← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 215

Sashe 49

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zama matsala da takura a rayuwa,shi yasa bazai bari ta kunno rayuwarshi yanzu ba har sai sanda ya shirya ya kuma kebe mata lokaci nayin nata. Idanunshi akan motar BMW din da aka sanyasu a ciki,sai da yaga fitarsu a gidan sannan yayi musu umarni suka tashi motocin suna fita suma daga layin. Sauke labulen window din da yake bata daman ganin farfajiyar gidan tayi cikin wata irin matsananciyar fargaba da kuma tashin hankali. Gaba daya kowacce idea tata ta kunce,ta rasa wanne zaren tunani zata kamo?. Wacce irin baqar rana ce yau?,wanne tsautsayi ne qaddara ya sanyata lokacin shigowarsa ya kubce mata har ta saki yaran haka?. Idanunta ta mayar saman agogo......sai a sannan ta lura,yau ya sabawa lokacin shigowar tasa ne,ya shigo da wuri ba kaman yadda ya saba ba,sai tasa hannu tana sharbe gumin fuskarta da tafin hannunta. Da dan hanzari ta taka da kanta tana fita farfajiyar gidan tana qwalawa mansir kira,kiran daya sanyashi sakin duk abinda yakeyi ya qaraso babu shiri. "Ka fito da mota,kabi bayan motar jadda diamond zuwa gidan muhammadu......akwai yara da sukaje gaida matar gidan,suna shiga minti goma kacal ka aika su taso ka dawomin dasu......mansir?,idan ka kuskura aka samu akasi baka maidominsu akan kari ba to ka kuka da kanka......ban yarda ku biya ko ina ba......ban kuma yarda ka ajesu ako ina ba" Ta fada tana zare idanu tanaji a jikinta tamkar wani abu zai faru. "In sha Allahu ba zaa samu ko daya daga ciki ba" Daga haka saita juya tana komawa ciki. Kasa zama tayi ko a cikinma,a jikinta takejin kamar akwai wani abu da ba daidai ba "Ki kira zuwaira kisa ta kula miki da motsinsu" Wani sashe na zuciyarta ya bata shawara. Bibbiyu ta dinga hada stairs din tana haurawa samanta,cikin lokaci qanqani ta isa dakinta,ta zauna gefan gado tana daukan wayarta dake saman drawer ta fara kiran zuwairan. Saidai kash!,kiran farko aka shaida mata kwata kwata wayar a kashe take,ta sake gwadawa cikin rashin gamsuwa da bayanin farko na na'urar......still sukace mata yana a kashe,ta sake dai gwadawa a karo na uku,nan dinma amsar dukka daya ce,saita ajiye wayar a gefanta tana jan wani matsiyacin tsaki _Daga hassan dan sumra R A yace,daga manzan Allah S A W yace:Duk macen da waliyyai biyu suka aurar da ita ga maza mabanbanta a lokaci guda,to ita din mallakin na farkon ce(wanda aka fara daura mata aure dashi)_ "Tur da halinki zuwaira,Allah wadai da halinki" Ta fada tana cika tana batsewa,har cikin ranta tana jin kamar tayi tsuntsuwa ta tafi gidan da kanta. To amma kuma idan tayi duba ga wasu abubuwa,hakan bame yiwuwa bane,dole taci gaba da zama tana gwada kiran akai akai,yayi da idanunta ya ta'allaqa akan agogo tana qidanye da mintunan fitarsu daga gidan. Daga qarshe ta sare kan samun xuwaira,to amma dole tana da buqatar kiran wani da zame zame mata garkuwa a can gidan "Laila" Zuciyarta ta tunasar da ita. "Yauwa" Ta fada da madaukakin zumudi,ta soma lalubar number wayar lailan. Duk da safiya ce amma ta kusan awa guda da rabi a gidan nasu. Cikin asalin dakin da yake shine mallakinta,saman gadon sun qule ita da mahaifiyarta hajja harira wadda ta tsareta da idanu bayan ta gama zayyane mata karonsu da fu'ad na qarshe. Sai da tayi kaman ba zata daina kallon nata ba kafin taja wani tsaki tana dauke dubanta daga kanta. "To wai meye ma amfanin zamanki a gidan laila?,kada ki zama albasa mana wadda batayi halin ruwa ba?,na kaiki gidan badon kin rasa wajen zama ci sha ko sutura ko kuma gata cikin naku gidan ba.....na kaiki ne saboda ki karanci komai.....ki haddace komai ki kuma bi kowanne taku da motsi na kowa a gidan kafin mu fara gabatar da namu shirin koda kuwa.mariya batayi nasara ba......nasarar mariya ko faduwarta ba damuwata bane.....hasalima inda zata fadi hakan shine daidai a tare dani......kinsan me?" Kai laila ta girgiza tana jin faduwar gaba da kiran sunan maamah da akayi. "Nasarata itace ya kamata ta fara samuwa......nasarata ita ya kamata ta fara wanzuwa kafin ta mariya........ni ya kamata na fara samun fu'ad na mallaka miki shi......muddin mariya ta rigamu samun fu'ad to ba shakka dukkan wata nasara da muka sanya rai a kanta zata iya zuwa mana da tsauraran hanyoyi da matakai......shan kai nake da buqata mu yiwa mariya laila.....donme kikaje kika kwanta kina bacci?,waye ya gaya miki nasara na zuwa ta sameka har inda kaka?,bakisan fita ake a nemota ba?!" Tayi maganar da alamun qunan rai a cikin muryarta,hatta kuma da lailan ta karanci haka,saidai batasan me yasa a kwanakin nan takejin sam bata da damuwa akan wannan lissafin na hajja ba......tamkar wannan lissafin an zare mata shi kwata kwata daga zuciyarta. "Ban sauka ba hajja......kawai dai saina dinga jin kamar idan mukayi hakan bamu kyautawa maamah ba,kamar idan mukabi komai a sannu zaifi....." . Baki kawai hajja harira ta sake tana kallon laila da wani mamaki daya taru a fuskarta,kuma koda ta zubawa lailan idanu saita karanci da gaske take maganar. Tana shirin yin magana aka turo qofar aka shigo. Madeena ce dauke da serving tray data jero dukka kayan dadin da aka dafawa hajjan a matsayin abincin safe. Tun asuba take tsaye don kawai ta faranta mata,kuma bata da tabbacin zata yaba ko kuma tayi accepting abincin gaba daya. "Gasu hajja an gama....." Ta fada tana rusunawa ba tare data iya hada ido da ita ba. Wani abu me nauyi da girma ya riga ya sauka a zuciyarta game da zancan laila,don haka bacin ran daya taso mata maimakon ta huceshi akan laila sai ta fara ragewa akan madeena "Wannan wanne irin iskancin banza ne?,ina ciki muna sirri da yarinya saiki wani bankowa mutane daki?". Murya a karye cike da ladabi tace "Kiyi haquri,kin manta ke kikace idan na gama na kawo miki a daki zakici" "Naji da Allah.....koma dashi ki aje saman table......tsnnnnn" Ta qarasa da tsaki. "Awnnn..... Me dame kika dafa mata ne?" Laila tayi tambayar tana maida dubanta ga madeena wadda je tiri tirin fita da tray din. Ido kawai hajja ta zubawa laila tana mamakin yadda take nuna halin ko in kula da magana me muhimmanci irin wannan. Dawowa madeena tayi ta durqusa ta bude mata dukka bowls da warmers din,sai lailan ta karyar da wuya. "Wallahi meat pie nake mugun kwadayin ci da safen nan.......don Allah hadamin yaji naman rago cikin sosai" Ta fada kanta tsaye da sigar umarni. "Tom" Madeena ta amsawa lailan wadda a qalla tayi qanwa ta hudu da ita,ta miqe ta kwanukan tana sauka. "Idan da a rayuwa tsaiwa ake duba abinda ya kamata......inda a rayuwa jira ake sannan ayi abinda ya dace........tabbas ke kanki da baki juya matan yayunki kamar haka ba" Hajja tayi zancan tana tsare laila da ido tare da qoqarin maida mata girman zancan cikin zuciyarta. Dan muskutawa laila tayi tadan kashingida,har yanzu a ranta ita batajin damuwar komai,duk da kuwa bayan kowacce daqiqa sai hoton kyakkyawar fuskar nan tasa ta gilma ta gaban idonta,abinda ke sakata sakin ajiyar zuciya lokaci lokaci gami da sakin qaramin murmushi. "Inaso komai sauya.....inason ki canza akalarki daga yau.......dole gobe ki dawo ki karbi naki kayan aikin......ki kula da zuwaira......banason tasan komai.....bana son kuma ta fuskanci komai" Ta fada tana tsareta da ido. Saidai bata kai ga amsawa ba wayarta dake saman kanta ta dauki tsuwwa. Tana daga kwancen ta daga kanta tana duban me kiran,saidai ganin sunanta kadai ya sanyata wani irin zabura hadi da tashi zaune. Hakan kuma baiyi mata ba sai data zamo daga saman gadon ta durqusa a qasa sanda take daga kiran hade da sallama. Dukka wadannan abubuwan da tayi su suka ja hankalin hajjan sosai taji tanaso taji da wanne mutum me matuqar girma da daraja haka a rayuwarta take waya?. "Ina kwana maamah.....kin tashi lafiya?,kiyi haquri inata zuci zucin na kiraki na gaidaki da safen nan.....amma na kasa tuna waye zan kira". Maganar ta yiwa maamah banbarakwai,to amma bata wani kawo komai a ranta ba,duk da laila bata taba mata magana da ladabi rusunawa da kuma kirki irin haka ba "Ba komai,kina gida ne zan baki wani aiki?". Rawa jikinta ya hauyi saita miqe tana daukan mayafinta "Bana gida maamah.....amma bani minti goma sha biyar yanzu zan isa gidan,saiki gayamin abinda kikeso ayi miki ko mene". Mamaki kadan ya sake kamata,to amma a yanzu garkuwa kawai take nema don haka ta amsa mata da "Okay......idan kika isa ki kirani" "Ko kibar wayarma kawai on hold karki kashe yanzu yanzu zan isa,zanyi sauri ma saboda agama komai da wuri". Wani mamakin dai still ya kamata,amma sai tace " Zan sake kiranki" "To" Ta amsa mata tana sauke wayar. Jakarta ta kaiwa sura,kamar ma ta manta da hajja dake wajen,kowanne sashe na jikinta rawa yakeyi,ta jefa wayar a jaka ta rataya tana yafa mayafinta. Sai a sannan hajja da mamaki ya kasheta ta kira sunanta da qarfi "Waike da waye kike waya haka lokaci guda hankalinki ya tashi?". Murmushi ta sakarwa hajjan sanda take saka takalminta "Maamah ce fa?,ta tambayeni ne ina gida?,wani aiki zata sakani kinga ya kamata na koma ai.....bai kamata ma ace na fita ban tambayeta ba,amma zan bata haquri daga baya.....hajja na tafi,idan na gama mata da wuri zan tambayeta,idan ta barni gobe na dawo zan dawo". Mamaki da ganin almarar abun ya hanata cewa komai,ta sanqame a wajen kawai baki bude tana bin laila da kallo wadda keta sambada sauri kamar zataci da baka. *_turqashi?,wai meke faruwa?,nace meke faruwa ne jama'a?,shin qaiqayi ne koma kan masheqiya ko kuwa yaya?,wanda lamarin nan ya yiwa dadi ya danna 1 ,wanda baiji dadi ba ya danna 2_* *_gasu huda a hanyar zuwa gidan addansu,yaya zata kasance kenan?_* *_yanzu wasan zai fara tafiya daidai *_muje zuwa _Daga nana Aisha R.A tace:manzon Allah S A W yace:Duk matar da tayi aure ba tare da izinin waliyyinta ba,to aurenta batacce ne,idan mijin ya tare da ita taci sadakinta saboda halastar farjinta a gareshi_ Ware idanunta tayi sanda ta isa dining area,sai ta tsaya cak tana sake ware idanunta da kyau tamkar wadda bata gani sosai,kwanyarta na gayawa zuciyarta kawai yaudarar kanta takeyi,basu huda dinta bane.....ba nadra a wajen......auta haneefa tana hannun waccar azzalumar "Adda.." Muryoyinsu suka zame mata kamar tsani a gareta na tashi daga wani dogon
Chapter 49 · 0% Book details