Sashe 2
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Hustle until you no longer need to introduce yourself,push your self because no one else is going to do it for you". Kalamansa na qarshe kenan da tarin mayan attajiran da sukayi meeting na qarshe dasu wanda keson saka share dinsu cikin sabon kamfanin da kwanaki bakwai suka rage masa ya budeshi. Kalamai ne da suka dauki hankulan mutanen dake wajen,wanda dasu aka kammala zaman. Sanda yake sallama dash fiye da rabin hankalinsa yana kan wayarsa da tun dazun ya lura tana haske. Sai da gurin ya rage saura shi daya da hudu daga cikin guard dinsa da wannan karon dasu yayi tafiyar wadanda ke nesa da inda yake,ya miqa hannu a nutse yana jawo wayar gami da fesar da iska me dumi daga bakinsa. Cikin kowanne motsi yana jin farinciki na yadda al'amuran bude kamfanin ke gudana da dukkan wani haske qyalli da kuma alamu na nasara,bai taba qwallafa rai akan wani abu kaman haka ba,baisan me yasa dukka tunaninsa da hankalinsa suka raja'a wajen son ganin cikar wannan mafarkin nasa ba. Tunda yazo samu cikakken zama na awa biyu cur ba,saidai idan dare yayi ya wafci wasu awanni ya tilastawa kansa kwanciya ya huta. Kowanne minti idan ya shude da amfaninsa a wajensa,ko baya din dama shi mutum ne me girmama lokaci tare da bashi muhimmanci qwarai. Sunan farouq kawai daya gani ya sakashi gyara zama yana furta "Ya salam" Qasa qasa fuskarsa nason fidda wannan sihirtaccen murmushin nasa da ba kasafai ake samun dacen ganinsa ba. Wani sirri ne kwance cikin murmushinsa dake qara masa haiba da kwarjini da fitar asalin kyan da ubangiji ya huwace masa. Yasan zayasha qorafi ne kawai wajen farouq din......don yace masa zai kirashi har baisan adadi ba......hakanan bazai ma iya tuna awar qarshe da sukayi waya ba. "Hala baka da wani abu me muhimmanci cikin rayuwarka sama da business dinka?" Kalmar da farouq ya fara jera masa kenan. Boyayyen murmushi ya saki yana daga dogayen qafafunsa ya aza saman dunqulallen table din gabansa me azabar kyau. Wani irin shaquwa da fahimtar juna ce tsakaninsu dake sanyasu iya fahimtar mode din juna koda basa kallon fuskokin juna. Yasan zaiji fiye da haka ma a bakin farouq din,don muryarsa a dake take da alama har kan fuskarsa akwai alamu na qosawa "Idan ka cire ku family na.......tabbas ba abinda ya fishi muhimmanci cikin duka kaf rayuwata". "Aurenka da yarinyar su a wanne muhalli ka sakasu?....." Ya sake masa tambayar kansa tsaye cikin salo na kaiwa maqura da son masa titsiye. "Aure?....yarinya?" Ya maimaita maganar har ga Allah cikin son neman qarin haske. "Eheeennn" Farouq ya fada a taqaice,cikin ransa yana jin rainin hankalin jadda yana neman fin qarfin tunaninsa muddin ya gaya masa ya manta da lamarin auren dake gabansa. "Mmtsewww......au" Fuad ya furta wani siririn murmushi yana sake qwace masa. Sai a yanzun kwanyar tayo masa tariyar karatun baya na abinda ya baro a nigeria. Kusan gaba daya sabgar ta shafe daga tunaninsa,abinda ya sanya a gaba ya mamaye tunanin komai daga kansa. "Am sorry......kasan halin......" "......halin mijin aljana.......zata sakashi ya aikata fiye da haka ma,saidai alhmdlh.....duk abinta a wannan karon munci qarfinta,kuma in sha Allah dan uwana bazai mutu babu aure ba". Dariya sosai ta qwace ma fu'ad din ganin yadda farouq din ke maganar very serious,abinda ya jima baiyi ba,ya rasa abinda yasa suka damu da auren nan......ya fuskanci gaba dayansu murna suke dashi.....ya karanci dukkaninsu sun daukeshi serious kuma da gaske suke lamuran baki daya.....ciki harda MAAMAH duk da akwai qatotuwar ayar tambaya a kanta......don ya sani,koda yaushe ita ungulu bata jewar banza. "Ka duba email dinka na sauke maka saqo......ka duba urgently" "Alright" Ya amsa masa suna katse wayar dukansu. Yasan tsaf xaya iya mancewa idan bai duba saqon yanzu ba kaman yadda farouq ya buqata. Don haka kanshi tsaye ya bude email dinsa. Baibi takan sabbin saqonni da ya fahimta kaman akwaisu ba,kanshi tsaye ya bude saqon farouq din. Daya bayan daya yake bin hotunan daya turo da kallo ba don yana fahimta can can ba. Hotuna ne na style readymade na kayan maza masu azabar kyau da aji da wani fitaccen kamfanin fidda readymade suturu ke samarwa. Company ne da sanya suturar data fits daga cikinsa sai wane da wane......sai mutanen da suka amsa sunan shegu ne su ta fannin kudi da dukiya. A idanu kayan sunyi kyau,saidai shi baisan me zaiyi dasu ba,don haka ya jawo daya wayar tashi ba tare daya dauke dubansa daga kan hotunan kayan ba ya dannawa farouq din kira. "Am coming" Abinda yaji farouq din ya fara fadi kenan da alama yana magana da wasu ne daga gefe "Have you seen it?" Idanunsa ya lumshe kadan sannan ya budesu "Yes I have.....but bansan me zanyi dasu ba......hala ka fara preparation na bude garment company ne?". Wani qululun takaici ya tsayewa farouq a wuya,seriously mutumin nan da gasken gaske yake ya fara mantawa da cewa aure zaiyi. Duka ya sakar masa ragamar komai a hannunsa ba tare da damuwa ko tambayar ya ake ciki ba ko meke faruwa ba. "Na rantse da Allah sa'arka daya baka kusa dani......shin wai ka manta yarinyar mutane da zaka aura wadda ka kaiwa sadaki?,in all likelihood ka samu memory formation right?" . Wannan karon ma saida sautin dariyarsa ya isa har kunnen farouq ''Calmdown mana dude......abun yayi zafi ne har haka?" "Yama fi haka zafi" Ya fada yana jin ya tuqewa halin fu'ad din. "To am sorry......amma dai ka sani......ina da abubuwa masu muhimmanci da yawa a gabana.....kai din kuma wakili nane a ko ina......duk abinda ya dace ka zartar ka zartar....na baka wuqa da nama" Ya fada calmly,don bayason ya sake tunzura farouq din,tunda yana ganin yana iya bakin qoqarinsa a abinda shi a nasa ganin baikai muhimmanci da suke bashi ba. Dan shurun da farouq din yayi da yadda ya sauke numfashi ya tabbatar masa fushinsa ya sauka,dama ko can basa wani dogon fushi da juna,da farouq ya zazzage abinda ke cikinsa shikenan,shine dama me yawan kauda kai.....zaka jima kana masa abu amma miskilancinsa bai bari ya nuna maka har kasan kana masa ba daidai ba,har sai sanda ya gama taraka tukunna. "Kayi magana dasu abdulghafar......for now ya kamata su sassauta tsaronsu akan yarinyar" "For what reason?" Fu'ad ya maida masa kanshi tsaye yana gyara zamansa sosai saman lallausar kujerar da yake zaune akai. "Ina ganin kaman ya kamata ta sake.....duk da dama dole ka bata security da guard,ko don yanayin halin tsaro da qasar ke ciki,sannan zuwa yanzu ta zama part of us......wanda duk xai d'amfara da sunanmu dole a bashi tsaro" "Forget about it farouq......she's gonna be able to do what you....." Sai kuma ya fasa qarasawa yana jan siririn tsaki. Shi sam sam koda sau daya bai taba jin wani abu da yayi kama da yarda ko gasgata yarinyar ba.....akwai abubuwa da yawa da uake suspecting a kanta,wanda ya sake qaruwa tun daga lokacin data bayyanar masa a mazaunin ZABIN MAAMAH. "Do you have concern about her actions?" Farouq ya tambayeshi yana tattara masa hankalinsa. "Manta kawai......mu ajiye wannan,baka tambayeni akan komai ba dude?". Yayi maganar calmly kaman zancan business din yafi bashi peace akan batun auren. "Akan komai?,akan business dinka?,wannan shine kadai damuwarka?" "Wani abu daban daya kamata na damu dashi sama da haka?". Numfashi sosai farouq yaja,yana tsoron yadda fu'ad gaba daya baya bawa harkar nan muhimmanci,yana tsoron faruwar wani abu......careless din yayi yawa har haka,yana jin kamar ya kashe wayar kawai,to amma ya sani wannan shine abu na qarshe da zaiwa fu'ad ya bata masa rai,ya tsani a kashe masa waya sam sam. Yadda yake masa bayanin nasarorin da sauran abinda ya rage ya sake bashi tabbacin business dinsa shine gaba da komai. Sunyi magana har ta kusan awa guda kafin su yanke sadarwar dake tsakaninsu. Sanda yake qoqarin minimizing email din idanunsa suka sauka kan wani sabon adreshin email din dake dauke da sabbin saqonni guda uku,kamar zai share ya wuce sai baiyi hakan ba,ya danna ya budeshi ya fara bin saqonni da kallo. Kallon farko zaka fahimci ya bada dukka hankalinsa akan abinda yake ganin gilmawarsa cikin wayar tasa. Saqonni ne kusan guda uku,kala daban daban,saidai kuma kowanne saqo daya yakeson isar masa. _mr muhammad jadda,You hereby warned to stop all activities related to lunching your company_ saqon farko kenan. A nutse ya sauke idonsa zuwa ga email na biyu _Not heeding this warning may put your personal and professional assets at risk_ . Sake matsawa yayi zuwa saqo na uku shima still dai kakkaifan jan kunne ne zalla a cikinsa. _Ignoring this warning may lead to financial losses and reputational damage_ still dai qasansa shima wani saqonne _Proceed with caution,as this may have unintended consequences_. Tsam yayi da ransa,yana sake bin saqonnin daki daki yana bitarsu. Wannan wanne irin barazana ce haka me girma?,daga wanne sashe ta bullo?,su waye keda alhakin aiwatar da hakan?. Ya jima da sani......ba sanin jiya ko kuma yau ba.....sana'arshi sana'a ce dake dauke da tarin hamayya gogayya da kuma abokan adawa na sarari dana boye,wani irin matsayi ne da Allah ya bashi wanda bai taba tunanin samuwarsa a qananun shekaru irin nashi ba. Akwai tarin mutanen da suka fishi jimawa cikin harkar.....saidai har yanzu basu samu irin nasibin daya samu ba. Gyara zamansa ya sakeyi da kyau yana furzar da iska daga bakinsa. Ya sani,zai iya bincike akan ainihin adreshin,saidai kuma yasan zai wahala ya iya reaching komai akai koda yaso samun haka. Beside ma,isn't the first time daya fara samun ire iren wadannan saqonnin,wanda daga qarshe yake cimma daga wanne waje suke?. Ba abinda ya taba girgizashi ko ya daga masa hankali kwata kwata,amma kuma hakanan yaji wannan saqon ya tsaye masa a rai. Bai sani ba.....ko don saqon yazo masa ne a daidai sanda yake da burin aiwatar da abinda ya qwallafawa ransa na cikar burinsa?. Yadda yake a tsaye a siffa da zati me taba zuciya,haka zuciyarsa take a tsaye. Ba komai ke bashi tsoro ko firgitashi ko sanyashi yaja baya akan abinda ya fuskanta ya kuma qudira zai aiwatar ba.....don haka wannan saqon ma sai ya sanyashi cikin sahun sauran saqonni marasa muhimmanci,wadanda ba komai bane a ciki face zallar barazana maras muhimmanci a wajensa. "Hasbiyallahu wa ni'imal wakil,hasbiyallahu la'ilaha illahuwa alaihi tawakkaltu wa huwa