Sashe 67
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wasa ko digo cikin kalamansa. Itakam a yanzun ina ta shirya mutuwa?,a irin wannan qadamin da take lissafin sake inganta rayuwarta da jin dadin da yake hange daga wasu?,itama ta samu ta dandala ta baza nata ikon da isar kafin zuwan randa zata bar numfashi?,shine tun a yanzu a gabanta wannan manya manyan alkaba'in yake faruwa?. Idanu ya zuba mata da kyau yana qoqarin karantarta,saidai kuma kafin yayi nisa an murza pivot door din daga can wajen falon an shigo. Farouq ne a gaba,Dr rubayya a tsakiya sai saddiq daga bayanta . Shigowarsun kawai cikin falon....hada idanunsa da farouq sai yaji kaman an janye wani kaso na bala'i da masifar da yakeji tana kunnuwa cikin zuciyarsa. Wani irin tashin hankalin da baisan dame zai fasaltashi ba. Dr rubayya na qoqarin gaidashi.....saidai shi hanyar hallway din kawai yake nuna mata da yatsa ba tare da yace komai ba,sai itama bata sake magana ba kasancewar halinsa ba baqonta bane,ta wuce da kayan aikinta kai tsaye zuwa hanyar. "Ka leqa ka kiramin saddam......suzo.su biyu" Yace da saddiq da rinannun idanunsa da suka sanya saddiq shan jinin jikinsa bayan mutane biyun da ya gani zube a wajen. Shima baice komai ba ya juya yana fita daga falon. A nutse farouq ya isa gabanshi,ba tare da yace komai ba duk da idanunsa na nuna kaduwa da abinda yake gani ya kama hannunsa yadan juya sannan ya saki "Dude.......wai meke faruwa?" Ya qarasa maganar yana saka idanunsa cikin na fu'ad din. Janye nasa idon faud din yayi daga na Farooq yana hadiye wani abu me tauri daga qasan zuciyarsa. To shi ta yaya ma zai fara bada wannan mummunan labarin?,yace meye?,yace masa wiwi ya kamasu suna sha har ya bugu asthma dinta ya tashi?,ko yace masa ta gayyato maza cikin gidan sun bugu sukaso gwada mata qarfi?,ko kuma yace sharri akayi mata?,barayi zai kirasu ko 'yan fashi?,zaice sun hauro masa gida ne?,gida ma irin nasa?,gidan da ba wani abu daya isa ya shiga ko ya fita cikinsa saida cikakken tsaro da kulawar security......waye hankalinsa zai dauka?,waye zai yadda da wannan labarin?. "Ka kwashesu ka sakaminsu a cage din dogs dincan....." Ya fada yana miqewa sanda hanzari ke qoqarin riqo rigarsa a gigice "Kayi mana rai oga.....ka hukuntamu duk yadda kaso,amma kada ka hadamu da karnukan can.....wallahi ko kafin safiya sun gama cinye namanmu oga...." Yayi magana fitsarin da yaketa son riqeshi yana kubce masa. Tun shigowarsu gidan yanayin karnukan ya tabbatar masa sunsha banban da dukka karnuka daya sani. Basu bi ta gefensu ba.....amma wani abun mamaki yadda suketa haushi ya ninku,yana ganin sanda me kula dasu ya dubasu,ya kuma yiwa security na gidan magana suna sake bincike sassannin gidan amma basu ga komai ba saboda sun shigo ne ta hanya mafi sirri da samun tabbaci,kuma sun samu mafakar da binciken me bincike bazai taba kaiwa nan ba. "What are you waiting for?!!!" Fu'ad da dama dukkaninsu suma a cike yake dasu ya fada a tsawace,ba shiri suka durfafesu,hanzari yayi wuf ya kama qafarsa yana sake roqonsa. Wani wawan duka yakai masa da qafar daya sanya hanzari zubewa warwas,basu saurara masa ba suka sungumeshi suka hada da mashkur da tsabar razana ya kasa magana,sai yakejin kamar qiyama ce zata tashi. Yasan illar karnukan,don sanda yake sharafinsa ya ajesu a gidansa sun kusa guda biyar,hakanan baisan adadin mutanen da ya sanya suka yagalgala ba. "Karku sakasu a cikin cage din.....ku ajiyesu dakin kusa dashi" Ya basu umarni sanda suke kicin kicin fita dashi. "Okay sir" Suka amsa masa sanin wayeye farouq wajen boss din nasu. Shi daya ne duk duniya yake tada hukuncin da fu'ad yayi kuma ta zauna ba tare da haufi ko kankare ba,shi yasa suka karba umarnin nasa kaman yadda ya basu. Yadda yaga komai yasan ba lafiya ba.......yadda kuma yaga yanayin hannunsa da gidan ya tabbatar akwai gagarumin wani abu daya faru.....uwa uba wani kwantaccen fushi d yake gani a fuskar Fu'ad ya sanar masa akwai matsala ko a yadda ya fita a fusace. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ Tun bai qarasa inda yake hangen security na gidan daya tara ba yakejin muryarsa dauke da fushi me nauyi. Fada yake da duka zuciyarsa da jikinsa ma,sam kaman ya manta dare ne a yanzun......daren ma kuma irin daren da akayi ruwan sama ya dauke wanda ke ninka kowanne dare a shuru da daukewar sawu. "Your services are no longer required......you were fired!" "Ya salam" Farouq ya fadi,abinda yaketa sauri ya dakatar dashi kenan. Fushinsa na yau yanata bashi mamaki,sau tari shike daukan abu da sauqi......yawancin lokuta shike jan qafa da jan lokaci akan abubuwa irin wadannan......yana bin komai da lura a kuma tsare,har sai ya tabbatar dashi a inda ya dace. Kasa cewa komai yayi,don su kansu ma'aikatan da security din dake on duty a daren kowa cikin matuqar tashin hankali yake. Yadda suke roqonsa da mabanbantan harsunansu dukka sai suka bawa farouq din tausayi. Kowanne a cikinsu idan ka dubi fuskarsa ya kadu da hukuncin ba zata na me gidan nasu. "Calm down.....ya isa" Farouq ya isa gabansu yana fadi bayan komawar fu'ad din ciki. Hankulansu kuwa suka bashi cikin mutuwar jiki hankali a tashe. "Ku kwantar da hankalinku.....kowa ya koma bakin aikinsa kafin wayewar gari......but,ku sake tsaurara kula kafin muga abinda hali zaiyi. Duk da bawai tabbaci ya basu na cewa ya dawo dasu bakin aiki ba amma hakan ya faranta musu. Sun sani babu wani guri da zasu samu walwalar rayuwa da 'yanci da albashi me tsananin azabar tsoka kaman gidan jadda.....salary yake musu na kece raini......irin salary din da sunyi imani ko a villa suke aiki babu me biyansu irinsa. Uwa uba ga ihsani da alkhairi da suke samu kowanne lokaci,wanda ya kusan kamo abinda ake biyansu albashin aikinsu. Da yawansu suna jin idan ba gidan Muhammad jadda ba babu a inda zasu iya aiki,shi yasa suke riqe da aikinsu fiye da yadda ma yake tsammanin zasuyi. A parlor ya sameshi a tsaye kaman wanda zama ya gagareshi. Baice masa komai ba ya taka inda yake tsayen ya riqe hannunsa sannan ya wuce dashi,suka ratsa hallway din suka saura samansa. Saman monotti sofa ya zaunar dashi,ya taka da kansa zuwa shiyyar da aka tanada don ajjiye first aid box,don kusan yasan komai na gidan tunda shine ma tsara yadda zai kasance din. A gabansa ya zauna,ya bude box din ya ciro cotton wool da spirit ya tsiyaya ya fara goge masa ciwon. Sai a yanzu yake danjin radadin da hannun ke masa amma kadan kadan,saidai har yanzu abinda yakeji a zuciyarsa ya dara wanda ke a hannunsa. "Ko meye da sauqi ake daukarsa......da irin wannan temper din da kake ji a ranka komai fa bazai warware ba" Farouq ya fada yana qarasa goge masan,har yanzu kuma yana mamakin abinda ya birkita nutsatsen mutum irin fu'ad din. Duk da ya sani,ba abu bane me sauqi a keta alfarmar gidanka a shigo maka ba......to amma kuma yadda yasan fu'ad zai iya cewa tun wani zamani can daya shude rabon da yaga wannan attitude din a tattare dashi. Wayar tafi da gidanka din dake falon,wadda ke ajiye kusa da console mirror din parlor din ce ta dauki tsuwwa. Saddiq dake zaune daga gefe dukka jikinsa a mace ne ya dauka "Daga hallway bedroom ne" "Ka daga ko Dr rubayya ce" Farouq ya fadi sanda yake tattare ragowa ragowan audugan da yayi amfani dashi. Maganan second goma sukayi kwata kwata,ya sauke wayar yana duban farouq "Dr ce ke magana.....tace ta kammala......amma wai tanason ganin hamma". "Ka gaya mata tayi abinda ya dace kawai basai nazo ba" Ya fada yana jin ciwon kan daya tashi da jin dadin ya sauka yana son dawowa. Kai farouq ya girgiza yana dubansa,muryarsa a qasa qasa yadda saddiq bazaijishi ba yace "Dole kaje tunda tace kaje din.....dole saika gwadawa duniya halinka?" Idanunsa da har yanzu basu koma fararensu ba ya watsawa farouq,kaman zai magana sai kuma ya fasa ya tsuke bakinsa. Kamar bazai tashi ba kafin ya miqe yana kiran sunan Allah,wanda motsawar bakinsa ne kadai zaisa gane hakan. A hankali yake sauka zuwa qasan,saidai duk sanda ya kusanci dakin sai abun daya faru mintunan baya yayita dawo masa. Bama irin idan ya tuna ba komai a jikinta......daga ita sai towel sai hijab,sai yaji tamkar iskar da yake shaqa tayi masa kadan. Su biyu a daki tana daga ita sai shi.....su biyu a dakin da babu cikakkiyar sutura a jikinta......gaban hijabinta yasha cukuikuiya?.....duk sanda ya kawo nan sai ya lumshe idonsa saboda ji yake kaman an dauka adda an kafta masa sara a tsakiyar kansa. Handle din ya murza ya tura ya shiga da sallama saman labbansa. Ma'u dake gyara dakin ta dago daga kwashe sharar data gama,ta rusuna tana gaidashi duk da dare ne,sannan ta kwashe dustpan da vacuum cleaner din tayi waje dasu. Haka kawai ya samu kansa da bayason kallon fuskarta,don ba abinda yake tuna masa sai a yanayin data fado jikinsa. "Numfashinta ya koma normal,kuma yanzun haka bacci take me kyau.....ko da wanne lokaci ma zata farka abinta........amma please sir......koda asthma dinta baiyi tsanani ba at least ya kamata ace an ajjiye mata in healer.....and ya kamata ta dinga kula da gujewa ta'ammali da abubuwa masu hayaqi da yawa". Kai kawai ya jinjina ma Dr rubayya "Allah ya qara afuwa yasa kaffara.......idan kuma ana buqatar wani abun.....am ready in sha Allah,koda yaushe kuka kirani am available for your needs". "Thank you" Ya fada can qasa da kalar miskilancin nan nasa da ba wani baqon abu bane a wajenta. Already kafin ta fita ya kira saddiq ya gaya masa gata nan su maidata gida,yana kuma sauke wayar kiran farouq ya shigo masa "Mu duka mun wuce gida,but.....na kira wasu daga cikin guards dinka an qara akan na cikin gidan......in sha Allah kome zaiyi daidai......but please please.....karka dauki doka a hannunka akan mutanen nan". Farouq ya fada cikin narke murya. Ya dade da sanin halinsa,muddin ranshi yakai qololuwar baci irin wannan bai iya hukunci ba. "Kaji?" Farouq ya sake maimaitawa jin yayi shuru baice komai ba. "Alright" Ya fadi a hankali kamar wanda maqoronsa ke masa ciwo yana gintse kiran. Iska ya sake furz arwa daga bakinsa,daga jikinsa har zuciyarsa babu wani abu dake masa dadi,sai ciwo kawai.....wani irin ciwo