Sashe 187
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Cikin sati guda komai ya kammala na fitar da maamah din qasar Egypt. Fu'ad da kansa yace musaddiq yayi zamansa su samu hutu sosai da amna,don itama amna din har yanzu yana ganin kaman bata gama sakin jikinta ba bata warware gaba daya ba. Sanda yake shirin tafiyar sabreen ta sameshi a daki,ya daga kai daga abinda yakeyi yana dubanta. Sosai cikinta yake sake bayyana kanshi kowacce rana. Sosai cikin ke qara mata wani kyau,shi kansa zamanta a jikinta kyau yake mata. Hannuwansa ya harde yana kallonta da sassanyan murmushin nan nasa. A kwanakin gaba daya ta sake sauya masa,wani abu me sunan tattali da kulawa da bai sanshi ba yake samu daga gareta. Wani irin respect take bashi,bai taba jin bashi respect yana burgeshi ba kaman a kanta,ta maida kanta qasansa sosai,komai zatayi tana nuna ita din a qarqashinsa take,ita din mallakinsa ce.
"Sun hanaki bacci halan so abbee dinsu suke jira yazo tayasu hira" Ya fada yana bude mata hannayensa. Bata tsaya wani bata lokaci ba ta taho ta fada ciki,ta kuma lafe abinta. Ba wani guri da takejin tsananin aminci kaman qirjinsa,ba wani guri da take ji take kuma samun cikakkiyar nutsuwa irin qirjinsa,wani guri ne na musamman da takejin duk duniya bata da kamarshi.
"Na gama shirya nawa kayan fa hamma" Ta fada a shagwabe. Dan dagata kadan yayi daga jikinsa yana duban fuskarta.
"Zuwa ina kenan adda?".
" Egypt mana" Ta fada a shagwabe tana maqale kafada. Kai ya girgiza yana sakinta sannan ya fara takawa yana barin wajen
"No.....zaki zauna a nan har mu dawo,kinsan yanayin da kike ciki ai ko?,ko kin Manta wani hutun nake shirin baki ma?". Batace masa komai ba har ya qare zancen,saita sauke hannayenta data harde a qirjinta tana takawa a hankali zuwa inda yake zaune yana basarwa ta hanyar qirqirar wani aikin.
Dab dashi ta zauna har jikinsu yana gogar na juma,tasa hannunta ta jawo fuskarsa zuwa inda take kaman yadda shima yakeyi mata.
"Nasan me kake tunani,nasan abinda yasa ka fadi haka kuma.....amma kada ka manta.....har yanzu maamah uwa ce.....kuma nidin nayi alqawarin riqe hannunka gam,zamuyi tafiya bisa tafarkin rayuwa a tare,da dadi ko babu dadi right?". Kansa ya daga a hankali yana dubanta,ya rasa wadanne irin mutane haka Allah yayi masa rahama da ni'ima dasu?,sam basa duba sharri sai alkhairi a tare dashi,duk da irin uwar da Allah S W T yayi masa jarrabawa da ita.
"Koda maamah zata kasance me laifi a waje na.....nikam na yafe mata,har abada babu wata uwar da zata iya haifamin muhammad jadda sai ita.....ta kuma haifamin din,ina da abinda zan iya saka mata dashi?". Idanunsa ya lumshe kawai yana jin yadda soyayyarta ke tsatstsaga jikinsa. Addu'ar mace ta gari da yayi Allah ya bashi ma sama da abinda ya roqa din,yana jin kunyar idanun kowa......yana jin kunyar sanyasu su yiwa maamah wani hidima bayan dukka tarin sharrance sharrancenta a garesu,wanda har zuwa yanzu shikam yana ji a a jikinsa maamah din bata hau sirad'al mustaqeem ba da gasken gaske.
Hannunta ya riqe sosai cikin nasa da wani irin taushi.
"Na gode sosai my world......na gode duniyata". Murmushi ta sakar masa
"Ba godiya tsakanina dakai.....kome nayi maka kafi qarfinsa a wajena".
Tafiyar sai ta kasance me sassauci a tare dashi,don kasancewar sabreen a tare dashi cikin kowanne motsi a rayuwa ba qaramin qarfafa masa gwiwa yakeyi ba. Sun isa Egypt bisa jagorancin Dr awwab,an kuma gabatar da maamah ga qwararrun likitocin asibitin,wadanda suka dauki kwanaki suna dukkan bincike da gwaje gwaje.
To sakamakon dai guda daya ne,hawan jini ne me tsanani da har a Egypt dinma dai bai sauka ba,sai kuma wani abu data qulle a zuciyarta da suke ganin kaman shima yana barazanar taba lafiyar zuciyarta.
Sabreen ta girgiza matuqa,jikinta kuma ya sanyaya,ta qara cika da mamakin maamah,ta kuma sake sallamawa lamarinta,ta qara yarda da imani da yaqinin lallai wanda Allah ya shiryayye......ba wanda kuma ya isa ya shiryar da wanda Allah ya batar. Daga idanun maamah da kallon da take binta dashi duk da kalar hidimarta gareta ta karanci ba wani rusunawa ko nadama a tattare da ita......qaddararren ciwon daya zama jarrabawa game hankali ne kawai yayi mata cikas ya hanata duk wani sukuni.
Daga qarshe sun yanke zasu ci gaba da bata kulawa har na tsahon wata guda suga abinda hali yayi. Da taimakon qwararun nurses dake kula da maamah din aka soma dorata akan magunguna da therapy kala kala. Duk da akwai masu kula da ita din sabreen bata zauna ba,saidai ko yanzun sabreen ce zata bata abinci ba zata karba ba. Da idanu take kafeta,wani abu yana sake mata ciwo,duk sanda ta kalleta zuciyarta tana gaya mata.
"Yarinyar tayi winning a kanki,ke gaki a zaune saman wheelchair ko yatsarki baki iya dagawa". Rana ta farko da zuciyarta ta gaya mata haka bayan sun gama zama da ita ne sun wuce masaukin da suke kwana.
Kuka sosai ta dingayi,hawaye shabe shabe daya na bin daya,hawayen zallar baqinciki faduwa da kuma asarar da tayi.
Hakanan nurses din dake kwana da ita suka taru a kanta suna lallashinta,amma taqi tsaida hawayen tamkar ma suna tunzurata. Haqurin da suke bata ma sake bata mata rai yakeyi,ta rantse inda bakinta yana magantuwa su kansu da sai sunji magana iya magana.
Jirigi guda musaddiq da amna,farouq da fannah......saddiq da huda wadda ta soma murjewa ta fara qiba suka shigo Egypt duba maamah din.
A ranar taga baqar ranar da zata iya cewa kaf fadin rayuwarta bata taba ganin irinta ba. Kowa yana zaune da qugunsa......yana takawa da qafafunsa....hannu kai da qafufuwansu dama bakunansu gaba daya suna aiki amma banda ita?,banda nata?,ita kadai dai komai a kanta ya qare?. Wannan tunanin ya sake sakawa ta dinga fitar da hawaye,har numfashinta ya sarqe saida likita ya shigo ya mata allurar bacci.
"Har yanzu akwai wata danqararriyar damuwa a ranta.....kuma indai bata cireta ba treatment dinmu bazaiyi aiki ba,jininta bazai taba sauka ba.....tana da ciwon tun asali tayi wasa da magungunanta har sai daya zame mata haka,qodarta ta fara nuna alamun failure.....duk yadda zakuyi ta cire damuwa a ranta". Bayanan da likitan yayi musu kenan. Dukkaninsu sunsan wani abune me suna gaibu tilasta maamah ta cire damuwa a ranta,damuwar da dukkaninsu suka kasa gane ta meye idan ka dauke fu'ad sabreen da musaddiq.
A nasu hasashen it's high time ace maamah ta cire komai a ranta,so ba damuwar dabi'unta bane na baya,saidai fu'ad sabreen da musaddiq sunsan cewa HALI ZANEN DUTSE......BARIN HALI KUMA SAIDAI MUTUWA.
*_TURQASHI.....WAI ME KARATU NACE BA.....WAI SAI YAUSHE NE MAAMAH ZATASAN ANNABI YA FAKU?,SAI YAUSHE NE HALINNAN ZAI CANZA?_*