← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 182 OF 215

Sashe 182

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read

be.....you're my forever adda sabreen......am safe.....karki damu da yawa,ki bani aron wadannan awannin,zamu kasance tare da juna in sha Allah,ma'u zata kasance tare da ke,ayimin afuwa"_ sai kawai ya tura mata,yana buqatar isashen time da zaiyi healing daga nan zuwa safiya,bayaso ya jefata a damuwarsa,wadda batasan sadda ta samo asali ba,yana ganin kamar yin hakan rashin adalci ne kawai. Yanaso yaji muryarta shima......yana kewar wannan lallausan sound din nata wanda koda fada takeyi ko masifa laushinsa sai ya bayyana,but definitely idan taji muryarsa saita gane damuwarsa. Cikin taqaitaccen zaman kusa da kusa da sukayi da juna,yana mamakin yadda take da saurin karantarsa,sauyawarsa ko damuwarsa,walwalarsa ko akasinta. Abu daya daya sani shine baiwa ce,ba duk namiji Allah kewa baiwar mace me kula da dukka damuwarsa da matsalolinsa ba. Sauran kiran da saqon nasu farouq ne,duka sai ya share,saidai akwai saqo guda daya daya dauki hankalinsa. "Maamah is sick,she was admitted to the hospital" Idanunsa yaja ya lumshe,baisan me zaice ba?,me zaiyi?,sai kawai ya kashe wayar gaba days ya cillata gefe. Ya samu yaci abincin kadan,sai ya maida hankalinsa kan tataccen ruwan blood orange natural da aka hado masa dashi,da kuma wadatar kayan fruit,cherry pear jujube sai gooseberry da suka hado masa dashi. Dasu ya danyi fresh up,yadan jira abincin ya narke kadan sannan ya wuce bedroom Kai tsaye. Duk wani haske da komai da zai bashi sauti sai daya kasheshi,ya zamana daga zallarshi sai sautin alqur'ani da yake tashi kadan kadan ta wata qawatacciyar fitila dake tsakiyar gadon,wadda ke zuwa da qaramar fanka me bada sanyi kwatankwacin na ac da Bluetooth da zaka iya using nashi,sai ya kashe hasken fitilar dake jikin yabar iya sound din. Yayi lamo saman gadon kaman dazu yana bibiyar karatun,bai tashi gane kuskurenshi ba sai da bacci ya qauracewa idanunshi fafur. Juyi ya dinga yi saman gadon shi kadai yana jin yadda kadaicinta yake neman hallakashi,kowanne sashe a jikinsa sabreen din yake buqata,kowanne bangare na jikinsa kewarta yakeyi. "Ya salam ya al-hadi". Yana sawwara ta yadda zai iya yin nesa da ita dalilin tafiye tafiye na kasuwanci......ta yaya hakan zata yiwu?" Ya tambayi kansa da kansa. Daga qarshe dai ya tabbatar hakan bame yiwuwa bane,ya tashi zaune yana duba qaramin kyakkyawan agogon dake saman side drawers na gadon. "Oops" Ya furta yana dafe goshinsa,dare yayi,yayi imanin zai wahala idan bata fara bacci ba yanzun,idan kuma har ya zama silar tadata a baccin bazai yafewa kansa ba,sai ya maida kansa ya cusa tsakiyar pillow din yana qagara asuba tayi.
Chapter 182 · 0% Book details