← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 215

Sashe 60

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read

murmushi na fita daga fuskarta lokaci bayan lokaci. Yau da wacce irin sa'a ta tashi?,wacce addu'a tayi yau?,babu....shine amsar data bawa kanta da kanta,don ko basmala cikakkiya bata jin tayi tun daga safe kawo yanzu. A dan fusace ta juyo jin an murda qofar ana shigowa,saboda ita din bata sakarwa kowa da kowa shigo mata guri kai tsaye ba....ko waye kai saika nema izini ta kuma baka. Idanu suka zubawa juna ita da hajja,saita janye cheque dinta tana lanqwasheshi ta daga pillow din kujerar gefanta ta saka a qasansa. Idanun hajja yana kai,abun kuma ya sake haifar mata da wani matsanancin bacin rai. Iya wannan abun da mariya takeyi kawai ya isa gaya mata komai daya faru ya faru ne bisa son ranta da kuma zabinta. Tunda suke da mariyan ba rufa rufa irin wannan tsakaninsu......tayi baqi ta kasa ganawa dasu a gabanta?,taga takarda duk da batasan ta mece ba amma mariyan ta jata ta boye?. "Kinga surukarki ko?,diyar ambassador khaleed mustapha" . Maamah ta sake maimaita abinda tasan already hajjan ta jishi. "Musaddiq ne kenan shima????". Kai da maamah kr girgizawa ya hana hajja qarasawa. " Fu'ad dai,d'ana fu'ad ". Da wani mahaukacin mamaki hajja ke bin maamah dake doka murmushi da kallo "Kinga Kalar surukan da ake fatan samu......wadanda za'a ciccibi juna....ba wadanda suke hangen turmusheka kai da mafarkinka ba.....maciya amana masu fatan kayi gyangadi su kafta maka sara.......zan shiga ciki in huta,ina da baqi anjima......idan kin gama ki rufe gurin.....karki damu kanki da lamarin laila......dama haka rayuwa take.....ka riqe dan wasu kaima a riqe naka,duniyar juyawa take haka da sauri........su madeena sun isheki zama.....ni kuma laila kadai ta isheni" Tana qarasa maganarta ta fara takawa zata fice _Daga nana aisha RA tace,manzan Allah S A W yace: "anayin wanka akan abubuwa guda biyar,janaba....da wankan juma'a...da idan anyi qaho,da wankan mamaci(mutum ya yiwa gawa wanka)_ "Mariya!" Hajja da zuwa lokacin ta kasa riqe kanta ta kirata a hautsine "Koda wasa......koda tsautsayi kada kiyi tunanin cutar da laila......karki manta dukka sirrikanki a nan suke" Tayi maganar tana nuna mata tafin hannunta. Murmushi ta kuma sakar mata sannan ta juyo sosai tana amsata. "Wadannan sirrikan da kike da ganin sun isa abun tunqaho.....nabar miki su halak malak kiyi yadda kikeso dasu.....laila kuwa a yanzu mallakina ce,baki da hurumi a kanta,idan kuma kina ganin zaki iya to bismilla,ga fili ga me doki,kinsan dakin dana sanya aka sauketa ai" Ta furta tana nuna mata hanya,sannan ta juya hankalinta kwance tana fita daga dakin.
Chapter 60 · 0% Book details