← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 183 OF 215

Sashe 183

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Tunda ya dawo sallar asuba ya wuce gym,yana fatan hakan ya dawo masa da kuzarinsa daya rasa a kwanakin nan saboda tashe tashen hankulan da suka durfafoshi. Waya ya dauka kai tsaye ya kira Jordan ya bashi umarni ya koma gida ya dauko masa duniyarsa. Yana so nan din ya zame musu wani kebantaccen guri da ba kowa bane yasan da zamansa,da qwaqwalensu zasu huta na koda kwanaki uku ne kafin su koma cikin jama'a.
Sanda ya kammala shiryawa cikin sassauqar shirt da trouser sai ya wuce parlor. Da kansa ya shiga kitchen ya tafasa madarar shanu fresh one da turmeric dan kadan ginger da cloves ya dawo falon yana sipping kadan kadan yana kamo tashoshin daya saba kalla a lokuta irin wadannan da ake labarai na qasa.
Tashar farko cikin headline na news din hoton maamah ya gifta da anyo briefing na case dinta daga qasa. Zuciyarsa ta motsa tana bugawa da wani irin yanayi,sai kawai ya matsa remote din yana canza tasha.
Channel din daya kama sun fara news tuni,the next abinda ya faru shima dai hoton maamah ne da title tafka tafka na zargin kidnapping.....wannan channel din sun samu nasarar saka wani d'an yanki na tambayoyin da 'yan press din sukayi mata a Farfajiyar gidanta,wanda kusan duk me hankali idan ya kalla yasan maganganu ne kama kai.
"Subhanallah" Ya fadi yana sauke canza channel.
Already su sun gama,saidai.maimaicin kanun labarai da shima hoton maamah dana hajja harira harma dana fareeda da suka cika screen din. A nan ma baida buqatar yaji komai,yasan tunda haka ta faru duk inda zai kunna ma abinda zasu nuna masa kenan tamkar sunsan yana da alaqa da ita.
Wani zafi zuciyarsa ke mass,wani irin kud'a da quna take masa. Ya dauka ko meye maamah tayi....kuma ko meye akayi mata ba wani sauran abu daya rage da zai tada masa hankali a kanta ko ya qona masa rai,sai gashi bayyanarta a screen na TV dinsa yana neman hana mishi nutsuwa.
Har addu'a yakeyi......har fata yakeyi ta zabi adadin abinda take buqata daga gareshin.....mutanen dake kewaye dashi a yanzun,mutanen da yake rayuwa dasu a yanzun suna da matuqar muhimmamci a tattare dashi,mutane ne da bayajin idan wani abu maras kyau ya samesu ta sanadinsa.....ko ta sanadin arziqinsa lallai ba shakka bazai yafewa kansa ba,bazai iya jurewa ya rasa koda rai guda daya a cikinsu ba. Koda maamah ta karbi abinda takeso ta koma inda ta fito,har kullum,muddin da numfashi a gangar jikinsa bazai fasa mata addu'a ta shiriya ba darajar haihuwarsu da tayi.
Idanunsa basa wajen,amma tsaiwarta a bakin wajen yaji a jikinsa,don haka ya daga risunannun idanuwansa yana dubanta.
Tayi wani irin kyau da shigar mutanen turkey,wasu irin riga da wando da dan hijab dinsu me suturce jiki. Ya sauke idanunsa akan cikinta,sai yaga kaman ya qara tasawa,kaman ya qara girma a kwana daya tak da yayi bai ganta ba. Wani sanyi da rahama yaji yana sauka a zuciyarsa,sai ya miqa mata hannuwansa yana lumshe idanunsa,abinda ya bata tabbacin lallai yana buqatarta kusa dashi.
A nutse ta tako,wanda tun kafin ta iso inda yake qamshin nan nata,qamshin kabbasar nan tata ya soma kasheshi daga inda yake a zaunen(incense by kabo daughter....duniya ne sis,ki gwada ko sau daya,basai nace miki gobe ki koma ba,wannan tasted and trusted ne,bawai just normal tallan da bakasan ya kan abun yake ba(+234 803 211 9803).
Kasa dauke idonsa yayi daga kanta saboda wani salon tafiya da takeyi da yake fusgar hankalinsa,har ya qagu ta qaraso inda yake ya shaqi ni'imtaccen qamshin nan da yakejin inama kowanne second da zai shude a rayuwarsa zai samu daman shaqarsa?.
Kaman tasan da hakan,tana zuwa dab dashi saita cake ta tsaya,ta yamutse fuska,ta turo lips dinnan nata ta kuma juya masa qeya.
Ya masa nisa ya tsaya tambayarta abinda ya faru,don haka kanshi tsaye ya miqe,ya taka ya zagayo gabanta. Tsaiwa yayi yana duban kyakkyawan fuskarta data soma nuna yanayi na masu ciki,yasa hannuwansa duka biyun ya kama kunnensa.
"Na tuba......bazan qara ba" Kafadarta ta maqale.
"Ni saidai kayimin tsallen kwado".
"Done madam" Ya fada yana dan ja da baya still idanunsa a kanta.
Hannuwan rigarsa ya tattare,ya durqusa a nutse ya tattare qafafuwan wandonshi,sannan yayi bismillah ya tsugunna ya fara.
Da idanu take binsa,tanaso taga alamun ya gaji amma saita lura kaman ko a jikinsa. Bata rai tayi ta soma buga qafa.
"Ni ban yarda ba Allah.....so nake ka gaji fa". Murmushi ya kubce masa,da gaske mata rigimammu ne,suna kuma rigimar da ba dalili,musamman masu juna biyu,don haka yana kaiwa qarshen bangon ya zube warwas yana numfarfashin qarya gami da jujjuya kanshi.
Dariya dole ta kubce mata da abinda taga yana yi din,ta qarasa gabansa tana dan dukan qirjinsa a tausashe.
"Wannan duka cuwa cuwa ne......kawai yi kayi kawai badon haka bane". Dariya me siririn sauti ya saki,sai kawai ya jawota jikinsa,yayi mata kyakkyawar runguma yana fadin.
"Na gaji da wannan qwalelen da kikemin,qamshi duka ya buwayi hancina,amma kin hanamini jinsa yadda ya dace?,haka akeyi?" Ya qarasa fadi yana yaye hijabinta ya salubeshi ya wurgar gefe sannan ya cusa fuskarsa tsakanin wuyanta da qirjinta.
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
_Zafafabiyar_
152
*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*
*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*
*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*
*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*
*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*
*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_*
*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*
*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*
*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_*
*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*
*_HAIHUWA KIKAYI?_*
*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*
*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_*
_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_
08104553105
08127084190
*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*
*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*
Chapter 183 · 0% Book details