← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 177 OF 215

Sashe 177

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

namanta kaman yadda hajiyarmu ta buqata daga nan zuwa wayewar gari" "Kuyi duk yadda kukeso" Ya fadi yana tsinke kiran don ya kwashi mintunan da yakeso. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ 147 *_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_* *_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_* *_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_* *_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_* *_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_* *_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_* *_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_* *_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_* *_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_* *_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_* *_HAIHUWA KIKAYI?_* *_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_* *_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_* _Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_ 08104553105 08127084190 *_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_* *_BGAWO'S KITCHEN_* *MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU* "Ya zakace musu haka?,ya zakayi haka hamma?" Sabreen data barke da kuka cikin rawar jiki ta furta,sabreen din da baisan da zamanta a wajen ba sai a sannan. "Ba zasu aikata ba.....kudi sukeso,sunsan kuma kudi ba zasu karbu ba muddin suka tabata......sai hajiyar da....." Cak ya dakata da maganar yana nanata sunan hajiyarsu da suke fadi. "Hajiyarsu.....kasan wacece hajiyarsu?" Sabreen ta fada tana miqewa tsaye cikin wani birkitaccen yanayi. Gaba daya ji takeyi tayi loosing duk wani control nata da tunaninta......tana jin komai yazo qarshe,komai yazo gaba.....tana jin ko na minti daya ba zata sake iya ci gaba da rufe sirrin matar nan ba,duk wani signal ya kama ya kuma nuna kanshi......sannan ya bayyanar da komai da komai. "Nace kasan wace hajiya suke magana akai?" Ta maimaita tana ware hannayenta gami da fiddo idanunta waje kaman wadda ta zare. Bata jira amsarsa ba ta dora. "Ba kowa bace sai MAAMAH!" ta fada da wata irin tsawa da bata tashi tarwatsewa ba sai a tsakiyar kunnen fuad da wani irin nau'in mafi munin sauti. Idanunsa da yakejin sun masa nauyi ya aza akan fuskar sabreen da wasu manya manyan alamun tambaya a kansu. "Maamah?" Ya maimaita sunan da salon tambaya. "Eh maamah.......maamah itce ya dauke amna.....maamah ita ta saka a dauke amnah!" Ta sake fada kuka me qarfi yana kubuce mata. Daga zaune da yake amma sai yaji kaman duniya tana zpagayawa ba daidai ba......kaman akwai wasu sautuka da abubuwa da suke tafiya ba daidai ba. "Kinsan me kike fada sabreen?....maamah fa?.....rashin imani da qeqashewar zuciyarta har......" Bata jirashi ya qarasa ba wani sashe na zuciyarta ya soma gaya mata cewa,kariya yakeson bata,qaryatata ita kuma yakeso yayi. "Abun nata baikai haka ba ko?,haka kake zato?.....kana ina sanda ta tursasamin aurenka don kawai ta mallakeka......ta tsundumani a rayuwarku don kawai na zama silar mallakarka gareta ta hanyar yin garkuwa da 'yan uwana......ta sanyani a kwanaki mafiya tsaho da tashin hankali a rayuwata?......kana ina a sanda ta sake diban qannena ta riqesu don ta samu damar cimma burinta a kanka da kaina......ta tirsasamin lallai saina shayar da kai na kuma ciyar dakai da asiri?.....na tufatar da jikina da rigar da zata zama silar soyayyarka a gareni?.mashkur......dama sauran wadanda suka kawowa rayuwarmu farmaki kina tunanin yin kansu ne?.....fareeda data samu nasara a kanka kana tunanin haka siddan ta sameta?......." Dora hannunta tayi saman matashin cikinta. "Hatta da wadannan yaran da basuzo duniya ba kana tunanin sun tsira a hannunta?,banda kiyayewar Allah zuwa yanzu lissafin watana nawa da barinsu akeyi.........ka duba wannan" Sai ta ciro wayarta daga handbag dinta tana bude masa inda ta adana videos dinnan da sauri sauri ta dangwarar masa ta juya da sassarfa tana fita a parlor din tana sauka qasa. Wayar yabi da kallo yana jin yadda jijiyar kansa ke wani irin harbawa. Yanajin kira na shigowa ta wayarsa dama system din gabansa,wanda ya tabbatar team dinsa da suke bincike tare ne suke kiran nasa,saidai baida wani kuzari ko kadan. Hannu ya sanya ya dauki wayartata,ya kuma bude video din da ta ajiye masa. Murya da komai ya fita tassss.....baya buqatar neman qarin bayani,sai kawai yayi connecting wayar da system dinsa,ya shiga aikin duba ingancinsa. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Yaji yana maimaitawa bakinsa yana rawa. Duk da ya jima yana hasashe.....ya jima yana kwana yana kuma tashi da tarin tulin lissafin meye da meye maamah zata iya aikatawa dama wanda ba zata iya ba?,amma sai ya samu kansa da jin komai sabo a tattare dashi.....sai ya samu kansa da jin komai ya zame masa baqo. Kaman wanda aka yiwa allurar qaimi,sai ya zabura,ya hada connection da kowa dake cikin team dinsa suka fara aiki akan kiran mutanen. Koda kowa ya gaji....koda kowa yana ganin dare yayi a barwa safiya,shi bayajin zai iya hakan......baya jin akwai abinda zai dakatar dashi daga lalubo maboyarsu daga daren nan zuwa asubahi......baya buqatar a wuce haka. Sanda ake qwala kiran assalatu na farko signal ya harba sosai,kai tsaye kuma ya basu daidai direction na inda network da layin yake motsawa. "Alhamdulillah" Ya furta yana zarar wayarsa da sauri. Jordan ya soma kira yace ya yiwa su abdulgafar magana......su hadu yanzun a masallaci zasu fita ana idar da sallar asubahin. Sai daya tabbatar ya gama hada komai sannna ya miqe yana nufar toilet. Yadda yakejin jikinsa kaman yana dab da kasa responding komai......amma ya gayawa kansa sai ya qarasa aikin daya fara,don haka ya hada ruwa me zafi yayi wanka. Cikin baqin shirt da wando ya shirya,ya jawo wani boots dinsa ya saka yana dora baseball cap a kansa. Duk wani abu da zai buqata ya hada a back pack ya rataye,ya maida baqin eyeglasses a idanunsa sannan ya fara saukowa a gurguje. Har yakai parlor din farko wani abu ya fusgi zuciyarsa,sai ya koma da hanzari yana dosar dakunanta. Bai sameta asalin dakinta ba,sai a daki na biyu ya sameta. Qudundune ya sameta cikin duvet,da alama baccin me jima da saceta ba,don ga cups nan da plate da tayi amfani dashi da sauran ruwa. Har ya qarasa gabanta bata motsa ba,alamu sun nuna baccin daya dauketan me nauyi ne. Saman kanta ya tsaya yana duban kyakkywar Fuskarta,wani matsanancin tausayinta ya saukar masa,ya tsugunna a tausashe ya sauke mata kiss a goshinta don baiso ya tasheta,ya miqe a hankali ya maida hankalinsa ga dakin. Plates din ya soma tattarewa da cups din,murmushi ya kubce masa. Da gaske ciki yana canza hali da dabi'a,matar da daqyar sai yayi fama da ita take cin abinci,yau itace anywhere anyhow kama abinci take bada wasa ba. "Allah ya qara lafiya" Ya fada yana ficewa dasu ya kaisu kitchen sannna ya fice daga gidan. Cikin dukkanin shirin daya kamata suka gewaye area din kafin su sanya kai zuwa ainihin inda na'ura ke basu direction a kai. Cikin qasa da minti biyar suka nannade qofar gidan suka nadeta tsaf da wani irin qarfe. Sake kutsawa sukayi da wata irin sassarfa suna bada sanarwar suna qarqashin kamen hukuma,kada kuma wanda ya motsa a cikin su. Tun kafin sukai ga qarasowa ciki sukayi surrender,ba yau suka fara irin wannan aikin ba,saboda haka sun tabbatar da cewa sun riga sun kamu,tunda kuma suka kai ga cimmasu har inda suke lallai ba makawa basu da sauran wani qofa na fita. Qoqarin dakatar da fu'ad sukeyi wanda shine na gaba sanda yake qoqarin doke qofar dakin. "Sir......it may b......." Bai iya bari sun qarasa ba ya yiwa qofar wata Kyakkyawar duka data sanyata bude kanta da kanta. Bindigarsa ya saita akan mutum na farko dake tsaye kafin sauran suma su saita ragowan na dakin. Ya jima da koyar harbi da bindiga,ya kuma mallaketa da license dinta da komai saboda dalilai na tsaro,amma ba kowa bane yasan da hakan. "Kowa ya cire abinda yake jikinsa,bindiga ko wani qarfe ku zube a nan" Shugaban tawagar ya fada yana daka musu tsawa. Jordan ne ya soke tashi bindigar sannan ya fara zagayasu daya bayan daya cikin qaqqarfan takun nan nasa don tabbatar da kowa ya cire komai dake a jikinsa. "Hamma....." Muryar amna ta daki kunnensa da wani irin sauti galabaitacce. Idanunsa ya daga da zafin nama yana maidashi inda sautin yake. Amna ce ke takowa a hankali jiri yana kwasarta daga wani daki dake cikin babban dakin. Maida bindigarsa yayi da wani mugun zafin nama yana dosarta,wanda baikai ga isa ba qarar sautin bindiga ya tashi a dakin. Cikin tsarewar ubangiji ya bashi ikon kaucewa ya kuma ture amna ya wuce ya bula bango ya nutse a ciki. Cikin qasa da second biyu Jordan ya masa wani irin duka,ya kama hannuwansa ya murdesu ya maidasu baya ya karbi bindigar,sannan ya daki gwiwarsa ya zube a qasa. "Zakasan kayi mistake........idiot!" Jordan ya fada cikin tsananin fushi yana masa wani mummunan dauri. Amna ya daga da hannu bibbiyu,ya cire rigar daya dora daga saman rigarsa yana yafa mata saboda yadda take gayarta haka,ba dankwali bare mayafi. Wani irin zafi zuciyarsa takeyi,ya riqe amna da kyau suna takawa kafin ya kalli jordan "A yau nakeso su fadamin waye ya sanyasu wannan aikin,a yau basai gobe ba!" Ya fada da tsananin zafin zuciya. Yau din ta koma masa lovey dovey dinsa,ta koma masa amnansa sak ta shekarun baya,ta mance da wani surukuta a tsakaninsu,ta lafe kanta saman kafadarsa tana rera kuka. Ita kadai tasan ya takeji a zuciyarta da qirjinta,nata duka me sauqi ne,tana tausayin fu'ad ne a sanda sakamakon binciken ya fito sunan MAAMAH ya zama suna na farko cikin wadanda suka assasa dauketa. A baya wani tsoron matar takeji......a yanzun kuwa sai zuciyarta gaba daya ta qeqashe a kanta. Tayita kwanciya ne bayan ta farfado saboda tsoro,saboda tanason ta tsira da mutuncinta. Tana tsoron ta nuna musu ta warke batasan meye next step nasu ba. Maamah tayi waya dasu har sau ba adadi......taji kuma muryarta ta sake tabbatarwa da cewa tabbas din itace. Abun ya matuqar bata m amaki ita kanta,ya kuma girgizata. "Wacce irin zuciya ce a qirjinta?" Ta tambayi kanta da kanta a mamakance. Wani abu me zafi da tauri ya dinga hadiyewa,kai tsaye ya bada umarnin wucewa da amna asibiti don a duba lafiyarta. Kasa
Chapter 177 · 0% Book details