Sashe 38
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"ma sha Allah,sannunta da qoqari" Anni ta fada sanda ta gama ganin kayan da amna ta kawo wanda sabreen ta bata. "Tana da kirki anni......amma sai nake ganin hamma me irin halinsa ya dauko,she's so quite,batason hayaniya da yawa,bata fiya bada amsa ba ko magana,tafi yawan murmushi kawai". Murmushi anni ta sauke,har zuciyarta tana sake jin yarinyar tayi mata,a duk wani lokaci da maganarta zata tashi tana sake jin sabreen ta kwanta mata ne. "Ai dama sai hali yazo daya ake iya zama ko?,Allah ya qara hada hankulansu......yauwa farouq yayi nemanki kuwa sanda kika fita......naji kaman yana maganar zaku abuja passport dinki yayi expired,za'a sake miki wani". Idanu amna ta fiddo sannan ta qanqame anni "Anni hala Lokacin tafiya ya kusa?". Dan tureta kadan tayi daga jikinta "Gashi kuwa kin gani keda tafiye tafiye basa isarki" Dariyar jin dadi ta qyalqyale dashi. "Amna wannan tafiyan daban yake a rayuwata Allah,ba wani trip da yakaimin wannan dadi....whole family fa anni.....wannan karan kuma abun zaifimin dadi saboda nima na samu partner addana,adda sabreen,na daina maqalewa su ya saddiq suna wulaqantani,wannan karon tafiyar zai zama na musamman" Tayi.maganar with full excitement. Da kallo kawai amna ta bita kafin ta saki murmushi,ita kanta tasan tafiyar zata qara dadi musamman da idanunta zasu dinga gane mata fuad dinta da iyalinsa a gefe,cikon mafarkinta kenan "Anni bari naje na sameshi" Ta fada tana daga yatsunta gami da lissafa watan da tafiyar tasu zata kama "Yes" Ta furta tana jin farinciki yana lullubeta,saita cilla da sauri zata fita tana cewa "Dis time har abba fa sai na karbi kudin tsaraba a hannunshi,komai bibbiyu zan dinga siya nida addana" "Kunfi kusa ai" Anni ta bata amsa. Dakatawa daga fitar da anni taga amna tayi shi ya sanyata daga kai tana dubanta zuciyarta cike da tambaya. A sanyaye taga amna din ta dawo tana zama gefanta "Lafiyarki ke kuma?" Ta tambayeta tana nazartarta da kyau "Wani abu na gani anni a gidan hamma". Jin an ambaci fu'ad din ya sanyata tattara hankalinta akanta "Me kenan?" Ta amsawa amnan cikin zuciyarta tana fatan ba wata matsala bace a tsakaninsu. "Anni.....me aikin gidan maamah na gani,ita da wata budurwa......bansan budurwar ba amma tana kama da wannan qawar maamah din aminiyarta dinnan....." ".....hajja harira" Anni ta samu kanta da fada ba tare data shirya ba "Eh ita" Ajiyar zuciya anni ta fesar "To shine me amna?" Ta furta cikin hikima. Tun asalin tarbiyya anni irin matannan ne da basa bari yaro yana kawo musu hira ko maganar wani guri. Qasa amna tayi da idonta "Ba komai,kawai anni ji nayi jikina bai aminta dasu ba,daga yanayinsu fa anni kamar a gidan zasu kwana fa,qilan ma komawa gidan sukayi Allah anni". Ta fada tana bata rai. Da kallo tabi amnan,amna din ba yarinya ce qanqanuwa har can can ba,kome ake ciki ko yake faruwa tabbas dole tana gani tana kuma fahimta. "Hammanku majibancin lamura da jama'a ne,bazai zama abun mamaki ba idan anga sabbi ko baqin fuska a gidansa ba,kedai kici gaba da taya dukka 'yan uwanki da addu'a". Kai kawai amna ta gyada ba tare data samu cikakkiyar gamsuwa da bayanin anni ba,ta miqe tana fita daga dakin kamar yadda tayi niyya da farko. Fitar amna dukka sai hankalinta ya dawo jikinta,sam sam taji bata gamsu da wanzuwar zuwaira da waccar yarinyar a gidan ba. Tasan wacece maamah,tasan kuma dukkanin wanda ya rabu da ita yaya dabi'arsa zata iya kasancewa. Indai da wata manufa ko wani qullin daban aran maamah din,muddin tana raye ba zata taba bari haqarta ta cimma ruwa ba. Koda ta dauke idanu akan abubuwa da yawa,koda tayi kawaici akan abubuwa masu yawa....amma a nan ba zata bari ba,ba zata bari tabi fu'ad har rayuwa cikin gidansa ta ruguzata ba. Saita jawo wayarta tana qoqarin danna kiran. *SABREEN* Batasan adadin sau nawa ta leqa dining din ba da zummar ganin ko ta samu nasara ya taba kayan abincin?. Saidai a duk gewayen da zatayi bataga wani alamun taba komai ba cikin kayan dake danqare a table din ba. Ba iya yaci abincin bane kawai damuwarta ba aah......tanaso tayi amfani da wannan damar ta karbi wayarta a hannunsa,tanaso duk yadda za'a yi ta samu cikakken bayanin yadda su hudan suka koma qarqashin kulawa da mulkin maamah. Abun yana tsananin daure mata kai......ta yarda da momma bahijja....ta kumayi imanin haka siddan ba zata bari haka ta faru ba,duk dadai ma batasan ainihin wacece maamah din ba. Sam bata sako kawu rufai a ciki,shikam tasan ko ya fita sanin wacece mariya to zai aikata fiye da hakan ma. Zuwa sha daya na dare haqurinta ya gaza,ta miqe da wani irin kaiwa maqurar haquri tana yafa mayafinta saman doguwar rigar jikinta ba tare data buqaci dankwali ba ta sanya slippers dinta tana bude qofar dakin ta fice. Kamar magen dake kwanton farautar kamun bera haka ta dinga tafiya a hankali tana durfafar stair case din dake facing dinta. Duk taku daya sai bugun zuciyarta ya qaru,amma kuma tuna huda nadra da haneefa kadai ke qara mata qwarin gwiwa. Tana jin a kansu zata iya komai,zata kuma fuskanta da tunkarar komai da kowa. Cak ta tsaya a stairs din farko tana jin kaman wanda ke kusa sosai da ita idan ya qurawa qirjinta idanu zai iya ganin yadda zuciyarta ke bugawa ma. "Shi waye?,mutum ne kamar kowa,mutum ne kamar ni,bashi da wuta bashi da aljanna,bai isa kuma ya yankani ya cinye namana ba" Ta gayawa kanta da kanta murya can qasa qasa dukka tana zaton BUGUN ZUCIYARTA zai daidaita. Aqalla ta tsaya jiran mintuna kusan goma amma still ba abinda ya canza,sai kawai ta runtse idanunta ta kama makarin stairs din ta fara haurawa saman da wani irin confidence da batasan daga inda ta aro shi ba. Idan ba jikinta da hancinta ne ya mata qarya ba,to tabbas atmosphere da weather na wajen daban yake dana kowanne bangare na gidan. Wani irin lullumsan yanayi da wani irin kebantaccen qamshi da bata taba jin makamancinsa ba. Bata taba lura da cewa shimfidadden carpet bane kan stairs din sai a yanzun da qafafunta ke barazanar nutsewa a cikinsa. Bayan qafafunta sun nutse din kuma wani irin sassanyan yanayi tafukan qafarta ke riska a can cikin carpet din. Duk yadda taso jure qauyancinta amma abun yafi qarfinta,dole ta dinga bin carpet din da kallo har zuwa sanda ta riski wata pivot door wadda gefe da gefanta duka glass ne da bazaka iya hango ainihin parlor din ba,yayin da daga tsakiya ta kasance ta gogagen katako da aka yima design na zamani wanda ya maidata smart door. Tun daga zubin qofar tasan wajene na musamman kuma kebantacce,ta bangare guda kuma taji dadin samun qofar a bude,banda haka da sai tayi tsaiwar da qofar zata gama tantance wace kafin ta bata daman shiga parlor din. Mutum ne shi me wani irin jiki wanda baya qaunar zafi tun asali,saidai duk da hakan tsananin kare lafiyarsa ya sanya bai fiya kwararawa kansa A.c ba. Duk wanda ya sanshi ya sanshi da wannan dabi'ar na kaucewa abubuwa masu sanyi ciki kuwa harda ac din. Zaune yake saman wata qawatacciyar minotti sofa qwaya biyu dake bayan qwatattun Belgium sofas din da aka yiwa yalwataccen parlor din ado masu wani irin design me daukan hankali. Daga bayan Belgium sofas din aka yi wani muhalli na daban da aka zuba minotti sofas guda biyu wanda suke bashi daman kashingida ko miqe qafafunsa a duk sanda yaso. Dogayen qafafunsa na miqe saman sofa din,yayin da night shirt dinsa ke ajiye a gefe,daga shi sai gajeran wandon rigar wanda iyakacinsa cinyoyinsa. Hakan ya bayyana zallar halittar fararen cinyoyinsa dake lullube da baqa sidik din gargasa. Madaidaiciyar Ac ke kadawa cikin dakin,wadda ba lallai yanayin sanyin ya sanya ka fahimci itace ba saboda glass door din dake hannun hagu na falon da yake a bude,tatacciya iska me kyau dake tasowa daga jikin tsirran da aka qawata wajen dasu tana busowa zuwa cikin falon. Tattacciyar iskar data sanya masa kasala da mutuwar jiki,duk karsashin aikin da yakeyi ya soma raguwa. Turo qofar da akayi shi ya sanyashi dauke idanunsa daga karanta saqon da William ya tura masa ta email da suke buqatar ya duba da kyau ya karanta ya kuma sanya hannu. Fes yake ganin fuskarta wadda ke tsaye daga bakin qofar,fuskar data bayyana tsakanin lullubin mayafinta wanda yadan zame baya kadan ya bawa kwantacciyar sumar dake gaban goshinta daman bayyana sosai. Fararen idanunta da suke da wani irin haske ta zube a kansa wani abu na dukan zuciyarta saboda yadda ta sameshi. Ba wani abu da gajeran wandon jikinsa ya suturta sai qasan cibiyarsa zuwa cinyarsa,don bai samu daman qarasawa gwiwarsa bama sam. Ginannen jikin nasa daya samu kulawa ta kowanne fanni,motsa jiki,tsananin tsafta da kuma cima me kyau. Kwantaccen gashin dake cike da qirjinsa shi ya zamewa faffadan qirijinsa tamkar adon baqin abu bisa farin yanki ko farar takarda. Wani irin kwantaccen gashi daya shirya kansa da wani irin siririn layi har zuwa cibiyarsa ya zarce har qasa. Har cikin jikinta taji rudewa sosai,don wani abune da tsahon rayuwarta bata taba gani ba,hakazalika bata taba hasashen zata shigo ta sameshi a haka ba. Cikin zafin nama ta juya da niyyar komawa inda ta fito,don batajin zata iya ci gaba da daurewa kallon wannan halittar tasa. Da nasa salon hanzarin da kuma son qurewa rashin kunyarta tare da qoqarin fuskantar wani abu daga gareta ya dauki remote na qofan ya dannan close,take ta rufe kanta da wata irin gaggawa kamar qiftawar ido. Cak ta tsaya zuciyarta na bugawa sosai,tsoro yanaso ya kamata Amma kuma wannan dakakkiyar zuciyar ta taso mata,taji a ranta cewa idanma ta juya ta fita ta nuna masa ta damu dashi kenan ta kuma damu da wanzuwarsa a haka. Nasa idanun ya janye daga kanta yana hade ransa tsam waje daya. Duk da kallon data masa bai wuce na second biyar ba amma ya fahimci lallai ta qarewa jikinsa kallo. Hannu ya miqa gefansa ya jawo night shirt dinsa ya zura,sai ya koma ya jingina da fuskar minotti sofa din yana ci gaba scrolling saqon yana dubawa. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ _Daga hassan dan sumra R A yace,daga manzan Allah S A W yace:Duk macen da waliyyai biyu