Sashe 204
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ma ya lura macace me gyara sosai(idan kina da kyau ki qara da wanka,karki yadda ki zauna a wargaje waike jego kike ko kin tara yara sun miki yawa,xaki banu zaki lalace fes wallahi). "Sabrrrr.......don ni bani da gata?,don ni bani da wanda zan gayawa damuwata......don ni namiji ne bani da idon kuka?" Yafada da wata raunanniyar muryar data tilasta mata daga idanu ta dubeshi. Wani irin tausayinsa daya tsarga mata ya sanya hawaye taruwa a idanunta. Miqewa yayi,da alama baiso maganar ma tayi tsayi can. "Alqawari nayi,tun a wancan daren bazan taba koda yatsarki ba muddin zamanmu sai kina cikin yanayin". " Ina ciki wallahi" Ta furta da wani irin sauri bayan ta yiwa kanta kyakkyawar masauki a qirjinsa tana cukuikuyeshi. Dariya ta kusa kubce masa duk da yadda sanyin hawayenta daya sauka budadden qirjinsa da wuyan rigan ya zama V shape ya taba zuciyasa sosai. "I can't live without you.....You're my everything,without you,I'm lost,i need you now and forever,you're irreplaceable hamma........ka yafemin hamma.....bazan sake ba hamma......na tuba" Ta qarasa fadi tana sakin masa wani kukan kisisina me tsayawa a zuciya. Hannunsa har rawa yake sanda ya riqeta,ya sake mata wani tsatstsauran riqo yana sanyata tsakiyar qirjinsa yayi mata kyakkyawar runguma. Kasa magana yayi,kasa cewa komai yayi,kaman yadda shirunsa ya isheta amsa ta hanyar bugun da zuciyarsa takeyi. Ta yarda ta kuma amince tabbas taso ta zalunceshi,jikinta ya sake sanyi da kalar soyayyar da yakeyi mata. "Dukka wannan bugawar da Xuciyar nan takeyi tana yine saboda ke.....ke kadai sabreen,ban taba koda sha'awar daga kai na kalli wata macen ba bare har naji ta fusgi hankalina na ko ta dace da rayuwata ba bayanke". "Nayi maka alqawarin xame maka aljannar duniya koda shine xai kawo qarshen bugun zuciya dana numfashina" Lafaxinta na qarshe kenan daya iya tantancewa,ya dauketa cak ya ajiyeta inda yafi wayo sannan ya fara rabata da towel din jikinta. Wata irin sassanyan safiya ta bashi.....wata irin safiya me tsayawa a Xuciyar masoya..... "Can i have you for breakfast today?" Ya fada da wata narkakkiyar murya dake wani irin rawa. Yana dire tambayar ta tabbatar masa da abinda yake buri,abinda yake fata yake kuma tsananin buqata. Shi da ita kowannensu da zafinsa yazo,shi da itan gaba daya ba wanda bai gigita dan uwansa ba da wani irin zazzafan salo daya sake tabbatar masa itace DUNIYARSA shima shine DUNIYARTA. Gaba daya ta canza masa,ta kuma caza masa kwanya,yana jin tamkar yaune ranar farko a rayuwarsa daya fara kasancewa da ita. Ta gigita duk wani tunani nasa......ya sake fahimtar cewa lallai macen datasan kanta haihuwa ko shekaru basa saka kimarta zagwanyewa,a yanzunne ya sake gamsuwa da lallai sabreen dinshi ta zama cikakkiyar mace. Tana kwance luf saman qirjinsa sanda komai ya kammala,kalar alqawuran da yake zayyano mata ya sanyata sakin wani sassanyan kuka,nan ya sake lalacewa wajen lallashin kayarshi. Sanda taga lokaci bayan ta kalli agogo batasan sanda ta wantsalo daga gado ba ta nufi bandaki tana fadin "Su fawad" Miqewa yayi ya bita toilet din da towels dinsu. "Ina da nufina dana daukarwa su fawad nannies,kwanan nan kuma zan qara guda daya kowacce taji da guda daya,lokaci na lokaci na ne.....banaso nayi sharing nasa da kowa" Yaso ya bata dariya,saboda yadda yayi maganar da gaske. "Ayi musu afuwa naje na dubasu,don zuwa yanzun ya kamata ace an dubasun" Bai amsa mata ba ya turata cikin bathtub din kawai yana sake maqale mata. Tsaf ta shirya cikin atamfa riga da zani,shigar data jima bata yita ba. Shi kansa yau din saita masa kyau sosai,ta maqala wasu sabbin design na earrings na gold marasa nauyi a kunnenta da siriryar sarqarsu saman dogon wuyanta,abinda ya sake mata kyau kenan. Ido ya saka da baki yana kallon kyakkyawan dokin wuyanta,tunda aka fidda design din shi sai yau yaga kyansa saman wuyanta,ya tako a hankali ya sumbaci wuyanta nata,abinda ya dauke mata wuta na sakanni. "An bani izinin sauka na dubasu?". "An baki duniyata" Ya fada cikin kulawa da shauqin qauna. Basa dakinsu koda ta duba,don haka saita yanke duba parlor dinsu. "Salwa.....Allah yasa ba rigima suke miki b......" Bata samu daman qarasa fadin abinda yake bakinta ba komai ya maqale mata yadda ta zuba mata idanu itama haka ta zuba mata,cikin wani irin kallon me cike da matsanancin mamaki da gigita. Maamah ce zaune saman wheelchair dinta,an dora mata farouq fawwaz da almustapha fawad saman cinyar tata. Yatsanta cikin nasu yatsan tana tabawa a hankali,duk da bacci sukeyi amma idanunta yana kansu gaba daya. "Ba wata rigima hajiya......tun dazun suna hannun kakarsu,har sukayi bacci.......fauzan ne ma yaqi zama gashican an goyashi" Salwa ta bawa sabreen amsa. Maamah ce ta fara cire idanunta akan sabreen din sannan itama sabreen din ta dauke kallonta daga kanta cikin matuqar mamaki jikinta yayi wani mahaukacin sanyi. "Tun yaushe tazo?" Ta tambayi salwa da harshen larabci data tabbatar maamah bataji murya qasa qasa "Mintuna kusan arbain kenan,a rubutunta tambayeni ma haka kuke barin yaran a qasa gurinmu kuna sama?" Salwa ta fadi tana murmushi. Ta fada ne saboda yadda taga maamah din tana qarewa yaran kallo,kallon dake nuna zallar qauna da shauqi da kuma kulawa. Tunda tazo idanunta yana kansu,bata kuma saukesu ba ko sau daya. Kai sabreen ta jinjina,abun yana sake fadada mamakinta. "A samo mata abinci da abinsha" Ta fadi tana maida hankalinta kan maamah tana takawa cike da qwarin gwiwa. Ganin maamah a gidan nata ba abu bane me sauqi,ba wani abu bane da zatayi zaton zai kasance haka a nan kurkusa ba. Gabanta ta qarasa ta kuma tsugunna tana fadin "Sannu da zuwa maamah......barka rana,ya jikin?,Allah ya qara lafiya". Wani kallo ta dago ta dan watsa mata. Da tana da iko zata tambayeta ne uban me sukeyi a sama kusan sama da awa daya suka bar kula da yara hannun masu aiki?,haka sukeyi kenan cikin gidan?,shi ya ajiye fita office ita ta saki ragamar gida kamar su kadaine suka rage a duniyar?,kaman ba wani abu me rai da yake rayuwa a duniyar saisu?. Saidai ba wannan damar,sai dai kallon tuhumar data gabatar mata tana jin ya kawo mata dan sassauci a zuciyarta. Sarai taga kalar kallon,to amma ita kanta tasan yasha banban da kallon qiyayya da takeyi mata,wannan din akwai sassauci qwarai a cikinsa,duk da cewa akwai alamu na jin haushi a cikinsa da batasan haushin meye ba?,sai daga baya zuciyarta ke raya mata na barin yaranne a hannunsu salwa?. Saida salwa ta kawo komai sabreen ta jera mata a gabanta,sannan ta umarceta ta karbi yaran ta bata abincin taci,amma qememe taqi bayar da yaran. Sanda fu'ad ya sauko ana wannan drama din,don sabreen ta haqura ta koma gefe tana kallon ikon Allah,yadda ta tattara dukka hankalinta akan yaran,kamar bata da wani sauran abu me muhimmanci a duniyarta sama dasu,duk kuwa da cewa ita din daga wannan kallon guda biyu bata sake samun wani kallon ba. Shima nasa kallon aka aje masa,sannan ta kauda kanta bakinta yana motsawa kaman meson yin magana amma kuma ba dama. Mutuwar tsayen da yayi yafi na sabreen,don har sai da maamah din ta sake daga idanu ta kalleshi tana masa nuni da ya zauna ya tsaya mata a kai. Kaman yadda sabreen tayi mata shima still hakan,saidai shi dinma ba wani muhimmanci ta bashi ba. Ganinta riqe da yaransu kuma gudan jininsu cikin hannuwanta da wata qauna data gaza boyuwa daga cikin qwayar idanunta yafi komai yi musu dadi shida sabreen din. Suna zaune zaman kurame kawai,amma lokaci lokaci suna satar kallon juna shida sabreen din,har zuwa sanda tayi alama da hannu aka bata abun rubutu. "Ka kiramin driver ya maidani gida,kada ku sake barin yara har tsahon sama da awa a hannun masu aiki ba tare da kuna zagayosu kuna dubasu ba" Iya abinda ta rubuta kenan da rarrababben rubutunta. Ya dauka idanunsa ne suke masa gizo ko suke nuna masa ba daidai ba,sai kawai ya miqawa sabreen din paper ya qarasa ya karbi yaran ya ajiyesu sannan ya tura wheelchair din da take kai da kansa. Sanda yake turata da kansa sai taji wani abu yana sauka saman zuciyarta,tana iya qididdige takunsa da kuma yadda yake tura kujeran cike da karsashi,sai takejin kaman ba'a taba tafiya da ita saman wheelchair din irin haka ba. Koda suka isa key ya karba hannun driver din,yace su biyoshi a daya motar. Shi yayi driving nata har gida,ya kuma danganata da bedroom dinta. Tsugunnawa yayi a gabanta a hankali,yana jin wani abu me kama da qaqqarfan farinciki yana dawainiya dashi. "Zan koma......ba wani abun?" Kai ta girgiza masa alamun ba komai,sai ya miqe a nutse yana furta. "Sai da safe,Allah ya huta gajiya" Ya fada yana dan rage Ac din dakin. Idanunta ta lumshe,wasu hawaye masu dumi suna silmiyo mata wanda ba nace ga dalili ba,ta miqa hannunta da qyar dake yawan yo mata nauyi tana goge hawayen fuskarta. Riqe da paper din kuma a inda ya barta ya sameta a zaune tsakanin yaqini da kokwanto. Cak ya dagata yana juyi da ita sannan ya direta yana duban tsakiyar idanunta. "Na gode sosai duniya.....na gode da tayani siyawa yaran nan soyayyar maamah......koda ni ko ke mun rasa soyayyarta.......soyayyar da zata bawa su fauzan ta ishemu". Da mamaki take kallonsa,sai ya lakace mata hanci. " Ko an gaya miki bana sane da boyayyar addu'ar da kikewa iyalinki.....ni number one,addu'ar kariya samun nasara da cikakkiyar lafiya,yaranmu shiriya da zama nagartattu.....sai samun qauna daga wajen kakarsu" Kunya ta kamata,ashe dukka kukenta da fatanta cikin sallolinta na dare fakare yakeyi mata?.