← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 215

Sashe 114

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

suka zama katangun dakin kaman zasu tsage ruwan ya shigo.....shi kuma saman nisan ruwan da suke ciki kawai ya isheta firgici. "Is alright......ki zauna a qasan,zan koma saman" Ya fada yana fara takawa. Ai batasan sanda ta hantsilo ta biyoshi a baya ba,ja yayi ya tsaya yana danne dariyarsa. "Eheennn" Ya fada yana dubanta da salon tambaya. Kasan masa magana tayi,sai qasa da tayi da kanta tana murza yatsunta,haka kawai yau takejin nauyinsa,ita magana ta Allah daga saman har qasan ba inda zata yarda ta zauna ita daya,gani take kaman zata rasa rayuwarta ne. To amma ta yaya zata gaya masa hakan?,fada masa hakan ma ai daidai yake da ce masa su rayu daki daya,idan kuwa zasu zauna daki daya kenan yana nufin suyi sharing komai?. "We can room mate?" Ya tambayeta a tausashe yana lalubar qwayar idanunta. Tambayan ta mata tsauri,a zahirin gaskiya a yanzun ba wata mafitan da tafi wannan,don dai ita ba zata bari ta zauna ita kadai ba......amma kuma t ana juya yadda hakan zai kasance. "Let's room together" Ya fada yana wucewa zuwa matakalun da zasu maidashi sama. Wannan karon sai da yayi da gasken gaske sannan ya hana dariyarsa fitowa,don duk inda ya aje qafarsa nan take jefawa,bata yarda ma ya koma saman ya barta a dakin can qasan ruwan ba. Tana tsaye ya dauki wani luggage me kyau da batasan sanda aka kawoshi ba da wani kwali na daban. "Ranar farko zai zama a dakin sama.....rana na biyu underwater nakeso nayi bacci......hakan yayi?" Ya fada yana daga gira daya gami d qarewa tsoronta kallo a fakaice. Kai kawai ta gyada don nata da wani sauran zabi,tsoron da takeji ma ya isheta. "Okay.....stay here.....zan duba wani abu zan dawo yanzu" Ya fada yana bata tabbaci da idanunsa. Kai ta daga masa,tana kallo ya bude qofan ya ratsa living room ya fice. A sanyaye ta sauke idanunta ga ruwan da take kallo gashi gata,wai a haka cikin daki kake kaman ka sanya hannu ka kamoshi. Kujerar da aka aje gaban qofar glass din ta matsa ta zauna tana sake ganin kusancinta da ruwan. "Subhana man kalaqal kalqa wa'ahsahum adad" Ta fada a ranta tana sake jin girman zatin Allah yana kamata. Ba shakka da yawanmu 'yan adam bamusan waye Allah ba,kawai muna fadinsa ne a bakunanmu ba tare da halasto girmansa a zukatanmu ba. Iya halittar ruwan ya ishi bayinsa sake sallamawa lamarinsa. Ta sauke numfashi tana maida kallonta cikin dakin,idanunta ya sauka kan littafin dake ajiye saman dan qaramin table din dake gabanta. Hannu ta miqa ta dauka,ta fara budewa,cikakken bayani ne akan gurin,taswirar dakin da suka kama inda toilet da restaurant da komai yake. Idanunta ya tsaya cak kan farashin wajen,adadin kudin da zaka biya duk kwana daya tal,dollar dubu hamsin kimanin million saba'in da wani abu. Idanu ta fidda waje mamaki yana kasheta,zuciyarta ta kasa gasgata farashin,ko a mafarkinta bata taba tunanin akwai me kudin da zai iya wannan ba daga qasarmu,amma sai take ganin kaman yayi yawa kudaden.....kaman yayi almubazzaranci,sai wani sashe na zuciyarta ke tuna mata hirar da amna ke yawan mata na hamma din. Tabbas ya isa ne yakai.....kudinsa kuma ya zarta yadda take kallonsa,mutumin dake sarrafa diamond da gold ya fitar qasashen qetare......gold ko diamond din kamfaninsa kaman abinci yake a wajensu saboda farinjininsa. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ 99 _Daga abdullahi dan mas'ud R A yace:manzan Allah S A W yace "BAZAI SHIGA ALJANNA BA,DUK WANDA AKWAI KWATANKWACIN KWAYAR ZARRA(MAFI QANQANTAR ABU) NA GIRMAN KAI A ZUCIYARSA_ _muslim ya rawaito_ Ajiyar zuciya ta sauke tana rufe littafin,yayin da a can qasan zuciyarta taji ta raina matsayinta,wacece ita da har zama zai hadasu da mutum me daraja irin muhammad jadda din?,mutumin da iya yau kawai tasan ya tserewa matakin rayuwa da ita.......ya mata nisa fau fau......ya kuma tsere mata irin da mugun nisan tazarar nan.. "Amma me yasa duk da wannan tarin matsayin nasa da zai iya auren kowanne nau'in mace a duniya.....duk da wannan dukiyar......kyau da ilimi dake gareshi ya nacewa rayuwarsa sai ni?,me yasa ya kasa rabuwa dani yaje yayi rayuwarsa?" Tambayoyin da suka zo kanta kenan. Ta kalli wayarta dake ajiye gefe,ada tana mamakin yawan kudin wayar,sai gashi a nan din kowacce rana zasu kashe kimanin kudin wayar a kwanan gurin kawai,banda personal cook da taga suna dashi da komai da komai da za'a zo kullum a maka personally. "Allah me iko" Ta fada bayan data kunna wayarta ta tadda WiFi da cikakken network na wayar,ta maida dubanta kan ruwan,kaman ba'a kan ruwa suke ba?. Daidai nan ya tura qofan ya sake shigowa,tadan zabura kadan saboda da gaske a tsorace take. Murmushi ya saki dan siriri daya qara masa wani kwarjini da kyau. "I'll safeguard you....indai kina tare da Jadda kisa a ranki baki da sauran tsoro ko damuwa" Ya fada a tausashe sanda yake qarasowa dakin da wani kyakkyawan tray a hannunsa ya ajiye saman table din gabanta. Haka kawai taji kalamansa suna samun matsugunni a zuciyarta,su huda suka fado mata......indai har hakan ya tabbata hakan na nufin qannenta zasu iya rayuwa da ita?,qannenta zasu samu kowanne kalan rayuwa da take mafarki?" Ta tambayi kanta idanunta zube kan price na wajen ba tare da tasan nan din ta bude ba. To amma meye tabbacin da take dashi a kansa?,kada fa ta rudi kanta........yanzun nan ta sake fahimtar wanne irin tarin dukiya da girman matsayi da yake dashi.......tasan cewa kwata kwata babu hadi tsakaninsu......zaren ba kalar yadin bane......bata da wani assurance. Baya kadan yaja a hankali,ya sauke gwiwoyinsa qasa yana tsugunnawa a gabanta,hannu ya sanya yana janye littafin yana sauke idanunsa a wajen,saita bishi da kallo haka kawai tanajin kaman yayi almubazzaranci......kaman ya kamata tace wani abu,kaman ya dace ta masa gyara. "Wannan.......gurin nan kaman yayi tsada da yawa......muna da wajen da zamu kwana fa?". A nutse ya daga idanun nasa yana ajesu a fuskarta,wani abu me kama da murmushi shimfide saman fuskartasa,har tsakiyar zuciyarsa yana jin dadin kusanta kanshi da ita,koda kuwa na qananun sakanni ne sai yaji yana samun nutsuwa. "Duk tsadarshi baikai ki tsada ba.......You're priceless,no cost is to high......I'd spend my last dime on you,you're worth every penny" Ya qarasa fadi yana duban idanunta......yanajin inama zata bashi dama ya shige jikinta.....ya dora kansa saman kafadarta?,ya sauke ajiyar zuciyar da zata kawo masa sassauci da irin yanayin da yakeji a zuciya da gangar jikinsa". Karon farko da itama ta zuba masa idanu......tanaso ta tabbatar da gaskiyar abinda ya fada ko kuma akasinta......tanaso ta tabbatar har zuciyarsa abinda ya fara ko wani sabon salon yaudarar ne?. Kasa jurar kallonsa tayi kama kullum,ta dauke kanta ta maida still saman ruwan,tana ganin yadda duhun dare ya cakudu da hasken fitilun da aka wadata duka resort din dashi,jifa jifa halittun kifaye nau'i daban daban suna kai kawo. Lissafin kudin take cikin ranta,inda zai rabawa marayu irinta wanne dadi zasuji,saita kasa shuru still,ta buda bakinta a hankali ba tare data kalleshi ba. "Inda zaka kaishi qasata.......akwai tarin marayu da marasa qarfi da zasu shiga cikin walwala da farinciki sanadin haka.....zasuyita sanya maka albarka.....mutane masu yawan gaske da suke kwana cikin yunwa da ciwo......suke kwana cikin halin babu.....'yammata da yawa sun rasa mutuncinsu sanadin talauci,iyaye da yawa sun rasa 'ya'yansu saboda abinda zasu sanya a bakinsu" Takai qarshen maganar wani abu yana taba ranta,wani abu yana taso mata yana tuna mata abinda ya wuce a baya. Sosai.....sosai da sosai maqurar gaske yaji tayi wani bala'in burgeshi......irin burgewar da ya jima baiji wani dan adam ya masa ita ba. A bangaren taimako idan ana maganarsa.....baisan adadin mutanen da suka dogara da rayuwarsa ba......baisan adadin mutanen da suke qarqashin kulawarsa ko kulawar wasu nashi ba,ba'a iya Nigeria kadai ba......bai bari tallafinsa ya tsaya a qasata ba kawai,ya leqa maqwaftan qasashe sosai,saidai kusan komai zaiyi baya bari a fadi sunansa ko a saka sunansa,wani kaso mafi girma na dukiyarsa ya ware ya kuma sadaukarwa al'umma........to amma kuma hirar tasu,yana buqatar tayi tsaho,yana buqatar wannan kusancin a tattare da ita......yana kuma cirar wasu abubuwa daga sautin muryarta da yanayin yadda take maganar daga qasan zuciyarta.....kamar akwai wani abu daya shafeta cikin maganganunta. A nutse ya miqe yana zama kujerar dake facing nata,yana zube idonsa a kanta tare da qoqarin lalubo qwayar idanunta. "Exactly......kin kawo point me girma......me zai hana ki karbi aikin a hannuna?.....a matsayin personal assistant nawa a wannan bangaren?" Maganar tasa taja hankalinta sosai har sai data waiwayo ta dubeshi da raunanan idanunta. Wannan din yana daya daga cikin cikar burin rayuwarta,ta zama sila na shigar da farinciki zukatan wasu,ta zama sanadin yayewar damuwar wasu....amma tana ganin kaman zatayi shishshigi ne ta shiga rayuwar da sam ba tata bace. Ya fahimci akwai kokwanto sosai cikin kallon da take binsa dashi,sai ya sakar mata murmushi yana dunqule hannunsa guri guda,saboda kallon da take masan kaman tana sakar masa wasu harsasai ne cikin jikinsa. "Da gaske......ina buqatar irin hakan.....irinki cikin rayuwata.....amma wannan karon ni zan biyaki.....bake zaki biyani ba" Ya qarasa fada yana kallon qwayar idanunta. Murmushi dan siriri ya qwace mata,ta kawar da kanta gefe tana kaucewa ganinsa. Wani irin kyau fuskarta ta sake masa,murmushinta ya tsaya masa a zuciya,ya kasa dauke idonsa a kanta,iya adadin murmushin da ya taba gani akan fuskarta qididdigagge ne,ashe haka murmushi yake mata kyau?. Yasan me ta tuna,don haka shima boyayyen murmushi ya saki,ya ciri wata farar takarda da abun rubutu da suka samu a gurin ya tura gabanta. "Zan shiga wanka......kafin na fito ki rubuta adadin salary din da kikeso,daga kan million goma har million dari". Waiwayowa tayi a nutse,ta dafe takardar tana dubansa. "Ba komai ne akeyinsa saboda kudi ba......kaman yadda ba komai bane kudi ke iya siyansa ba......wasu ladaddakin sunfi duniya da abinda ke cikinta muhimmanci a rayuwar d'an adam" Ta qarasa furucin yana duban labbanta da suke motsawa da wani irin yanayi dake matuqar daukan hankalinsa. Kai ya jinjina yana miqewa gami da matsawa a nutse yana zare socks din qafarsa. "Na sani....saidai ko Allah daya haliccemu ya sanya ladan kowanne aiki.....kaman yadda idan nayi aiki haqqina ne ka biyani....haka idan akamin haqqi ne akan kowa na biyashi" Ya qarasa fada sanda yake zare rigar jikinsa. Kanta ta dauke da sauri daga kansa zuciyarta na harbawa,batason kallon wannan ginannen jikin shi wai baisan hakan
Chapter 114 · 0% Book details