← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 133 OF 215

Sashe 133

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

itama,banda abune da ubangiji ya sanyashi ya zama sirri tsakanin ma'aurata......tabbas duniya data cika da mamaki idan akaga matashin zaki gwarzo irin muhammad jadda yau a gaban mace yana mata kuka har haka. Ita kanta a rikice take,ta kuma aikatu sosai a hannunsa duk da controlling din kansa daya dinga qoqarin yi,kafin wani lokaci zazzafan zazzabi ya sake rafketa bayan amai data yi a jere har sau uku. Abinda ya daga hankalinsa kenan,ya tsaftacesu shi da ita,ya kuma shiryata cikin abayarta me sulbi shima ya sanya jallabiiyyarsa,ya duba asibiti mafi kusa ya kirasu donsu dauketa aje a duba masa ita,don bayajin zai iya jure wannan zazzabin yaci gaba da taba masa ita. Cikin mintuna qalilan motar al_ansar hospital ta iso suka wuce da ita. Baiko samu tsaiwa gaya musu ba,don kiran sallar farko kawai akayi,sai ya rubuta saqo kawai ya turawa Farooq. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ 114 Ko na second daya bai barta ta matsa daga jikinsa ba,tana kwance cikin jikinsa da wani irin yanayi. Cikin kowanne numfashi da zai sauke ko zai fitar jinsa takeyi da wani irin maqalallen yanayi a cikin zuciyarta,duk bayan minti kadan sai ya tambayeta "Ina ne kuma yake miki ciwo?,menene yake damunki?,me kikeso?" Ido kawai take lumshewa,don ita kadai tasan me takeji cikin qasusuwanta,saidai tana qoqarin nuna masa all is well saboda ta fahimci a gigice yake,amma duk da haka bataga nutsuwa a tattare dashi ba,kaman me gani har hanji,ya fahimci duk wani motsinta. Yanayin zazzabin ya sanya suka fara bata taimakon gaggawa a daki na musamman,kafin daga bisani su fara gudanar mata da test har kusan kala biyar suka tafi kan zasu dawo da result din. Sanda tayi farkawa na biyu bayan tayi sallar asuba gari ya waye sosai,kusan goma saura na safe. Shine mutum na farko data fara gani,fuskarsa ta fito fes yana zaune daga gaban gadonta yana jan tasbaharsa,lokaci lokaci yana duba saqonni a wayarsa. "Sabahal khair muffin" Cikin ba zata muryarta ta sauka a kunnensa. A nutse ya daga kansa ya sauke mata idanunsa. Itama shi take take kallo da fararen idanunta murmushi na fita daga fuskarta. "Muffin?......thanks ny world" Ya fadi sunan data bashin yana masa wani mugun dadi. "Sabahannur......khaifa asbahti?" Ya fada da tataccen larabcin da kana ji zakasan yasan qa'idar kowanne harafi a cikinsa yana nutsa tafin hannunsa cikin nata. "Asbahatu bikhair walhamdulillah" Ta maida masa da murmushin nan nata data tsinceshi saman fuskarta. Kansa ya langabe gefe guda kaman wani qaramin yaro,fuskarsa a narke yace mata. "I'm scared that am going to loose you,i know it's stupid,but i just can't stop thinking about it" Murmushi ta saki tana danjin nauyinsa kadan "Ka wahalar dani ne kawai......you won't lose me,am not going anywhere in sha Allah". Riqe hannunta yayi sosai cikin nasa. "That's my wish in sha Allah,you're the most important thing in my life" Sosai maganganunsa suke sake samun mazauni a zuciyarta,maganar amna data taba fada mata ta dawo mata fes akai. "You're the luckiest woman da kika samu hamma na" A yanzun take sake tabbatar da maganganun amnan,duk da a baya ta qaryata hakan. "Have your breakfast and then brush your teeth" Idanu tadan bude kadan tana kallonshi kafin ta sauke dubanta kan jerin kayan breakfast din daya jawo gabanta saman dan wani gado. "Ehnnnn" Ya fada yana dage mata girarsa,ya fahimci akwai abinda takeson fadi. "Brush din xai zama first ko?" Kai ya girgiza "No.....Brushing teeth after breakfast helps remove food particles and maintain oral hygiene" Shuru tayi murmushi na qwace mata,ba a banza ba takejin su musaddiq na gulmarsa. Komai nasa yasha banban dana kowa,tsare tsarensa ba irin na mutane bane. A jikinsa ya ajiyeta,ya dinga qoqarin bata breakfast din amma ta kasa cin komai a ciki. Iya black tea kawai ta dinga kurba,tana sha yana kallon fuskarta yana qarfafa mata gwiwa,a haka tasha rabi da qyar. Saidai tana kammalawa ya dawo duka,ta wankesu tsaf da aman shi da ita. Hankalinsa tashe ya danna wani guri,qasa da second sha biyar wata nurse ta iso. Zata karbi gyaran wajen ya dakatar da ita da harshen turanci. "Barmin zan gyara,aman nan da takeyi ne banaso,inaso shima ya tsaya ko ya tafi,ya kamata abinci ya tsaya a cikinta hakanan". "Likita yana dab da shigowa da dukka result na gwajin da akyi mata,sai a sannan zaa san abinda ya kamata ayi mata,amma yanzun xan sake saka mata ruwa don kada jikinta yayi rauni da yawa". Yana tsaye a gefe ranshi a jagule ta gama mata komai sannan ta fice,koda ya matso sai ya samu har bacci yayi awon gaba da ita. Ajiyar zuciya ya sauke,yana jin kamar ya dawo da ciwon jikinsa,agogo ya kalla.....yau din juma'a ce,yanason samun sahun gaba gaba a masallacin ma'aiki,duk da zuwa yanzun ma yasan ya makara,baya ga haka akwai wani al'amari me muhimmanci da zai aiwatar a can din,wanda bayajin akwai abinda zai sanyashi jinkirtawa ko dakatawa a wannan ranar ta juma'a. Rana ce mafi dacewa daya aiwatar da al'amarin. Idan yace zai koma gida ya shirya ma ya bata lokaci,don haka ya daga waya kawai ya kira farouq. "Ka turo saddiq ko musaddiq......ina buqatan Friday attire please". " Ina kusa da hospital dinma......but bari na koma na duba maka kayan...." "Thanks dude" "Don't mention it....ya jikin nata?" Dubansa ya mayar kanta sannan yace "Alhmdlh....she's sleeping,inaso naje mosque ne na dawo kafin ta farka" "Zaa kula maka da ita dude....kada ka damu,dukansu na barsu suna shiryawa zasu taho nan" "Alright" Ya fada a taqaice yana ajiye wayar. Ba jimawa farouq ya qaraso,dauke da wata leda me kauri. A nan parlor din dakin ya zauna,shi kuma ya wuce ciki inda gadon sabreen din yake. Cikin qanqanin lokaci ya shirya,Moroccan jallabiyya ce fara tas me asalin tsada me adon gold din zare,sai zagayayyar hular nan irin ta larabawa wadda set ce tare sukazo da hular da loafers din dake ciki iri daya. Wani irin sassanyan kyau ya aje,saika dauka balaraben Morocco dinne,ya matsa inda take kwance tana baccinta kaman ba abinda ke damunta,ya sunkuya yayi kissing dinta sannan ya fara takowa yana fitowa. Tun bai qaraso parlor din ba yaji muryar farouq dana likitan,yana tsaye sanye da farar lab coat dinsa suna hira sama sama da farouq din. Fuskarsa sake ya miqawa fuad hannu cikin sanin darajar dan adam da iya aiki,shima ya bashi suka gaisa,sannan ya fara bude takardun hannunsa. "After conducting the necessary tests,I'm pleased to inform you that your wife is pregnant...." Likitan ya fada da murmushi a fuskarsa. Karon farko da yaji ya koma kaman dan koyo a fannin turanci,kaman ma baya gane komai. Ya zubawa likitan idanu yana buqatar qarin bayani,muryar farouq ta dawo dashi hayyacinsa. "Alhamdulillah......ya rabb lakalhamd.....alhamdulillah......muna godiya sosai likita" Farouq daya kasa zama ya fada yana kama hannun likitan da kyau ya riqe cikin nasa. "Allah ya inganta......ya bata lafiya me dorewa.....ina tayaku murna" Abinda likitan ya fada kenan yana murmushi,sannan ya miqawa farouq takardan gwajin yana masa bayani. "Idan ta tashi a bacci za'a qarasa bata duk wani treatment daya kamata" "Mun gode" Farouq ya sake maimaitawa yana karbar takardan likitan ya juya ya fice. Ganin gaba daya fuad din ya zama wani statue ya sanya farouq kai masa duka "Dude......kayi nasara.....ka jefa qwallonka a raga daidai" Sai a sannan ya tattaro kalaman bakinsa da qyar "Am going to be a father?" Ya tambayi farouq cikin neman bayani gamsashe. "Yes dude.....bakai kadai ba,harda ni,anni zata zama grandma for the first time......zamuyi yaro ko yarinya dukanmu......" Bai jira farouq ya kammala ba yayi masa wata wawiyar runguma hawaye suna kubce masa. "Ya rabba.....antal kareemul lazi ya yaraddu sa'eelan,la'ilaha llla antar rahmanir raheem......shukran ya Allah,shukran" Sai muryarsa ta karye,ya dora fuskarsa saman kafadar farouq kuka nason qwace masa. "Bansan wannan jarumin muhammadun da saurin kuka ba.....duk da na lura sabreen ta maidashi baby da gaske" Farouq ya fada shima zuciyarsa tana raunana amma yana qoqarin bawa kansa qwarin gwiwa. Kansa y a daga yana riqe farouq da kyau,yanata qoqarin masa magana amma ya kasa,sai kawai ya jijjigashi yana kada kai sannan ya taka da sassarfa yana komawa dakin. Baccinta take kaman yadda ya fita ya barta,ya sake sumbatarta a goshi da labbanta,a hankali ya furta "Kece duniyata.....na gode,na gode" Sai ya rufe mata qofar yana komawa parlor din da sauri. "Zanje nayi sallah masallaci......zan kuma aiwatar da wani abu,idan zakaje mu hadu a hanya" Ya fada yana saka hannu ya kwashe takardun ya zubasu a aljihunsa sannan ya fita da sassarfa bayan ya sanar musu su aika me kula da ita zaije juma'a ya dawo. Ba inda yakejin ya kamata yaje ya juye farincikinsa da godiyarsa ga Allah irin cikin rauda.....ya godewa Allah daya samu wannan labarin a irin wannan wajen,banda haka ya tabbatar sai yayi qaramin hauka saboda farincikin yayi masa girman da zuciya ba zata iya daukarsa ba ita kadai. *_BAYAN AWA DAYA DA RABI_* *_B A Z A T A_* Anni,amna,musaddiq,saddiq dukkaninsu suna zaune a parlor din dakin asibitin bayan sun shiga sun dubata tana bacci sun fito. Huda haneefa nadra da kuma momma bahijja sune kadai daga cikin dakin,suna taba tasu hirar kadan kadan wadda ke cike da farincki da qaunar juna. Maamah dake zaune kallon kowa takeyi kawai daya bayan daya,yanayin yadda taga sabreen a yanzu ya soma sauke mata duk wani qwarin gwiwa da takejin tana dashi akan ba ciki bane a marar sabreen din. A shigarsu ta dazu ta gama qare mata kallo da kyau,ba abinda idanunta suka hango mata kuma banda dashewa irin ta me yaron ciki. Iya wannan abun kawai data gani ya sanya gumi ya fara yanko mata,duk da yadda zuciyarta keta qarfafata tana mata romon bakan cewa ba ciki bane. A yau din batajin zata matsa daga asibitin nan ba tare da an gwada yarinyar nan ba anga uban abinda yake damunta ba. Sake jan qaramin tsaki tayi jan qasa qasa tana gyara zamanta. Gaba daya zaman wajen takeji ya gundireta,daidai lokacin fu'ad ya turo qofar dakin da sallama a bakinsa ya shigo. Sannu da zuwa dukkaninsu suka fara masa banda maamah dake jifansa da wani irin kallo. Saddiq musaddiq da amna dukka suka gaidashi da tambayar me jiki,ya amsa musu cikin kulawa kafin ya qarasa gabansu anni yana gaidasu. Da qyar maamah ta amsa,ta bishi da kallo
Chapter 133 · 0% Book details