Sashe 160
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
fadi yana juyawa yana fasa shiga sitting room din. Hannunta ya kama. "Muje ku gaisa da malam.....mutumin kirki wanda ta silarsa ne na samu ilimin addini". Bata musa masa ba suka taka zuwa farfajiyar da aka qawata da kujerun zama. Tun daga nesa ta gane malam dinta,mutumin kirki na gasken gaske wanda kusan zata iya cewa tafi fu'ad sanin hakan. Mamaki sosai malam yayi sanda yake zama saman dayan kujerun dake wajen. Ta zame tana gaidashi kaman yadda fu'ad yayi. "Ashe da gaske rumaisa take?,sanda take gayamin ke kike auren muhammadu ba dauka shirmenta ne kawai.....muhammadu kayi sa'ar mata da gasken gaske" Malam ya fada yana maida dubansa ga fu'ad. Sabreen fu'ad din ya kalla sannan ya maida dubansa ga malam. "Tana da tausayi da taimako......tana da yawan sadaka da kuma kyauta,bata wata batayi sadaka ga mabuqata ba......marainiya ce muhammadu......nasan halinka kai dinma.....muna da kyakkyawan zaton nagarta daga gareka......ka riqeta hannu bibbiyu,lada biyu gareka,ladan riqon maraya,ga kuma ladan kula da iyali". "In sha Allah malam" Ya fada yana sadda kansa qasa. Inama ace malam yazo a sanda yake tsaka da fara cusgunawa rayuwarta?,inama ace malam yazo a sannan ya ceceshi daga feeling guilty da yakeyi a duk sanda ya tuna yadda ya mu'amalanceta a baya?. Duk da cewa ba laifinsa bane.......yayi dukkanin binciken da zai yi a matsayinsa na dan adam.....kuma abinda ya samu kenan. Da gaske ga a inda kudaden da duk take diba sukafi tafiya kenan fiye da jikin 'yan uwanta,sai yakejin wannan din dama ce ta sake samun wasu labaran a kanta ta wajen malam din. Hira kadan tayi da malam tana tambayarsa inna ta bada saqon gaisuwa ga rumaisa da shaida mata sun dawo sannan ta koma ciki. Da kanta ta shirya abun motsa baki ta kawowa malam din,duk da ma'u tace ta barshi amma tace sam malam yafi gaban haka. Qarfe tara tayi shirin bacci,don tunda ya fita ba sake jin motsinsa ba,ta tabbatar zai wahala idan ba baqin bane suka sha masa kai. Ta dawo parlor din farko da nufin daukan madarar shanu ma'u na fitowa a kitchen da alama ta gama komai na yau sai gobe kenan. Tana mata sallama amma idanunta akan kwalin hannun mau,tsirfa da tsarabe tsarabe irin na musu ciki haka kawai taji yawunta ya tsinke. "Amma fa ma'u meye wannan?" Kallon farin box din tayi tayi murmushi. "Wallahi amna ce ta aikomin dashi,wani doughnuts ne da ta taba ban guda daya ta yafi dani,sai tace zata sake sakawa a kawomin". "Mu gani" Sabreen ta fada tana matsowa,bude mata ma'u tayi take yawun bakinta ya qarasa tsinkewa gaba daya. "Don Allah ma'u ko guda daya ne" Ta fada tana narke fuska idonta akan doughnuts din da aka yiwa wankan madara. Dariya ta qwacewa ma'un,tasan halin ciki yafi gaban haka,bataga abinda zata samu ta hana sabreen din ba,bare wannan da nan da nan idan sunason wani za'a sake kawowa. "Jeki da kwalin gaba daya" Ta fadi tana tura mata kwalin. Har wani dan tsallen murna tayi,ta amshe tana godiya ta haura saman dashi. Gudu gudu ta gama shiryawa,ta ware gashinta saman bayanta ta haye sofa tana bude kwalin. Lashe baki tayi tana jin kaman ya mata nisa ta tsaya bude ledar a daidai kawai saita farke. "Uhmmmnnnnn" Ta fadi saboda yadda wata lafiyayyar madara ta hade da doughnuts din a bakinta "Ya salammmm" Ta sake fada sanda tayi gutsira ta uku,kawai saita kasa daurewa ta juya bayan kwalin ta kuwa dace da sunan mamallakiyar abun. *_Maman ummies delight_*+234 803 049 9555 A fili ta karanta komai tana lumshe ido,saita rasa wanne zata fara kira a tsakaninsu?. Landline kawai ta nufa ta soma kiran amna. "Addarmu" "Ba wani addarmu......yanzu amna harki samo abun arziqi irin haka amma ki kasa tunawa dani?". Tsam amna tayi tanaso ta tuna meye,ita ta dauka ma complain zatayi akan sun sauka bata nemeta ba " Adda mene?" "Doughnuts mana.....doughnuts din maman ummi". Dariya sosai ta zowa amna,duk yadda taso tareta kuwa sai data fito,karon farko data fara yarda masu cikin ajinsu da zasuga sun fiya fi'ili da neman fitina da gaske sukeyi bawai iya shege bane,yadda ta fadi doughnuts din maman ummin tar a bakinta saika rantse ta santa farin sani,kaman ba yaune cin farko ba. "To adda mu fara da bismillah mana.....dama anni ta gayamin triplets ne,suna sauka albishir din data fara yimin kenan da alama da abun take kwana tana tashi.....Allah ya bawa hamma juriya,ni dama guduwa zanyi na barku". Baki sabreen ta kama "Iyeeee,au gayamin kike aure zakiyi kenan" Kunya ta kama amna kaman sabreen tana gurin. "Ni na isa adda...." "Yanzu mu ajiye wannan maganar.....ina za'a samu doughnuts dinnan?,na kusa cinye wannan" Ido amna ta zaro. "Tana kaduna fa?,amma saga kaduna zuwa kano kawo doughnuts dinta kaman kina garinsu ne,sharp sharp ne.....idan ta kama sai asa hamma ya tashi jet a karbo miki" Dariya sosai maganan ta bawa sabreen,saidai da gaske dadin doughnuts din har cikin tsokokinta take jinsa. "Seriously amna.....am addicted to it......zan samu nayi breakfast dashi?" "Lemme call her......zaki samu koda wajen 10 ne haka in sha Allah.....ko duba flight din safe sai ayi idan akwai a sako miki.....amma indai shi zaki koma ci hamma yana kwale kwale" Amna ta fada tana qyaqyata dariya tayi kuma saurin katse kiran. "Kada fa haka ta kasance" Ta fada tana raba ido bayan ta lamushe taji bata gamsu ba. Ledar tabi ta tande madarar tasss ta saka kwalin a gaba har tana fatan inama tana sauran wani a ciki?. Bata ankara ba bacci yazo yayi awon gaba da ita sassaucin da aka samu kenan. Qarfe sha daya saura ya qaraso cikin parlor din,idanunsa a kanta,wani soyayyarta yakeji tana sake ratsa dukka qasusuwansa. Bayanan da ya sake ji daga bakin malam sai yakejin kamar ta cancanci sama da soyayyar da yake nuna mata.....kamar ta cancanci sama sa wannan rayuwar da takeyi a yanzu. Sai daya kammala komai a hankali don kada ya tasheta,ya dawo ya zauna da wayoyinsa. Su anni farouq da musaddiq duka yakeson kira,yanason komai ya kammala da wuri,don kwanaki hudu ne kadai suka rage daurin auren. Sai sannan idonsa ya sauka kan kwalin,ya jawo ya dudduba yana mamakin yadda aka yiwa ledar tasss,yadan girgiza kai ya kwashe ya zuba dustbin sannan ya dawo ya zauna yana sake duban fuskarta. Wani kyau take qarayi masa kullum,hakanan ba qaramin kyau bacci yakeyi mata ba,murmushi ya subucewa labbansa ya fara kiran farouq. Kira daya ya daga kaman yana kusa da wayar,muryarsa can qasa yayiwa fu'ad sallama. "Are you okay?" Fu'ad ya tambaya tana tsayawa cak. "Am okay dude" "Ma sha Allah.....ka karba envelope" "Na karba" "Ka bude?" "Na bude dude.....but I'm.....I'm speechless dude.......rubutun jikin invitation card dina da ruwan gold na ainihi?" Murmushi ya subucewa fu'ad. "Kafi qarfin wannan dude......kada ka sake magana akai.....akwai sadakin fannah a daga envelope din....have you seen it?" "What?,dowry fa kake magana dude?......wannan gold din ya ninka abinda suke karba a matsayin sadaki......babanta malami ne,kada yaga mun zura da yawa fa". "Fannah tafi qarfin haka a gurinmu....tunda takeson wannan tsohon tuzurun namu,ta kuma amince zata zauna mana dashi da zuciya daya.....sadakin mace baya yawa a musulunce,ko nawa aka bata yayi,saidai ma yayi kadan,yadda kace babanta malami ne nasan yasan da hakan,sayyadina umar yaso qayyadewa a zamaninsa,wata mata ta tunasar dashi annabi baiyi hakan ba, sai ya qyale shima.... Ka fahimta?" "Ya ilahi dude.....am speechless seriously" "Zamuyi fada dakai......ina fata ka riqe data din....kwana hudu......saura kwana hudu dude dina ya angwance" Sautin murmushinsa ya riski fu'ad,hakan kuma ya masa dadi a haka sukayi sallama. A duniya bayajin yana da wani abu da zai iya sakawa farouq dashi koda meye yayi masa. Musaddiq ya kira wannan karon,shima dai kaman yana kusa da wayar ya daga. Muryarsa da mugun sanyi ya amsa sallamar,still shima tambayarsa yayi lafiya yake?. "I'm fine hamma" "Maamah ko?" Shuru musaddiq yayi yana mamakin yadda ya gano haka ta farat daya. Shurunsa ya bawa fu'ad tabbaci,ya sauke numfashi. "Idan ka dorama kanka daukan damuwoyinta ba inda zakaje a rayuwa,zakayita zamane kamar a inda ta tafi ta barka ba tare da damuwan yadda rayuwa zata kasance maka ba.....na kiraka na gaya maka,kayi magana da musaddiq kai dashi ku duba gidajen nan dana bashi details dinsu ku zaba,za'a hade bikinka sana farouq in sha Allah,so ka ajiye damuwan da bata cancanci damuwarka ba.....ka fuskanci rayuwa da reality dinka.....but kada ka sake ka manta da wannan......ka riqe mana amna sai mutuwa ce zata raba". Mutuwar daya fada ta saukar masa da wani irin matsanancin faduwar gaba......ta kuma tuna masa da maganarsu ta dazu da maamah. "Mutuwa hamma?". "Yes.....mutuwa,saboda ita kadaice ta isa ta raba Soyayyar masoya" Shuru ne ya wanzu tsakaninsa da shi,har sai da fu'ad din yace. "Kana layi?" "Inaji hamma" "Good......komai da amna zata buqata ka rubuta ka turamin.....bance ko sisinka ka saka a bikinka ba" Baima jira ya masa godiya ba ya katse,saboda baya buqatarta,yanajin wani wajibinsa ne ya saukeshi. Anni ce ta qarshe daya kira,amna na kusa da ita ta miqa mata wayar. Ban gajiya suka yiwa junansu,sannan itama ya buqaci ta bada duk wani abu da take buqata. "Muhammadu kabar 'yan uwanka suyi wani abun mana?" Murmushi yayi "Anni sai idan bana raye.....ki fadawa amna ta rubuta komai da take buqata na lefe.....idanma ba zata iya ba tazo nan gidan su hadu ita da duniyat....." Saurin katsewa yayi bai qarasa ba,kunya ta kamashi ya aza hannunsa aka yana sosa sumarsa. Murmushi me sauti ya qwacewa anni "Ita da duniyarka ameenatu" Murmushi shima ya saki. "Su rubuta komai,bance ta dauke masa komai ba". Kaman sauran bai jira ta masa wata godiya ba ya katse wayar,ya zubawa sabreen ido wani abu yana yawo cikin ranshi. Da alama baccin ya mata dadi sosai,amma dole ya tasheta don akwai magana me muhimmanci da zasuyi da bata buqatar takai safiya,yana ganin kaman tayi nisa. Wayar anni ta ajjiye gefanta,tana jin wani abu yana sauka a ranta. Tabbas fu'ad din wani kyautar Allah ne a garesu,bawai don dukiyar da yake da ita ba.....aah....ta jima da sanin haka tun yana fu'ad dinsa dan makaranta secondary school,fu'ad dan bautar qasa. Wata irin zuciya ce shimfide a qirjinsa,wani irin dattako daya girmi shekarunsa......wani irin halin girma me dumbin yawa. "Tabbas mariya inda kinsan irin kyauta da alkhairin da Allah yayi miki a rayuwa da baki gudu