← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 196 OF 215

Sashe 196

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ce taso kubce mata,amna ta danneta,saidai hakan ya nuna a muryarta. "To ai kawu abun na Allah ne,shi yake bada iya adadin da yakeso". " Eh amma ai yace ku roqeni zan amsa muku ko?,qarshen watannan zamu shiga qasa me tsarki,farouqu xai fara cika alqawarinsa.......zam zage nayita roqo miki.haihuwar haka haka din" Wannan karon saida tayi dariya sosai. "Kawu Allah ya bamu masu albarka wadanda zamu iya dasu". "Ke!,kana da wadata da arziqi irin na mijinki harka dinga tunanin kalar yaran da zaka iya dasu?,yo ko yawan taron arfa kika haifa masa ai yana da abinda zaiji dasu". Kai ta girgiza tana murmushi. "Kawu......tarbiyya ba'a nan take ba,kace ameen kawai" "To ameen sarkin tsari......nace ba?" Ya fada yana komawa serious. "Ina jinka kawu" "Ina iya tahowa zaman dab'aro?". Idanu sosai sabreen ta bude dariya tana son qwace mata. "Kawu kaifa kawuna ne,kuma namiji ne kai,ai mata suke zaman dab'aro,inama laifin ace inna A'i?(matarsa)". "Ke komai yanzu a zamanance akeyinsa,ta yaya zan turo A'i gani?,bayan ba abinda bazan iyayi miki ba?,ni damuwata na kula da d'iyar ahmadu,na rama halascin da ya yiwa rayuwata" Ta fuskanci da gaske kawu yake,saita gyara muryarta. "Kawu kada ka damu,mun dauko masu kula da yaran musamman,sannan kuma ga masu aikin gidan na ainihi". "Duk da haka ba za'a barki haka ba,xan aiko A'in ta zauna miki kona kwana arba'inne na al'ada" "To kawu Allah ya saka da alkhairi ya qara zumunci" Ta fada tana jin dadi qasam ranta. Ko ba komai zata ce ga wani daga dangin mahaifinta,duk da zuwa yanzu 'yan uwa ne kowa keta kutsowa da b'arkowa don nuna kulawarsa da bajintarsa akan haihuwar,tun suna madeena ma kafin sukai ga dawowa. Wayar ta sauke tana murmushi sanda take tuno baya,drama dinsu da kawu wadda kusan kullum sai an yita,rayuwa kenan.....komai yayi farko said qarshe,kuma dukkan tsanani yana tare da sauqi tabbas. Farouq yayi bacci,saita ajiyeshi kusa da dan uwansa hamza,ta miqe ta soma shiryawa,tana yi tana duban fuskokinsu. Ita kadai murmushi yana subuce mata,tana jin qaunar yaran har a cikin jininta. Duk sanda ta kallesu su ukun a jere reras saita samu kanta cikin mamakin yanzu wadannan din daga jikinta suka fito?,yanxu wadannan din 'ya'yanta ne?,mallakinta ne?,yanzu wadannan din jininta ne?,jinin muhammad fu'ad ne?. Sanda ya shigo tsaiwa kawai yayi yana qare mata kallo,tayi wannan sa ssanyan kyau cikin shigar atamfar data yafawa mayafi onion color. Sautin sauke ajiyar zuciyarsa shi ya dawo da hankalinta,tadan juya ido a shagwabe "Ka tsoratani hamma.....ka iya sanda ka tsaya kayita qaren kallo.....so kake kyauna ya qare?". Bai amsa mata ba har sai daya iso inda take,ya rungumeta ta baya sassanyan turarukansu suna gauraya waje daya. "Bakisan kina sake qara shekaru kina sake qara kyau a waje na ba?,tsarki ya tabbata ga ubangijin daya qagi wannan halittar ya kuma mallakamin ita a matsayin halaliyata......kuma uwar 'ya'yana" Luf tayi itama a jikinsa,tana jin yadda soyayyarsa take hudata tako ina. Mota uku kawai tayi musu rakiya zuwa gidan maamah din,wadda tun a bakin gate masu da guards na gidan suka taso,kowa barka yakeyi masa da nuna farincikinsa. Shi ya dauki farouq da hamza,ita kuma abba ne a hannunta wato almustapha. Yana gaba yayi sallama tana biye dashi. Mutum daya suka samu a parlor din wato saratu,ta miqe tana musu sannu da zuwa,ta kuma karbi yaro guda daga hannun fu'ad din tana musu barka da addu'o'i sosai. "Yanzu muka kai hajiya ciki,munga kaman ta gaji da zaman bacci takeso tayi" "Har yanzu ba batun magana?". Kai saratu ta girgiza cikin jimami. "Ba abinda ya canza har yanzu" Shuru kadan yayi yana juya al'amarin,a irin kulawar da take samu physically and mentally yaci ace an samu ci gaba sosai,amma yana mamakin yadda komai yaqi canzawa koda qanqani kuwa. Daga saman gadon da take zaune jingine da fuskar gadon ta daga idanunta sanda suke sallama cikin dakin. Idanunta ta zube fes a kansu kowanne dauke da yaro guda. Saratu ce ta fara isa gefanta ta aje hamza tana juyawa ta fice a dakin. Da wani irin kallo taci gaba da binsu ba tare data dora idanunta akan yaran ba da takejin ba zata iya kalla ba,zuciyarta ta fara zafi tana jin gumi yana fara keto mata. Kaman hadin baki suka isa gabanta a tare,fu'ad ya ajiye mata farouq a gabanta,ya karbi almustapha ya ajiyeshi shima kusa da farouq,ya dawo da hamza kusa da yan uwansa still idanunta akan fu'ad din yake. Yatsarsa ya sanya ya nuna hamza. "Ga hamza......wanda ya zamemin tsanin zama muhammad jadda din da ake kirana dashi a yanzu,hamzan daya bani dakin kwana......ya bani sabuwar rayuwa,ya bani sabon ahalin da zan rayu dasu,na kuma kallesu a mazaunin nawa,ya kashemin kudinsa,yayi amfani da lafiyarsa don sama mana abinda zamu rayu dashi cikin aminci.......ga farouq,wanda ta sanadinsa nakai ga hamzan daya zama qashin bayan ilimina da tarbiyyata gaba daya........ga kuma abbana..." Ya nuna almustapha yana tsagaitawa wanda da alama wani abun ya hadiye. "Abbana.....sanadi na......abbana da bani da wani abban daya haifeni wanda zai sake maimaituwa irinsa sak" Yana kaiwa nan ya miqe,ya damqi hannun Sabreen "Gasunan maamah.......gasunan ki kallesu,kiga waye bakiso a ciki?,waye yayi miki wani laifi na rashin kyautawa?.....ki.kallesu jikokinki ne......yaran da suka fito daga tsatson fu'ad.....dan da kika dauki cikinsa wata tara,d'an da kikayi naqudarsa tsakanin mutuwa da rayuwa" Yana kaiwa nan ya fara jan sabreen din suna fita a dakin. Bugawa kawai zuciyar sabreen takeyi,don tace akai mata yaran ba hakan yana nufin su fita a dakin subar mata su ba,zuciyarta ta kasa nutsuwa ko amincewa da hakan "Hamma......" "Shshshsh" Kawai yace da ita da qarfi. "Hamma yara na....." Ta sake fadi a gigice wanda sautin da reaction din yakai kunnen maamah dake zaune a dakin. Suna fita a dakin ya kama kafadunta dukka biyun ya riqeta da qarfin gaske. "Relax sabreen.....ba abinda zai faru......ba zata iyayi musu komai ba......inason zamansu a dakin ya wanke duk wani daci da tsanarsu da zata iya ji a nan gaba......ban isa na sanya ta soki ba kota soni......amma definitely!.....dole!......dole taso wadannan yaran" Qwarin gwiwar da take gani tsakiyar idanunsa shine ya bata relief,ta bishi xuwa falon suka zauna. Tana iya jin zaman yaran kusa da ita har cikin jikinta,tana iya jin wanzuwarsu sosai a tattare da ita,saidai kuma ta gaza daga idanunta ta kallesu. Zafi takeji a ranta,zafin sabreen sosai takeji,tana ganin kamar itace silar komai da komai. Sun dauki mintuna masu yawa a haka,iyayen basu dawo sun daukesu ba,abinda ya dinga bata mamaki kenan. Me yasa suka iya dauke idanunsu akan yaran?,me yasa suka iya bar mata su suka fice abinsu?. Motsin da hamza ya fara yi shine ya fusgi hankalinta ba tare data sani ba takai dubanta kansu. "Subhanallahi" Ta fadi a ranta tana mamakin zallar kamannin dake fuskar yaran. Kamannin da suka tuna mata da fu'ad din sanda yake tsumman goyo kaman haka. Idanu ta zuba masa shi kuma yana ci gaba da motsinsa,a hankali har ya fara qushin qushin din kuka,abinda kuma ya tashi sauran 'yan uwansa kenan. Mutsu mutsu suka fara yi su duka ukun,kafin kuma a hankali su kece da kuka. Hannun fu'ad ta riqe da kyau tana ji kaman ana matsa zuciyarta sanda sautin kukan nasu ya isa ga kunnuwanta. Jikinta duka ya dauki rawa,ta daga idanu tana kallon fu'ad. Qin kallonta yayi,kuma kaman ta fahimci yana sane yaqi kallon nata,sai kawai ta sadda kanta qasa tana sake jin yadda zuciyarta ke tsananin bugawa. Cika mata kunne sosai kukan nasu yayi. "Ya isa....kuyi shuru" Ta fadi tana jin ciwon yadda furucinta baya fita a sanda ta yishi,saidai kuma ga mamakinta sai almustapha ya fara rage sautin kukansa,a hankali dukkaninsu suka rage kukan kafin kuma suyi shuru. Mamaki taji ya kamata,ta sake xuba musu idanu wanda kaman sunsan da hakan sai hamza ya soma bude idanunsa. Tarwai qwayar idanunsa,kai ba zakace jariri bane dan sati biyu kacal,tana waiwayawa ga sauran suma duk idanunsu sun bude,kuma ita suke kallo. Batasan me yasa ba ta samu qaramin murmushi ya subuce daga fuskarta,ta samu kanta da yunqurin miqa hannunta ta kamo hannun koda d'ayane a cikinsu. Cikin wani irin ba zata da mamaki sai ga hannunta ya motsa,ta maida dubanta ga hannun,ta sake gwada dagashi xuwa gaba,ga tarin mamakinta sai hannunnata ya isa ga almustapha ta riqe yatsunsa hannun nata yana wani irin kakkarwa. Wani abu da batasan meye ba ya soma ratsa zuciyarta,hawayen da batasan daga ina suke ba suka tsinke mata. Wacce irin baiwa ko hukuncin Allah ne tattare da yaran?,abinda ta dinga maimaitawa kanta da nacewa da tambaya kenan idanunta akan fuskokinsu dukka su ukun. Sun zame mata waraka daga wani bangaren ciwon ta kenan?. Tambayar da tana ajiyeta fu'ad ya murza qofar ya shigo a hankali shidaya,don gaba daya sabreen ta gaza miqewa bare tayi jarumtar biyoshi,kawai zuciyarta tana gaya mata shikenan,shurunsu wani abun ne maras kyau ya samesu. Hannun nata yabi da kallo yana mamaki shima wanda har yanxu yana cikin yatsun almustapha,ya qarasa gabanta ya tsugunna yana duban hannun yana kuma duban yaran. "Hannunki ya motsa yau?" Ya tambayeta,saita gyada kai a hankali hawaye yana silmiyo mata daga idanunta. Qasa yayi da kansa yana tasbihi ga Allah,sun jima a haka sannan ya fiddo wayarsa. "Ubangiji ya tabbatar da lafiya" Ya fadi a taqaice yana kiran sabreen zuciyarsa ta nauyaya da girman zatin Allah. Tana kallo suna ficewa da yaran a dakin,sai ta samu kanta da gaza dauke idanunta a kansu har suka kammala ficewa. Tafi qarfin awanni uku bacci bai dauketa ba,tana jin kamar dakin nata ya koma kango bayan fitar tasu,kamar ba wani abu daya rage a dakin sai ita kadai. Abun mamakin shine,kwana tayi tana mafarkin yaran,cikin mafarkanta na daren gaba daya sune kewaye da ita,harda wanda suke magana da ita,saidai ta kasa bambance me suke fadi. Ajiyar zuciya kawai ta dinga saukewa sabreen din tana tariyo abinda fu'ad ya gaya mata na yadda ya shiga ya samu maamah din. "Ya Allah.....ka jefa matsananciyar soyayyarsu a zuciyarta ninkin ba ninkin yadda ta tsani mahaifiyarsu" Ta samu kanta da wannan addu'ar. *_NAMING CEREMONY_* Katafaren kuma qawataccen guri ne na alfarma,aka aka shirya sannan aka tsarashi musamman saboda gabatar da radin sunan. Komai na gurin kusan fari ne,farin ma irin qal dinnan me daukan hankali da kuma daukan idanu. Tun daga farkon shiga gurin har zuwa ciki wasu irin manyan hotunan ne
Chapter 196 · 0% Book details