Sashe 94
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
akan yarinyar ba?. Komai bai dameshi ba irin yadda zai maidata mallakinsa fiye da yadda ya maidata a yanzun......yanaso ita kanta a jikinta ta sallama cewa ita din mallakarsa ce har abada,sai ya kalli farouq ya daga masa yatsa alamun zai amsa wayar. Kai ya jinjina masa,saidai kafin yakai ga dagawar wayar ta yanke. Qoqarin lalubota yakeyi ya kira sai tex ya fado masa _"Duk wanda kayi gangancin kamawa ko hukuntawa cikin mutanenmu dake hannunka.......ba shakka labarin matarka zai zama labari na farko da zai zama fitaccen labari kowacce safiya saman jaridun qasar mu da qasashen dake huldar kasuwanci dakai,suke kuma ganin kima da daraja a tare da kai_ Wani irin fusgar hankalinsa saqon yayi,saidai kuma kafin ya sarrafa kwanyarsa ya fahimci komai kiran maamah ya danne saqon,dole ya kauda abinda ke taso masa ya daga kiran yana sawa a kunnensa,bakinsa dauke da addu'ar "Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla,wa'anta taj'alal hazna iza shi'ita sahla". cike da fatan ba wani abu bane na daban zata baro dashi ba bayan abubuwan dake dabaibaye dashi ba. *_Da sauran masu bibiye da rayuwarsa kenan_* *_Ya zafafa da gaske wajen yin campaign na samun soyayyar ta,xaiyi nasara ko kuma zata zille masa?_* *_shin fareeda zatayi nasara ta hannun maamah kuwa?,kaman yadda tayi nasarar sanyashi auren sabreen a wancan lokacin?_* *_munata gangarowa da MAFARIN warwarar kowanne qulli da tonuwar binnannun asirai_* *_sai ince muje zuwa dai_* *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ _An rawaito daga manzan Allah S A W yace: Daga cikin mutane ukun da baxasu shiga aljanna ba,kuma Allah bazai musu duban rahama sune 1_ _"WANDA YAKE ZINA TUN YANA YARO HAR YA TSUFA YA MUTU BAI TUBA BA_ _2 _TALAKA ME GIRMAN KAI_ _Bukhari da muslim_ Cikin cikikakkiyar nutsuwarsa yayi sallama,zuciyarsa bata fasa neman dauki da ambaton sunan Allah ba. "Wa'alaikumussalam" Ta amsa masa a dake,tanaso ya fahimci cewa lallai shi din me laifi ne a wajenta.....wannan fahimtar tata da zaiyi ya zama sila kuma jagora zuwa ga wanzuwa da amsar babban burinta a yanxu na auren fareeda. A nutse ya fara gaidata,ta amsa masa a dake kaman dazun. Shuru ya ratsa na wasu sakanni kafin tace. "Baku hadu da fareeda bane?" Mamaki kadan ya kamashi,mamakin yadda akayi maamah din tasan da zuwan fareeda Maldives. "Mun hadu" Ya amsa mata kai tsaye,kasancewar mutum ne shi da wahala ko tsanani basa sakashi yayi qarya. "Amma me ya hanaka zama me masaukinta?......tunda kana da tabbacin ba don kowa tazo ba sai don kai". Mamaki ya sake kamashi,ya lumshe idanunsa yana jin takaicinsa yana sake daduwa. Gaba daya maamah din kowacce rana sake jirkita takeyi tamkar wahainiya,wasu abubuwan nata da takeyi sai ya dinga ganin tamkar ba cikin hayyacinta take ba. Maamah ke magana,uwar data kawoshi duniya,inda wani ne ya masa magana makamanciyar wannan yana da amsoshi masu yawa da zai bata. "Bansan da zuwanta.....batayi shawara dani ba kafin ta taho.....and a yanzun ina da iyali maamah,bani da wata alaqa da ita ta kusa ko ta nesa,banda dangantaka da ita" Ya amsa mata da kwantacciyar murya duk da tarin quna da bacin ran da yake ji na cin zuciyarsa. Idanunta ta qanqance cikin jin tashin hankali yana ratsata a hankali a hankali. Meye yake shurin faruwa?,meye yake faruwa da har yau din fuad da bakinsa ke ambaton INA DA IYALI?. Yaushe ne ta samu wannan matsayin a wajensa?,wata kalma da bata taba jin ta fito daga bakinsa ba?. Tarin masifa da wani irin tsanar sabreen tana ratsata,batasan wanne kalar abu ya kamata ta yiwa yarinyar ba......a yanzun a dukka illar da aka mata a rayuwa bayan ameenatu sabreen din itace ta biyu,koda ta raba sabreen da fu'ad bata jin taci riba idan tabar yarinyar haka siddan taci gaba da rayuwarta,tana jin ya kamata ta ajewa rayuwarta wani babban tabo ko miki da zai sanya koda a gaba zata zamewa wasu izina a kanta. To amma babban qalubale da barazanarta a yanzu shine TA WACCE HANYA ZATA RABASU?. Haka kawai take jin matsanancin faduwar gaba da fargaba idan ta tuna kalaman sabreen akan auren fu'ad,bawai ta fara son fu'ad bane matsalarta,idan hakan zata kasance ma zai zame mata daidai,tsoron shine shi fu'ad din......yana da wata irin zuciya da bata iya soyayya ba kaman yadda bata iya qiyayya ba......yana da wata irin zuciya me riqe abinda takeso da gasken gaske..... Wata irin zuciya da idan tana so tana so.....idan bataso bataso,zuciyar da zata iya sadaukarwa da abinda takeso komai data mallaka.....ta zamewa abinda take qauna kariya daga dukkan wata iska ko kuma guguwa. "Wanne iyalin kake magana akai fu'ad?,iyalin da nice silar wanzuwarsu a rayuwarka?.....ko kuma iyalin da babu wata kima ko martaba a tattare dasu?.....ko kuma ni da aka tsinceni daga ayarin tafiya aka wofantar dani saboda kun nunawa duniya bani da wata daraja a wajenku?,ni din ba kowa bace a wajenku?". Wani ciwon kai dukka maganganunta sukaso tasar masa lokaci daya,ya sanya tafin hannunsa ya dafe goshinsa yana murzashi a hankali tare da lalubo me ya kamata yace mata?,gefe guda kalmar IYALIN DA BASU DA WATA KIMA KO MARTABA tana masa zillo cikin kwanya. "AKWAI WANI ABU A LULLUBE" yaji wani saqo na zuciyarsa yana gaya masa. Idan har maamah ta aura masa sabreen ne saboda ta yarda da tarbiyyarta kaman yadda tace da farko......me ya kawo wannan maganar a kanta a yanzu?. Bayajin akwai wani abu qwaya daya da zai iya tunawa wanda ya taba hadasu koda cikakkiyar magana bare yayi tunanin akwai abinda ta taba yi mata. "Fareeda ta taso qafa da qafa.......ta sameni har muhallina......ta girmamani matarka ta tabamin haka?,fareeda tabar qasarta ta biyoka har inda kake,bata da kowa batasan kowa ba saboda tana sonka.......me matarka ta taba yi me kama da wannan?". Kanshi yaji ya sake qullewa......a yau din duka me ya kawo maganganu akan sabreen?,me yahau kan maamah duka akan sabreen din?. "Ina me baka umarni a matsayina na uwar data haifeka.......nan da kwanaki goma zan bar qasar nan......ba wani jirgi da zanbi,ba wanda zaizo ya daukeni....kai da kanka nakeso kazo ka daukeni ka kuma kawoni Maldives......ka kuma soke barinku qasar ka daidaitashi da nawa barin har sai na kammala uzurina sannan mu tafi......daga qarshe ina me baka umarni kaje kaga fareeda......ka kuma marabceta kaman yadda kowanne baqo yake marabtar baqonsa......wannan umarni na ne indai nice na haifeka" Daga haka ta yanke kiran ba tare data jira cewarsa ba. Shima wayar ya sauke daga kunnensa yana kallonta,kafin ya sakata a tafin hannunsa yana dan dokata kadan kadan. Kallonsa farouq yayi kafin ya aje dubansa ga wayar hannunsa. Ya fahimci wadda tayi kiran ya kuma ji wani abun da take cewa saboda magana take da qarfi da kuma fushi. A abinda yake lisssfawa zaiwa fareeda kowanne ya debo sai yaga yayi masa kadan. A hankali maganganun maamah din sai yaji kamar suna tafiya da farincikinsa suna son rushe duk wata walwala daya samu. Idanunsa ya bude kan farouq yana hadiye kowanne bacin rai da maamah ta sanya masa da rudanin saqon daya shigo wayarsa a dazun. "Ina jinka......kaman magana kakeso muyi ko?" Yace da farouq. Idanu yadan zubawa fu'ad din,sai yaji tausayinsa yana kamashi. Kowacce ni'ima da baiwa ta rayuwa Allah yayi masa......amma ya rasa UWA TA GARI. Ya sake yarda tabbas rayuwa jarabawa ce,hakanan kowanne dan adam akwai inda tashi jarabawar take,ba wanda yake samun jin dadin duniya dari bisa dari. Murmushi farouq ya sakar masa,sai yaji bazai iya kowacce magana dashi a irin wannan yanayin ba,don haka ya sauya akalar zancan yana yin murya qasa qasa "Wai yaya akayi wannan gingimarin ta iya hawa saman keke?,karaya nawa keken ya samu?,duk da ni shaida ne akan yadda keken ya kusa komawa akwala sabod......" Naushi yakai masa cikin sa'a ya daki iska. Ya fahimci lallai da gaske farouq so yake ya maidashi birin wasanshi. Gefe farouq ya koma yana dariya,can qasan ransa yana jin dadin hararar da fu'ad yake watsa masa,yasan tabbas ko bai nasarar gusar da baqincikinsa ba zai rage masa wani abu. "Wallahi ka iya bakinka akan iyali na......kada ka yarda mu saka qafar wando daya dakai" Yayi maganar yana nunashi da yatsansa. Ido farouq ya zaro yana daga hannuwansa sama "Ya salam.....kace me?,iyalinka?,unbelievable.....wazai tayani jin wannan kalmar.......sabreen won the battle" Qaramin dutse ya dauka zai jefeshi ya kwasa da sassarfa ya wuce cikin gida yana cewa "Wallahi ta haukatashi......ya zama madoki" Tilas dariya ta subuce saman labbansa. Sai da farouq ya bacewa ganinsa sannan ya maida hankalinsa kan wayarsa. Kai tsaye ya kira jordan sukayi magana ta wasu mintuna sannan ya kashe,ya kalli agogonsa yana lissafin awannin da suka rage su kaishi gurin target dinsa.