Sashe 125
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*MAAMAH* Kaman wadda bata da aikinyi haka ta dinga bin diddigin shudewar kowanne awa da minti na zamansu a gurin da delay din fu'ad na qarasowa gurin. Ba shakka banda idanunsu ameenatu a wajen ba abinda zai hanata komawa gefe tayi kuka koda na minti ashirinne,wataqila ta samu sassaucin abinda takeji cikin zuciyarta. Yau ita mariya ta wayi gari karyar farautarta ta farauto abinda take da muradi ta sakashi a gaba tana wasa dashi yadda taga dama?. Yau ita mariya ita ke zaune tana jiran dakon isowar yaronta?,wata macen bariki ta riqeshi tsahon wasu kwanaki?,a yau da take jiran qarasowarsa kuma sai time din da taga daman ganinsa kowa zai ganshi?,ita kuwa idan batayi taba rayuwar mutanen nan biyu ba ai tayi asarar zuwanta duniya. Guda gudan baqinciki haka ta dinga hadiyarsa tana korawa da yawun bakinta,tana sake tsarawa da shirya yadda zata gigita rayuwarsu duka su biyun idan sun sauka Nigeria. Tana jin kamar idan ta jira su koma ya mata nisa,don haka ta koma gefe ta zaro wayarta tana duba wata number tana jin gwara ta shirya komai tun yanzu,ta yadda komai din zai fara da wuruwuri. Sauran ma'aikatanta dake hannun yanzu haka dukansu bata da wata damuwa a kansu,tasan akwai babban aiki a kansu daba wanda ya isa ya furta sunanta da sunan toxarci ko tona asiri. Tana qoqarin kira wani kiran ya shigo. Matsanancin mamaki ya kamata ganin sunan fareeda yana yawo saman screen din,bata tsaya jinkiri ba ta daga wayar tana kiran sunanta. "Na'am....ya kike?" Tayi namijin qoqarin tausar kanta ta karya harshenta ta tambayeta. "Ina kika shiga fareeda?,bayan kinsan babban aiki muka tunkara?" Sake hadiye wata guduma da taxo kan harshenta tayi,tasani cewa banda tana tausar kanta ta samu isa ga dalilin kiran da tuni ta jima da daddannawa mariya zagi. "Kowanne aiki ma yazo qarshe......kowacce magana anzo qarshenta......kowanne al'amari dadinsa da wuyarsa sun qare..... Kedai kawai turamin date din da zaku iso Nigeria,da airport da zaku sauka,kano ko Lagos ko abuja". Daga kai tayi tana duban musaddiq dake nesa kadan da ita. "Musaddiq" Ta kirashi tana sauke wayar,waiwayowa yayi sannan ya fara takawa a hankali har ya iso gabanta,a tsume ta danna kan number ta miqa masa wayar. "Kayi confirming na date din komawarmu da airport din da zamu sauka ka rubutamin a nan ka tura". Wayar ya karba yana kalla,number ba suna,hakan yadan saka shakka cikin ransa,amma ta wani sashen kuma daya tuna kalmar UWA UWA CE sai ya rubuta kaman yadda tace din,ya tura bayan ya gama kalle numbers din tsaf sannan ya miqa mata yana barin wajen. Details din daya rubuta take kalla "Me fareeda zatayi dashi?" Taji tambayar ta tsargo mata. Cak ta tsaya tana son laluba amsar amma kuma saita kasa. Wani sashe na zuciyarta sai taji yadan shiga fargaba kadan,sai kuma daya sashen ya taso ya danneshi yana gaya mata. "Fareeda masoyiya ce....wataqila akwai mafitar data samo mana,zatayi abinda ni na kasa yi wataqila" (Ni kuwa nace ummm inji me ciwon haqori......ba girin girin ba tayi mai dai,maji ma gani wai an binne tsohuwa da ranta). Aje wannan tunanin tayi tana tureshi gefe,ta kashe wayar tana ajeta da zummar ci gaba da lissafin sai yaushe zata bar fu'ad din ya qaraso?,sai kuma idanunta sukayi mata kyakkyawan gani. A nutse suke takowa da wani irin qyallin da idan ka kirashi na amarci bakayi laifi ko kuskurr ba. Kanta yana aje saman kafadarsa wanda tayi hakanne bisa dole saboda jiri jiri data fara ji. Da farko taqi ganin zasu shiga jama'a ne,amma daga baya dole ta kwanta din saboda indai batayi hakan ba tana iya faduwa ko ya dagata ya dauketa in ya tabbatar hakan zata faru. Tsakiyar qirjinta kuma wani abune ya dunqule mata,tana jin kaman amai ne yake taruwar mata,saidai bata gasgata hakan ba ganin lafiya qalau take ai,bataci wani abu daya bata mata ciki ba bare tace. "Na shiga uku......la haula wala quwwata" Maamah ta fada tana jin yanayinta yana hautsinewa gaba daya....... "Anya.....anya.....anya?" Ta dinga maimaitawa cikin zuciyarta tana tsoron furta abinda ke cikin zuciyarta. "KINYI KUSKUREN ZABOTA" Maganar bokan ta sake maimaita kanta cikin kwanyarta. "Bazai faru ba.....saidai ita tayi danasani" Ta fada tana furxar da iske me qarfi daga hunhunta zuwa bakinta. _uhmmmmmmmmm_ *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ 108 Idanunta ta dan lumshe kana ta budesu,tana iya hangen maamah dake farko,farouq daga gefanta kadan yanata amsa waya,anni daga can gaba ita amna. Musaddiq da saddiq ne bata hango ba,ko kuma yadda amai din yaketa faman mata kai kawo tsakanin cikinta da maqogorone ya hanata ganinsu oho "Amai nakeji" Ta fada qasa qasa kanta a kafadarsa,don ta tabbatar zai iya kufce mata tsaf kafin sukai wajensu. Hannunsa yasa ya riqe hannayenta sosai,kafin ya sake riqe tafin hannunta da kyau yana cewa "Ga can hanyar washroom,zaki iya qarasawa?" Ya tambaya a tausashe. Kai ta jinjina masa "Oya.....be fast" Ya fada yana mata riqon da zataji dadin tafiyan da kyau,duk da ba haka ranshi yaso ba,yaso ace ta bari ya rage mata wahalar tafiyar kawai. Murmurshi farouq ya saki,daga inda yake yana kallonsu,duk kuma da bayajin abinda suke fadi amma yadda yake kaffa kaffa da ita ya tabbatar masa dude dinsa ya qarasa zarewa......hauka tuburan na soyayya yasan ya sameshi,baisan kuma ya za'a qare da lamarin kula da gold da diamond ba,lokaci yayi na daukan sabbin ma'aikata kenan amintattu na kusa kusa dasu. Ta bangaren maamah kuwa ta shaqa iya shaqa,wannan karon kasa riqe ashar dinta tayi sai data furtata,ta furzar da iska tana dan dukan gefanta. Ta yadda duk macen data taba bariki.masifa ce,abune a jininsu da komai dadewa sai an saida hali. A nata tunanin sabreen tana sane tayi hakan,tunda ta ganta,tayi ne kawai don kada su hadu da fu'ad din kai tsaye,tayi ne kawai don ta nesantata dashi,daga qarshe kuma tayi ne kawai don ta gwada mata tata iyakar. "Zakiga taki iyakar a sanda kika qare a gidan tabbabbu mahaukata" Ta fadi a fusace tana qoqarin danne abinda takeji. Tanajin kaman ta saka hannu aka ta fasa ihu,tana jin kaman yanzu yanzu ta bude ido taga babu sabreen an shafe babinta daga tarihin rayuwarsu.....akwai lokaci abinda zuciyarta keta nanata mata kenan. Ta yarda da hakan,to amma shi lokacin yaushe xaixo?,amsar tambayar da bata santa ba kenan. A nutse ya koma baya yana qare mata kallo bayan ta gama aman tana wanke kyakkyawar fuskarta da take wani fresh da ita. Ta kammala ta gyara hijab dinta sannan ta juyo,saidai ba zato ba tsammani ta sameshi tsaye yana qare mata kallo kamar yau ya fara ganinta. Qaramar harara ta watsa masa da fararen idanunta,sai ya daga hannayensa sama alamun surrender sannan ya hade tafukan hannayensa alamun ban haquri kafin ya sauke yace. "Kinci wani abune da yake baki reaction?" Ya tambaya da yanayi na seriousness. Dan shuru tayi tanason tunawa,saidai kuma iya saninta ba wani abu da taci din. Kai ta girgixa masa tana tsane hannunta da towel din daya miqo mata. Taku biyu yayi ya matso gabanta,ya cire hannunsa a hankali yana taba fuskarta kafin ya xare ya xurashi ta qasan hijabinta yana tattaba dogon wuyanta. Abinda ya dauke mata numfashinta kenan na wucin gadi,don bayan jin temperature na jikinta sai daya hada da tsokanota har sai da taja baya tana ture hannuwansa. Jirin da taji yasa ta tsaiwa tadan dafe kanta,kaman walqiya yakai gareta tana riqota jikinsa. "Idan bazai yiwu ba mu wuce Seychelles......ki qara hutawa a can saimu samesu......xatafi burgeki akan Maldives" Ya qarasa maganan cikin kulawa. Fararen idanunta ta sake watsa masa. A abinda take gani cikin idanunsa ba hutawa zai barta tayi ba,saidai ya qara mata lalura ne kawai. Batasan inane Seychelles ba.......iya Maldives ma ya suka qare ya kaita qasan ruwa?,ita kuma Seychelles ai qila cikin cikin kada(crocodile)xasuyi rayuwa. Ta fahimci a son ranshi kowa ya mutu a barsu su rayu su kadai. "Muna sake makara" Ta fadi a shagwabe kaman xata narke. Abunda yayi masifar qayatar dashi,har sai da yaja baya yana gwada yadda tayin. Dariya taso qwace mata amma tayi hanzarin kauda kanta,sai kawai ta dauki wayarta ta soma takawa zata tafi ta barshi. "Ganganci ma kenan" Ya fada yana zaburowa ya daidaita tafiyarshi da tata. Wannan karon farouq suka fara taraswa,suns hada ido da farouq din dai ya wani basar,yana dauko wannan tsohon dabi'an nasa na miskilanci wa mutane ya azawa fuskarsa. "To waye ya damu dakai?" Farouq ya fada yana jifansa da harara,ya maida kallonsa ga sabreen da kunya ta fara mata qawanya. Tanaso ta zame hannunta ne daga nashi amma yaqi bata damar hakan "Madam barka da zuwa......inajin xamu iya wucewa ayi miki screening,minti arbain ya rage lokacin tashin yayi dama" Farouq ya fada a girmame. "Izinin wa ka nema da xaka kama yiwa mutane magana da mata?,if kana da wani important issue da kakeso lallai kayi magana da ita a kai ba gani ba?,dani zaka fara magana na nema maka izini ai ko?" Fu'ad ya fada sounding seriously. Dariya ta kama farouq sosai,yaja da baya ya kama kabbara kafin yace "Dole ne kam,dole ne na nema izini ai.....don ko bugeni kayi na fadi ai ba'a shari'a da wanda ba cikin hayyacinsa yake ba......madam kiyi haquri kinji......wannan zama dashi sai me haquri". " Na rantse harda Allah farouq kana qarawa kanka da kanka kwanakin bikinka ne" Fu'ad ya fada da gaske gaske,abinda ya sanya farouq ya fara shiga taitayinsa kenan. Yasan halinsa,idan har yace abu yasan ta yadda zai maida abunnan yadda yace din,shi kuwa wannan ruwan madarar soyayyar da yaga ana aiwatarwa shi a haramta masa wanzuwar tasa ai anyoshi......gwara yaje ya dandana shima kam. "Nif bance komai ba.....daga welcoming naku?.....madam ki qarasa ciki" "Ba ruwanka......banason kana min magana da mata fa,kana takurata,banaso kana sata magana.....she's sick". "Sick?" Farouq ya tambaya,daidai sannan taji xamanta tsakanin drama din farouq da fu'ad ba nata bane,ta sabule hannunta ta qarfi ta soma yin gaba tana barinsu. "Dude......ba sake lahani kayi mata ba ko?,wallahi wannan karon anni ba zata barka ba". Harara ya wurga masa "Wai sa'anka ne ni farouq?" "Inafa.....mutumin da yaje inda ni banje ba?" Murmushi ya saki,yasan da gaske farouq ya damu dashi da lamarinsu ne gaba daya,kowacce tambaya yana yinta ne don tabbatar da lafiyar kowannensu. "Juts a fever" Ya maida masa a taqaice idanunsa suna