Sashe 47
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Qarfe tara na safiyar alhamis ce wadda aka wayi gari da lullumi qwarai,sakamakon hadarin farko daya fara hada jikinsa tun bayan sallar asubahi. Bai bada ruwa ba amma kuma ya yiwa rana shamaki daga fitowa tayi rawar gaban hantsi kamar yadda ta saba kowacce safiya saman sararin samaniya. Yanayin sai ya haifar da yanayi me dadi da kuma sanyaya zukatan da suke cikin wani yanayi. A irin wannan lokacin ne muhammad jadda mamallakin kamfanin jadda diamondchore resources yake saukowa a hankali daga samanshi. Cikin shigar aiki,saidai kuma yau zaka dauka juma'a ce saboda shigar kaftan yayi. Dinkin zamani daya zauna masa sosai,ya kuma fidda sigar kyan nan nasa da kana kallonsa zaka tabbatar tabbas halfcast ne shi din wato ruwa biyu. Cikin parlor din ya samu tuni ameh ya kammala shirya masa komai na breakfast dinsa. Ameh din shi ya koma masa girki tun bayan wancan abun daya faru,yaja daya daga cikin kujerun wajen ya zauna ameh din ya gaidashi cikin rusunawa. Amsawa yayi da kulawa sannan ya fara serving nasa,yana yi yana dibansa da labarai,wanda kusan dukansu labaran da suka fita ne a jaridar safiyar. Ameh din yana da karance karance da yawan sauraran kafafen yada labarai,don haka a mafi yawan lokuta idan bai samu damar duba news paper ba shike bashi latest na cikinsu. A nutse ta maida littafin amdatul ahkam da take dubawa,ta kuma d'auki zaduzzaujaini ta sakashi a ciki don yin alama akan inda ta tsaya din. Saman side bed drawer tayi masa kyakkyawar ajiya tana jin wata nutsuwa tana ratsata. Sati guda kacal kenan da fara karatunsu da rumaisa'u d'iyar malam amma wani nutsuwa takeji da gamsuwa da karatun. Rumaisa'u din da tayi tsananin mamakin ganinta a matsayin malamarta da ya dauko mata domin daukan karatun addini a hannunta. Zuwanta kusan uku tana rejecting tana qin fitowa......sai ana hudun ta fito da zummar yiwa malamin ko malamar bayanin ta daina wahalar da kanta tana zuwa......ta gayawa wanda ya aikota dalibar bata da buqatar wani karatun. Ganin rumaisa'u din sai ya zagwanye komai daga zuciyarta,ta cika da mamakin zuwanta gidan,saidai daga baya rumaisa'u din ta gaya mata "Hamma muhammad tsohon dalibin malam ne" "Gwara da kika ce tsohon" Sabreen ta furta a ranta. Don tako ta ina bataga ta inda ya dace ko ya cancanta mugu maqetacin mutum kamar fu'ad din ba ya hada alaqa da malam ba. Daga haka ba wani zance daya qara shiga tsakaninsu,sai hiran duniya kawai da kuma karatun daya biyo baya. Da farko kawai dai tana sauraren rumaisa'u dinne,amma karatun kwata bayayi mata wani armashi ko burgeta. Saidai lokaci guda kuma a rana daya data arawa rumaisa'u hankalinta sai taji karatun ya fara shiga kanta,mafari kenan data fara hada hankalinta da zummar Tsintar abinda ta Tsinta,saidai tafi tafi sai ta fahimci karatun yafi qarfin ka tsinta kawai. Ita kanta rumaisa'u mamaki takeyi ainun....mamakin yadda karatun yake gudu saboda yadda suke qara karatun da yawa. Ta sallama da gaske karatun yana gudu ne saboda wata irin sharp brain da Allah ya bawa sabreen din,irin kwanyar da bata taba ganin irinta ba. Don duka karatun da sukayi da yammaci,zuwa wani yammaci din sabreen din ta narkashi ya koma cikin kwanyarta. Tun asali tana da bala'in son karatu,musamman na addini din,saidai wani dalilin me zuwa ya ture wani. Ratayuwar hidimar qannenta saman wuya da kafadunta ya sanya tilas ta haqura da komai ta tattara ta ajiye,a yanzun kuma data fara shiga cikin abun sosai sai takejin komai kamar an yaye mata wani hijabi ne da da ya lullube kwanya da idanunta. Tun sanda ta fahimci ya ajiye cook dinsa cikin gidan saita saita lokacin ta,sanda zata fito tayi sabgarta daga shi har cook din nasa basa gidan,hakazalika kafin su dawo ta kammala komai ta koma daki abinta. Tayi mamakin yau da taji yunwa da safe da wuri haka,to amma kuma idan ta tuna ba wani abun arziqi take ci ba musamman jiya da dare bata saka wani abu me muhimmanci a bakinta ba sai taga ba abun mamaki bane. Indonesian hijab down squeeze ta saka saman soft and cotton nigh gown din jikinta da bata fidda siffarta ba,saidai tadan lafe mata a mazaunai saboda taushinta. Hijab din ya qara qawata mata fuska,fuskar data fita sosai ta tsakiyar hijab din da wani irin kyau kai kace itama haifaffiyar Indonesia dince. Ta qarasa gaban mirror ta qara turare a jikinta dan kadan kamar yadda ya zame mata wajibi,sai ta tsaya tana duban fuskartata. Wani irin glowing skin dinta yakeyi wanda ita kanta ta rasa dalili,saidai a yawancin lokuta tana bawa kanta amsa da wataqila zaman guri daya ne,sabanin baya da kullum muddin gari zai waye rana ta fito to zata saka qafarta a waje ta fita. A hankali take tako hallway din,yau kawai tana jin nishadi cikin ranta sosai da cikakkiyar nutsuwar da batasan dalilinta ba,kwanyarta tana bitar wasu daga cikin karatuttukan data haddace,a haka ta rasa parlour na farko ta wuce zuwa na biyu. Tana murza glass door din ta sanyo qafafunta ya daga idanunsa a hankali daga inda yake zaune ya zubesu fes saman fuskarta,idonta ya shiga nasa,sai ta janye nata idon a hankali,ta kuma ja da baya tana komawa da bayan a maimakon fitowa da tayi niyyar yi. Sam bata qaunar gamuwa dashi,a kwanakin data janye kanta daga komai da zai sanya su hadu ta kama karatunta sai take samun wata irin nutsuwa a zuciyarta. Ta dauki kwanaki rabon daya sanyata cikin idanunsa,daga shi har maamah sai takeji kamar Allah ne yayi mata maganin matsalarsu. Janye nasa idanun yayi shima bayan ta koma da baya tana kuma komawa ciki. Yadan jijjiga kai kadan yana daukan mug din gabansa ya sanya a bakinsa. Tana gyara bedroom dinsa kamar yadda sukayi sharadi,saidai daga wannan ko gilmawarta bai sake gani ba tun daga ranar. Can qasan zuciyarsa tana cike da wasi wasi da kuma qiyasi akan abubuwa da dama. Sai yake zargin shurunta dana maamah dukka kamar akwai wani magana a qasa,don haka ya jawo wayarsa ya kira me sunan malam. Cikin qasa da second ashirin suka gama magana,ya shaida masa ya nema farouq ya turo amintacce kuma sirrintaccen me musu installing CCTV. Mules din qafarsa ya maida,sannan ya ciri napkin guda daya yana goge dan abinda ya bata masa hannu kafin yace da ameh. "At night.....ka dafa paw paw leaves ka ajiyemin da duminsa.....daga yau inaso ya zama first drink dina for morning". Kai ameh ya jinjina cikin girmamawa "As you wish sir". Sai ya sauka a nutse amma hankalinsa yana dan kan qofar kadan,yanason sake tabbatarwa komawa tayi ta fasa shigowa saboda yana wajen?. Murmushi ameh yayi yana binsa da kallo,sosai boss dinsa yake burgeshi,yayi aiki kafin wajensa gidajen manyan attajirai da dama,amma baiga mutum me kiyaye lafiyarsa da yasan sirrin abinci ba irin boss din nasa ba. Yasan duk wani abu da zai gyara lafiyarsa a matsayinsa na namiji,yasan duk wani abu da zai gyara masa lafiyar ido da fatarsa,hakanan yasan duk wani abu da yake natural anti aging remedies kala kala. Ire iren abubuwan da shi yake tanadarwa manyan da yayi aiki a qarqashinsu don inganta lafiyarsu da gina garkuwar jikinsu suke qin ci ko sha don ba dadi a baki ko basusan muhimmancinsa ba......sai gashi shi kullum ne sai an tanadar masa da wannan abun morning and evening. Akwai hadin salad daya dinga mamaki sanda yaga yana cinsa farkon xuwansa,musamman da yake yasan yadda yake inganta qarfi da lafiyar d'a namiji,da yawan wasu abubuwan ma shike qaruwa dashi a wajensa. Baya son maggi da yawa a abinci,kaman yadda sanyi zaqi da kuma maiqo da abokansa bane sam sam (Mata da yawa suna complain din rashin lasting din mazansu a other room,sunsha magani sunsha maganin amma a banza,anata samun sabani da sauran masu matsaloli,to wallahi wallahi da yawansu maggi shine yake kashesu,inda kinsan yadda maggi yake kashe lafiyar mazajenmu da kinyi mugun gudunsa kuwa,kiga mace ta saka farin magi a abinci,tazo ta saka wadancan cubes din kala daban daban,ta hada drink ta laftawa miji sugar,ga uban sanyi,abinci mai yana kwanciya,ba ruwanki da manja ma sam sam,to billahillazi kunji na rantse muku haka zaita zame miki mace,kuma duk irin maganin da zaisha fa a banza,muddin ana kan cin magin nan,tashi daya ba zaki iya dainawa ba,amna gradually zaki dinga janyewa,idan goma kike sawa ki koma bakwai daga haka ki koma hudu,tabbas indai zaki dimanci haka zaki ga canji,ki ajiye farin maggi kwata kwata,zaqi da maiqo duka ki rage masa,hadin wancan salad din in sha Allah zan kawo muku shi a gaba,ya gwada cin na sati biyu bayan kin janye magin kiga ikon Allah,koda me gida yana da lafiya ma normal ne kina iya hada masa shi ya dinga ci,amma ina maimaita muku ku raba kanku da kayan d'an d'anon nan,Allah yasa mu dace). Kamar kowacce safiya muddin yana da isashen lokaci......ba baqi ba meeting na early morning da sauransu,zuwa duba lafiyar anni da gaida maamah din yana cikin schedule dinsa na kullum. A farfajiyar gidan kamar ko yaushe ya samu guard dinsa,kowa na tsaye akan aikinsa. Bai qaraso bama amma tuni Jordan ya buda masa bugatti dinsa yana jiran qarasowarsa. Cikin girmamawa da nuna kulawa suka gaidashi ya amsa yana bincikar lafiyar kowa kaman kowacce safiya,sai daya tabbatar da kowa lafiya sannan ya miqawa saddiq da kusan a makare yake isowa kayan hannunsa,wannan dalilin ya sanya baya samun shiga cikin gidan duk zuwan da yakeyi. Sun dauki hanya sosai kiran musaddiq ya shigo masa,ya fidda wayar yana connecting nata da Bluetooth dinsa yana amsa wayar. "Hamma na gama komai......sai yaushe zan dawo?" Musaddiq din ya amsa a karye da alama gida yakeson dawowar. "Ka dawo kayi me?" Ya tambayeshi yana jin tantama a dawowar tasa. "Hamma nayi missing anni......nayi missing saddiq". Iska kadan ya furzar daga bakinsa wadda ta fita da qamshin mint leaves saboda mouth fresh dinsa kenan na dindindin " Anni kuna waya haka saddiq.....kuma ko ita nasan bata da damuwa me yawa a tafiyarka.... Dude ne kawai nakeji ban kyauta masa ba dana dauke masa personal assistant......shima nasan ya fahimceni.....oops......anyways......nan da sati biyu zamu hade a madeena in sha Allah,it was family trip time". Har a muryarsa yaji dadi "Hamma na Manta da lissafinma.....okay..." "Hope komai naka ba matsala ko?,daga can zaka iya shiga koda Jeddah ne sai ka qaraso