabansa tana kiran sunansa. "Kanason jefa amna a hadari bayan wanda take ciki?" Kai ya girgiza da qarfi. "Yayi....to kada ka soma wani motsi ko aikata komai har sai munji daga bakin yayyenku.....qila fitar da zancan shine zai zama namu kuskuren.....kayita karanta ya hayyu ya qayyumu birahmatika astagis". Kafin ta dire ya kama,a hankali sai yaji hankalinsa yana daidaita,ya miqa hannu ya kama hannun saddiq da kanshi yana cewa "Muje". A parlor dinsu ya zaunar da saddiq shima ya zauna yana matsowa dab dashi,ya kalli saddiq din sosai muryarsa tana Rawa "Saddiq tsoro nakeji su waye?,tsoro nakeji karsu cutar da ita,saddiq munaji muna gani a hannunsu zata kwana?,wanne irin gurin kwanciya zasu bata?" Wanne kalan ruwa da abinci zasu bata?" Sosai saddiq ya riqe hannunsa yana fadin. "Kayita maimaita fadin ha hayyu ya qayyumu din kamar yadda anni tace......bamu zalunci kowa ba in sha Allah ba wanda Allah zai dorashi a kanmu". Sun jima yana riritar musaddiq kafin ya samo nutsuwarsa 'yar kadan,saidai ko cikakken zama ya kasa bare ayi maganan kwanciya,kai kawo.kawai yake tsakanin qofa window zuwa farfajiyar gidan,yana jin kamar ya zura da gudu ya tafi neman amanansa. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ 143 *_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_* *_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_* *_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_* *_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_* *_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_* *_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_* *_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_* *_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_* *_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_* *_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_* *_HAIHUWA KIKAYI?_* *_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_* *_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_* _Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_ 08104553105 08127084190 *_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_* *_BGAWO'S KITCHEN_* *MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU* 143
Chapter 171 · 0% Book details