← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 215

Sashe 74

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da uku dake da aiki ranar a gidajen jaridu ukun......saidai mun rasa mutane uku a ciki,mutum daya daga gidan kowacce jarida......abinda ya qarfafa zarginmu akan suke da hannu.......na tura ma'aikata don binciken inda suke,kuma ina saka ran koda wanne lokaci zasu bani information,amma sauran mun tabbatar basu da masaniya akan komai" Wani abune daya tsaya masa tun jiya ya dinga sulalewa yana narke masa,ya gyada kai yana jin sassaucin dunqulallen abun daya tare masa wuya. Kafin yayi magana aka nemi izinin shigowa dakin. Ma'aikacin ya duba ya kuma bada izinin shigowa. Salute nasa sukayi mutum biyun da suka shigo,suka kuma miqa masa wani takardu. "Auwal sadi.....nura mahadi......labaran isyaku.....gaba dayansu mun samu tabbacin sun fita daga qasar nan kusan awanni biyu da suka shude,saidai kowannensu mun samu tabbacin qasar daya sauka.....auwal ya sauka a uk.......nura South Korea......shi kuma labaran ya sauka a china". "South korea.....UK.....china" Fu'ad ya furta sunayen a fili yana irgawa da yatsunsa,sai ya fesar da iska a bakinsa yana maida dubansa kan CP. "Well done sir......i really appreciate your effort,thank you for your hard work.......a sallamesu inason muyi magana privately" "Okay sir" Ya amsa masa cikin girmamawa. Cikin qasa da mintuna ya sallami kowa,ya kuma riski fu'ad din cikin motarsa qirar Mercedes sprinter. Duk yadda yaso mazewa da ganin alatun dake cikin motar tamkar kana cikin wani hamshaqin parlor din bawai mota ba amma ya gaza,sai daya daga kanshi ya kalli saman roofing din da yafi kama da lafiyayyen roofing din dakin sanda fu'ad ke qara hasken cikin motar daga galaxy blue stars zuwa brighter light. "Ina expecting tafiya nan da kwanaki uku......inason kayi gaba da kula da komai har zuwa sanda zan dawo......saidai banason binciken ya dakata......zanyi qoqarin ganin an kawosu daga dukka qasashen da suka tsallaka din don su fadi w anda ya basu contract din......wadancan mutum biyun kuma,ko tambayarsu bana fata kuyi.....ajiya na baku......irin ajiyar nan ta ma'anan ajiya" Yakai qarshen maganar yana tura cheque na kudi daya rubuta masa masu yawan gaske. Kai ya girgiza "Nop sir.....bazan amshi komai ba,aikina ne nakeyi kuma dole mutum irinka a masa aikin daya dace saboda alfanunsa ga al'umma". Wani abu dake gefansa ya dannan wata qaramar ma'ajiya ta fito,ya jefa cheque din yana cewa "Ba bribing naka nakeyi ba.......wannan din kyauta ne na baka,na jima da sanin wanene kai......inda baka cancanata ba ko qwandalata ba zata shiga hannunka ba.....kana daya daga cikin mutane masu aiki tuquru da qoqarin kamanta gaskiya duk da yadda qasarmu ta lalace.....so you deserve it,xan baka koda bakamin aikin komai ba" "Thank you sir.....thank you so much" S.nuhu ya fada yana jin dadin gwaggwabar kyautar da me jadda din ya bashi. Tunda wuri taqi zaman parlor din don batason ma ya dawo shi ya gansu ko ita ta ganshi,ta zame tayi zamanta a daki dole amna ma ta biyo ta can. Tana saman sofa din dake gefe daya a dakin,amna na zaune saman tattausan carpet din tana assignment. Idanunta kan takardun tana jin sha'awar amna din,tana jin inama ace itace ta samu dama irinta amna?,inama ace ta samu daman zuzzurfan karatu kaman amna?,wadda gata ya sanya tace bazatayi karatu wata qasar ba tsabar samun dama. Maida bangon littafin tayi tana duban sabreen cikin murmushi "Done......sai yanzu hankalina ya kwanta...lecturer dinnan mugu ne adda.....any mistake game over" Murmushi ta tayata dashi,ta jawo jakarta tana qoqarin maida litattafan "Adda......kin taba jin labarin labarin uwar data watsar da yaranta tun suna qananu ba tare data damu da waye zai kula dasu ba?,waye zai zama gatansu?" Takai qarshen maganar tana zuba idonta akan fuskar sabreen. Maganar sai tayi ma sabreen wani iri,a hankali ta girgiza kanta "Aah amna" "Kin taba jin labari,bayan wasu shekaru ta dawo garesu,amma kinsan me yasanya ta dawo garesu?" Kai sabreen ta sake girgizawa "Kudi......arziqi da rufin asirin da suka samu tazo ci,ba yadda suka rayu bane damuwarta......ba lafiyarsu ko akasinta ba". Idanu sabreen ta zubawa amna tana jin labarin ya kasa kama hankalinta,tsahon wasu mintina ba wanda yace da kowa komai,har sai da sabreen ta fara magana "Wanne irin cukurkudadden labari ne wannan amna?,a ina kika jiyoshi." Qaramar dariya amna ta saki tana janye jakarta gefe "Labarin mijinki kenan.....hamma na....." Bata qarasa ba shigowar saqo wayarta ya katse sauran maganar dake bakinta. Wani irin shuru sabreen tayi lokacin da hankalin amna yayi kan wayarta "Maamah?,mariya?....." Abinda kawai sabreen ke iya juyawa cikin ranta kenan "Bai rayu da ita ba?......batasan komai nasu ba?......batasan wahalarsu ba?,dukiyarsu tasa ta dawo??,dukiya???" Tarin tambayoyin da suka jujjuyawa cikin kwanyarta kenan. Maganganun amna gaba daya sai suka kasance mata kamar ta jefeta da wata cukurkudaddiyar sarqa,ta kasa hada daya da daya ya bata biyu. "Unbleavable!......oh my god!" Amna ta furta da wani irin qaraji,abinda ya yanke zaren tunanin sabreen kenan,ko kafin ta farga har amna ta fado jikinta ta cukuikuyeta "From nigeria to Maldives........wedding bells adda.......wedding bells" Ta fada tana dariyar dake cakude da farinciki zalla a muryarta. Qoqarin dagata sabreen takeyi cikin murmushi da mamakin abinda ya sanyata tsananin farinciki irin haka "Zaki karyani auta" Ta fada a dan shagwabe tana riqe amna din. Da sauri ta dagata tana fadin "Am sorry adda.....wani irin mamaki uncle BB ya bani......yayi surprising dina irin wanda ya jima baimin ba......adda hutunmu na wannan shekarar zai fara daga Maldives......kinsan mafarkaina akan wajen kuwa?,kowanne year idan anzo zaben wanne qasa za'a je idan na kawo sai BB da saddiq sun kushemin.......yaa musaddiq kawai ke goyon baya na" Ta qarasa maganar muryarta a narke,da alama tana jin haushin yadda abun yake kasancewa. Dan murmushi sabreen ta saki,don ita inda take maganar ma batasan ina bane ballantana tasan muhimmancin da yake dashi ba da za'a dokanta aje. "Your dream have come true" "Really adda.......adda wannan shine tafiyan da zatafimin kowacce dadi da alama......ina da sister like you nima wannan karan.......ha saddiq ya daina yimin gori idan za'a fita......i don't know yadda zan miki bayanin Maldives......but gani ya kori ji" Dan qaramin murmushi ta aje mata kawai don ita bataga wani abun doki ba a nan. "Labari na biyu adda.....muna da biki,borno zatayi kira......bikin BB farouq date din yayi daidai da dawowarmu da sati biyu kacal". "Ma sha Allah.....Allah ya sanya alkhairi" "Wannan qarshen shekaran bame sauqi bace adda......can't wait......bari na bawa besty labari" Ta fadi tana laluben number wayar aminiyarta guda daya da take da ita. "Adda......anya ba honeymoon BB farouq ya hada muku keda hamma ba?" Amna ta dakata daga qoqarin kiran besty din nata da take tana duban sabreen. Bata jira ma sabreen ta bata amsa ba ta saki dan qaramin ihu tana tsalle gefe "It makes sense .....that's my big bro farouq" Amna ta fada tana dariya nishadi kaman zai kasheta. Baki kawai sabreen ta kama tana kallon amna "Amna......nace miki binku zanyi?". Tana dariya ta bata amsa " It's for the whole family adda........kowa ma yana tafiya hutu a wannan lokacin,indai kai under jadda family kake......hatta ma'aikatan dake aiki cikin gida lokacin hutunsu ne.....kawai dai,nayi mamakin rage date din da aka saba tafiyan" Ta fada tana duba wayarta. Rasa abinda sabreen zata fada tayi,maganan gaskiya ita sam bata shirya zuwa ko ina dasu ba,don bata jin tana cikin family dinsu,hasalima tazara take son bayarwa tsakaninsu. Duk sanda amna ke waya da qawarta ita tayi nisa wajen juya maganganun amnan. Wani irin mamaki ke tsarga mata,wai dama haka matar take tun usul?,ta yaya zata samu gaskiyan abinda amna ta gaya mata?,tun tale tale gurbataccen hali gareta?,indai haka ne mene yaran sukayi me muni da zata cutar dasu?. Kwanyarta ta sake harbawa,da qarfi da yaji ta soma qoqarin hada daya da biyu ko zata bata daidai *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Manzan Allah S A W yace "idan dayanku zaiyi fada/zai daki dan uwansa,to ya guji fuska/kada ya mari fuskarsa_ _sai a kiyaye,mari ko dukan fuska haramunne a musulunci_ "Biri yayi kama da mutum,tsananin qaunarta da duniya da kuma dukiya,shine silar qoqarin mallakar d'anta ta qarfi da yaji?,wannan shine daliinta?". Numfashi ta fitar me nauyi tana saka hannuwanta saman fuskarta " Adda......maamah keson magana dake" Amna da sunan maamah din ya fito ta true call din ya gaya mata wace ta fada kai tsaye,duk da bata da tabbacin da sabreen takeson magana. Hannu kawai ta bawa amna,tana maida wayar kunnenta. "Har yanzu kina kan bakanki?,kinci gaba da lamuntar jefa rayuwarki cikin hatsari maimakon tseratar da rayuwar taki?,a naki tsammanin kin tsira kin tseratar da yan uwanki?" "Idan kura tana maganin zawo ta yiwa kanta mana?". Dif maamah tayi,batayi gaggawar amsa mata ba,don maganar ta jefeta da wani qudundunanniyar ma'ana. "Kece kike sake tafka kuskure akan kuskure......kuma kwanaki dukka wani sirrinki yana qarewa.......komai yana dab da bakaduwa tamkar yadda iska ke diban lallausan gari tana watsashi cikin mutane........ashe ba kaina kika fara nuna rashin sanin darajar halittar D'A ba......ashe baiwa ce sanin darajar haihuwa a zuciyar iyaye......d'anki bashi da muhalli ko daya a zuciyata ko rayuwata,.....kaman yadda banda sha'awar zaman aure dashi......saidai fita a gidansa da rayuwarsa duka sai sanda naga dama... Kinsan yaushe nake nufi?" Bummm zuciyar maamah ta buga tun bataji qarshen zancen ba "Zan fita ne a sanda na gama karanta masa ainihin WACCE KALAR UWA yake da ita......ba don ina sonsa ba......sai don alkhairi guda daya tak da yayimin........ya karbo 'yan uwana daga hannunki ya kawominsu......abinda yayi silar takawarsu tudun muntsira......ya sanyasu hayewa duk wasu qananun qullinki.....zan saka masa da iya wannan,don bashi da wata nagarta ko guda daya da zata sanya sabreen sha'awar kasancewa dashi......ki riqe wannan......ki rubuta ki ajiye......sabreen ce zata zame miki silar BANKADA!" Tana kaiwa nan saita kashe wayar ta azata saman cinyarta tana ci gaba da lullube fuskarta "Ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis" Ta dinga maimaitawa,tsanar uwa da danta duka suna turereniya cikin zuciyarta. Ko da amna ta dawo abinci kawai taci ta fara list na abubuwan da zasu buqata lokacin tafiyar da abinda zasuje dashi. Ba wani abu data tofawa amna sai idanu da take binta dashi. Ba qaramin jarumta tayi ba da take iya binta da murmushi ba,gaba daya ganin abun take a wani abu maras yuwuwa,ita ba ahalinsu bace,bata kuma tunanin zata zama ahalin nasu.....hasalima gaba daya lissafinta yafi karkata ga qarawarta gaba kafin sukai ga dawowa daga yawon qasashe hudun da suka tsara zasuyi,kowacce qasa zaman sati guda zasuyi,ciki kuwa harda umra
Chapter 74 · 0% Book details