← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 215

Sashe 75

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

data zame musu dole duk lokaci irin wannan. Dukka maganganun sabreen sukayi mata tsaye a rai,a daren ranar duk inda ta juya furucinta ne ke mata kai kawo a rai. Tanaso jin rauni game da yarinyar yana sauko mata,amma wannan dakakkiyar zuciyar da shedaninta dake gefe suna gaya mata _karamar halitta irin ta mace......yarinya qarama me qananun shekaru bai kamata taga rauninki ba.....bai kamata ace itace taci galaba samanki ba_. Abu daya ta kasa samun aminci akan yarinyar shine 'Yiwuwar aikata komai". Ko ba'a fada ba ta sani......sabreen zata iya aikata komai,tana da taurin zuciya da qwarin zuciya dama zarrar da zata iya yin komai.....wannan zarrar tata ita taja hankalinta ta zabota zuwa ga aikin da bata taba kawo komai zai warware da wata irin faduwa da rashin nasara haka ba. Tunda ta idar da sallar asuba bata koma bacci ba. Ta jira har sanda gari yasha,sannan tayi wanka,ta shirya kaman kullum da qasaitattar shigar nan tata dake qara mata jin izza da jin takai inda ya kamata ace takai din,saidai bata qarasa gabar da take da muradin qarasawa ba. Wayarta ta fitar ta kira driver dinta,ya tabbatar mata yanzu haka yana cikin mota yana jiranta,kai tsaye ta dauki jakarta tana yafa mayafinta ta fice. Dab da zata bar falon taji laila na kiranta "Maamah" Tsaiwa tayi tana jan tsaki,don bata shirya komai ya dakatar da ita ba. Qarasowa lailan tayi,ta kuma zube a gaban maamah din. Sam tun daga waccan ranar bata iya tsaiwa gaban maamah.....magana ce ko gaisuwa zubewa takeyi a gabanta tamkar bawa da uban gidansa. "Ina fatan ba wani abu nayi miki ba maamah?" Ta tambaya da tsananin tsoron kada ranta ya baci "Naga zaki fita baki tasoni ko kisa an gayamin ba" . Wani qaramin tsaki maamah din ta saki,wannan abun ya fara isarta,ba wani motsi da zatayi sai yarinyar ta buwayeta. Irin wannan abun da akan fu'ad ya fada tabbas zata iya cewa tafi kowanne mutum sa'ar zuwa duniya. Ko yaya taga fuskarta ta canza takanyi kaman zata fashe da kuka,komai kuma har abinda bai dace ta sani ba game da lailan lailan saita gaya mata "Unguwa zanje,kafin na dawo ki gyara falo din,ki hada da bedroom din,duk abinda kika gani ki ajiyeminshi inda kika ganshi,kada kibar kowa ya hauramin sama,akwai underwears dina dana cire ki wankesu ki shanya a backyard ki jira su bushe ki dawo min dasu ciki" "In sha Allah an gama,Allah ya dawo dake lafiya" "Amin" Ta amsa tana yin gaba. Sau tari idan taso bautar da laila sama da haka sai wata zuciyar ta gaya mata lailan kome tayi bisa jagorancin mahaifiyarta ne,wannan ya sanya take sassauta mata akan abubuwa da dama. Tafiyar awa daya da rabi cif suka fara gangarawa mummunan jejin,sai da suka sake kashe wata awar sannan suka isa. Daga nesa ta sanya driver din ya sauketa,sannan ta tattare zanin tsadaddar atamfar jikinta ta fara tsallake qayoyi da busassun tsirrai tana wucewa ciki. Gurine da zaiyi wahala kaje ka taras d wani duk da tarin al'ummar dake zuwa wajen a kulli yaumin neman duniya,tamkar sun manta da wata rana da zaa shimfidesu babu wannan ruhin daya zama masarrafi na motsinsu da kai kawonsu izuwa gurare daban daban. Ba wata kafa a jikinta da bata fitar da gumi sanda take zaune a gabansa tana jiran bayanansa na qarshe. Da qyar ta samu ya ganta.....don sharadinsa ne baya aiki biyu akan matsala guda daya. "ZANGON NASARAKI guda daya ya rage miki......BANKADA zata sameki.....tonon asirinki zai fara daga yanzu zuwa kowanne lokaci.....zangon nasararki zai iya narkewa ya dulmiya sanadin hakan!!!" Ya furta da wata irin murya maras dadin amo. Dukkanin 'ya'yan hanjinta taji sun tattara sun cure guri daya,idanunta suka qara girma saboda wani sabon kalar tashin hankali da bata taba jin makamancinsa ba "Kanaso kacemin itace zatayi nasara a kaina?!!!" "Me muka gaya miki wancan karon?!!!!......" Wasu muryoyi da tafi tsammanin sun kusa guda goma sukayi amsa kuwa a wajen kafin bokan ya karba "KINYI GANGANCIN ZABOTA......SAIDAI TAURARONSA DA NATA TAURARIN KADAI SUKA DACE......ITACE KADAI MAHADIN AIKINKI........zabi biyu gareki.....ko ki kasheta duk wani burinki ya dulmiya ya koma mafarki......ko ki barta ta rayu kina kallonta kuma naki burin shima yana raye amma babu wata dama ko hanyar cikashi.....zan miki wani aiki guda daya......amma daga kansa!....ina me gargadinki kada ki kuskura ki sake dawomin akan matsalar data shafesu.......aiki yayi kyau ko akasin haka......". "Na gode da wannan dama daka bani.....na tare dakai su dafa maka" Ta fada jikinta yana rawa da jin qarin dama guda daya,abinda a tarihinsa bai taba ba maimaicen aiki. "Zaayiwa na tare dani da ma'aikata yanka......zasusha jini wadatacce da zasuyi aikin jinkirtawar tonuwar asirinki........yayin da zangon nasararki ya kama......nan da kwanaki goma sha hudu zuwa ashirin da daya......kiyi duk abinda zakiyi wajen ganin muradinki ya cika......ke zaki yiwa kanki wannan aikin.....mun miki alfarmar samun jinkiri kadai.....amma ki sani tabbas RANAR HASARA DA RANAR TABEWA TANA NAN ZUWA.......DOLE KI FUSKANCETA DA DUKKANIN ZUNUBANKI.........KIYI NESA NESA DA MATSANTAWA TAURARINTA........BA NASARA TA KUSA KO TA NESA......NATA ZANGON NASARAR YANA DAB DA FADOWA HANNUNTA". Duka bayanansa bai wani dameta ba......zangon nasararta da damarta guda daya daya tabbatar mata ita tafi komai yi mata dadi. Kudade masu kaurin da suka haura million hudu ta zube masa,sannan ta fita da baya da takalmanta a hannu ranta fes,tana gayawa kanta dogon zangon tunani ya zame mata dole don samun kyakkyawar mafita. Tabbas ta kowacce fuska tana da buqatar barin sabreen gidan koda itace murfin nasararta.......gwara tasan yadda zatayi ta maye fareeda da ita a madadin cikar burinta. Hadith yana daya daga cikin karatuttukan da suke mata dadi qwarai. Sau tari idan suna karatunsa da rumaisa yafi kowanne littafi daukan musu lokaci. Ko a yanzun da take zaune tana bita amna na zaune a gefanta,sunata hira da anni wanda rabinta kusan na tafiyarsu ce jibi,lokaci lokaci kuma da tsare tsaren abinda zaa gudanar da bikin farouq. "Anni....gata karatu take,ki mata magana don Allah" Ta fada a narke. Duk da sabreen batasan akan me amna ke magana ba,amma sai data daga kanta da sauri. Tana balain jin kwarjinin matar da ganin kimarta,daidai nan amnan ta miqo mata wayar tana danne dariyarta hadi da hade hannun alamun am sorry. Da idanu ta nuna mata zan kamaki sannna ta karbi wayar tana sakawa a kunne "Barka da dare d'iyata.....ina fatan dai bata miki shirme?" "Barka da dare anni....." Ta fada tana murmushi "Ya jikin naki?...ina fata dai kinji sauqi?" "Alhmdlh na warware....anni na gode" "Ba godiya ai tsakanin uwa da d'iyarta......nace ba,nasan halin yarona sarai,duk sanda tafiya irin haka ta kama saidai a tayashi shirya kayanshi shi kansa,nace idan akwai wani abu da kuke buqata na tafiyar kiyi magana....karki daukeni suruka ameenatu ni mamarki ce,ki rubuta sai a kawo,idan kuma ta amnan zakiyi to saiku fita tare goben,saiki masa magana" Kunya ta sake kamata,bangare daya kuma tana jin wani iri. Ta aza an soke zancan tafiya da ita ne kwata kwata,don tun randa akayi maganar da amnan tace BB farouq yace ta bada details dinta da sauransu bata sakejin komai akai ba. "In sha Allah anni......Allah ya saka da alkhairi ya qara girma" "Ameen ameen,a baya magaji ne yake hada masa necessary abubuwan da zai tafiyar dasu.....ina fata yanzun zaki maye gurbin hakan?" "In sha Allah" Ta amsawa annin tana jin wani qaton nauyi ta aza mata akai,daga nan ta miqawa amna wayar ta maida kanta kan karatun. Amma kuma sai karatun ya gagareta,saboda batasan yadda zata cika maganar anni ba. Batason haduwa dashi kwata kwata,hakanan idan batayi yadda annin tace ba zai zama kaman rainuwa,kuma amna da akayi a gabanta ba zataji dadi ba. Dabara ce ta fado mata,ta rufe littafin tana duban amna data gama wayar. "Kina da number magaji din?" "Eh ina da" Amna ta amsa mata "Faka faka kiramin shi" Ta furta tana gyara daurin dankwalinta. Sosai abun ya yiwa amna dadi,ta kira magajin ta hadata dashi. "So nake nasan da meye da meye ake hadama boss idan zaiyi tafiya?". Tayi maganar tana miqawa amna hannu alamun ta bata takarda da abun rubutu. A ladabce ya dinga zayyano mata tana rubutawa,har ta gama tsaf tayi masa godiya ta yanke kiran,ta miqawa amna bironta ita kuma ta miqe da takardar a hannunta,amna ta bita da kallo tana murmushi. Tasan abinda take shirin yi,zataje ta hada masa jaka tana tunanin baya nan kafin ya dawo,saidai tun daxun taga shigowarsa,kawai bata gaya mata bane tunda ta lura ba hawa saman take ba,itadai adduarta daya Allah yasa adda sabreen din bata cikin sahun shashashun matan nan da basu iya baiwa miji kulawa,duk da itadai a hakanta a halittarta bataga alamun hakan ba. Duk da tana da yaqinin baya nan,amma duk taku daya sai bugun zuciyarta ya qaru,kaman yadda numfashinta ke fita da nauyi. Bude smart door dinsa bame wahala bane a wajenta,saboda tuntuni ya sanyata cikin sahun masu shiga kai tsaye. Ko ina fes kaman yadda ta saba,yana fita da safe take shiga,tasan lokacin fitarsa,zai kuma wahala ya wuce wannan time din be fita ba,zata shiga ta kintsa komai. Duk da baya barin komai sai dan goge goge da qananun datti,bai taba barin underwears dinsa ba koda kuwa singlet nashi bata taba gani ba,abinda ma ya sanya mata qaramar nutsuwa kenan. Bedroom dinsa ta wuce,tayi kuma amfani da details din da magaji ya bata ta dinga fiddo da komai,sai data hada shi tsaf sannan ta rufe briefcase da luggage din ta ajiyesu a gurbin da ta tabbatar zai wahala ya kasa ganinsa. Yadda batayi zaton ganinsa ba haka shima baiyi wannan zaton ba. Batasan ya shigo saman ba kwata kwata. Ta zare idanunta daga cikin nasa idanun da yau take ganin kamar sun rusuna sunyi kuma laushi,can qasan ranta tana mamakin yadda ya balbalawa kansa A.c tayi qau a falon,abinda iya saninta dashi ba sabonshi bace. Idan kaga ya kunnata ma to tabbas ranan ana zafi,ko kuma bai samu irin fresh air din da yakeso ba. Kanta ta dauke sosai ta fara takawa zata wuceshi,yau daya sai taji tana jin shakkar giftashi,koda kuma bata kalleshi ba tana jin kaman idanunsa a kanta suke. Allah ne kadai ya sauko da ita,don bibbiyu bibbiyu take hada stairs din tana saukowa,tana jin kamar zai biyota yayi jan masifar daya saba,tana kawowa bakin bedroom dinta ta saki numfashi tana danne
Chapter 75 · 0% Book details