← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 215

Sashe 127

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hira abinsu,saidai komai ya tsaye mata a wuya,hatta ruwan da tasha. Yana takowa ta tsakaninsu xai wuce VIP suit zazzafan aman ya taso mata,ta saka hannu da nufin tareshi ta miqe da saurin don wucewa lavatory.......saidai inaaa,wani karo da tayi da fu'ad din take aman ya qarasa fitowa ta kuma soma kwararashi tun daga qirjinsa saman lafiyayyar suit dinsa har saman qafafunsa. Ba wannan bane damuwarsa.......yadda take kakarin amai duk jikinta yana kyarma shi yafi daga hankalinta,ya bita da sauri a rude yana fadin. "Subhanallah......ya salam......sannu.....am sorry" Kaman zai sake mata kuka. Yadda ya kanainaye abarsa su anni sai baya suka tsaya suns jera mata sannu tana ci gaba da yunquri kaman zata fidda kayan cikinta. Kafin ta gama kanta ya fara sarawa da wani irin ciwo,zazzabi jikinta kuma ya sake ninkuwa akan nada. Shi ya karbi ruwan daga hannun daya daga cikin crew din ya bata tasha saboda yadda take haki,ya saka hannu ya dagata suka wuce lavatory. Da idanu take binsa kawai sanda yake qoqarin gyara mata jikinta ba tare da ya damu da qazantar data zuba masa a nasa jikin ba. Idanunta ta lumshe a hankali a kansa sanyi yana ratsa gabbanta. Ta dauka zaiyi mata fada,ko zai nuna fushi saman fuskarsa,ko yayita hargagi idan ta kama ya tureta ma,amma sai taga sabanin hakan. Gaba daya ya bata attention dinsa,tanaji anni na cewa amna ta biyosu ko xata tayashi da wani abun yace "no need.....zauna kawai". Wani irin abu taji yana ratsata a kanshi,ta zuba masa ido sosai sanda yake goge mata saman qafafunta da takalminta daya dan baci,saita miqa hannu ta zaro napkins dake ajiye a lavatory din ta tsugunna a gabansa tana daidaita tsahonsu. A nutse ya dago suka hada idanu,fararen zagayyun idanuwansa sun qara haske wanda suke sauya launi nan da nan da wani abun ya taba zuciyarsa,sai ta langabe sannan a nutse ya dora napkin din saman qirjinsa tana cewa. "Am sorry" Ta furta a hankali. Labbanta yabi da kallo yana jin suna qara burgeshi,murmushi ya subuce masa wanda ya sake qara fidda kyansa,hannuwansa duka ya saka ya daga kafadunta suka miqe tsaye,idanunta yake kalla "Sorry for what?" Shima ya tambayeta muryarsa can qasan maqoshi. Idonta ta janye tana nuna qirjinsa da yatsarta,sai shima ya maida dubansa wajen. Murmushi ya kuma saki,ya kamata yana jinginata da jikin mirror din gurin,sannan yaja da baya ya soma balle button din suit din farkon,ya xareta ya ajiyeta a gefe,ya sake balle button din ta biyun itama ya ajiyeta a gefe,sai ga shirt din cikin ta ukun ta fito fes ba abinda ya tabata. Idonsa ya sake dagowa ya kalleta sannna ya daga mata kafadunsa gami da watsa hannuwa alamun ba abinda ya sameshi. Murmushi ta saki itama abinda ya kusa narkar dashi kenan,fararen jerarrun haqoranta sun fito reras tamkar adon lu'ulu'u,har qasan ranta taji dadi da dayar rigar bata baci ba,ya sunkuya a nutse ya zare takalman qafarsa sai socks kawai daya rage,sai ya miqa hannu ya kama hannuwanta,a hankali yace "Kinga abinda nake gudu ko?,zazzabin nan ya dawo sosai". " Ba matsala......zai" "Da matsala mana......bakisan yanzun nan sai na rasa nutsuwata ba saboda wannan zazzabin?" Ya tambayeta da dukka idanuwansa a kanta suna kuma karanta gaskiyar abinda yake fadi daga qasan zuciyarsa ne. Wani abu na daban takeji,wai yau ita ake damuwa da ciwonta?,matar da saidai ta damu da ciwon wasu amma nata ciwon dai damuwar qannenta ne kurum?. A nutse ya riqe mata hannu suna takowa har xuwa bakin wani dan box,yasa hannu ya danna ya budeshi,saiga loafers masu kyau ya ciro ya saka a qafarsa sannan ya kalleta *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ 110 "Zan iya daukarki mu qarasa?" Kai ta girgiza masa da sauri,sai ya dauke kai bai sake cewa komai ba. Qafafunta takejin kamar ba zasu iya daukarta ba sanda daya daga cikin crew din ke gyaran wajen aman haka taja jiki tana komawa gurin ta. Xarginta yana sake qarfi da kowanne motsi na yarinyar,amma jikinta da zuciyarta sunqi aminta da cewa coki zai iya kasancewa a jikinta. Ita ta kawo yarinyar rayuwarsa kuma har yanxu bata manta da fafatawar da akayi dashi kafin ya karbeta ba......to mene haka yayi sautin sauya masa ra'ayi game da yarinyar idan ba sihiri bane?. Wannan abun yafi qarfin bariki......ta samu kalar kulawa da damuwar da ko amernatun bata sameta ba. Har yanzunda take zaune idanunta suna iya gane mata yadda hankalinsa yayi mugun tashi da aman da takeyi din,baya jin kunyar kowa dake tsaye a wajen,kamarma ya manta da wanxuwar kowa a wajen saishi da ita kawai....dole ta lalubo musabbabin ciwon nan da dukka iyawarta,musaddiq ne kawai kuma zatabi ta kanshi ta samu information din da takeso hankali kwance. Tayita zuba idanu ta gansu ta inda su anni ko maamah suke amma sai tsintar kanta tayi a VIP suit. Ta yita maimaita sunan bayan ganin wajen,wajen yaci sunansa dari bisa dari,zama rantse da Allah ba cikin jirgi kake ba,don ko windows sai ka danne wani abu sannan zai yaye maka su. Akwai mini bed da sofas masu tsananin kyau da taushi a gurin,tamkar kana cikin wani qawataccen madaidaicin parlor maras tarkace da hayaniya,harda office area da aka yiwa gurin daya ajiye tarkacen kayan aikinsa kamansu system dinsa da wasu documents nashi. Gadon yaso tayi kwanciyarta amma taqi,sai ya ajiyeta saman recliner,ya jawo foot setter din dake qasanta ya dora mata qafanta akai sannan ya lullubeta da wani sky blue din blanket sannan ya juya a hankali yana fita a wajen ta wata qaramar qofa. Numfashi taja sosai tana saukewa,tana yawo da qwayar idanunta cikin wajen. Wani nutsatsen guri ne da yaci sunan VIP suit din,daga ita saishi a wajen,guri ne da idan kana nan bazakasan meye yake faruwa cikin jirgin bama. Tabbas duniya girma gareta kuma fadi gareta,sannan ta sake yarda ta sallama kuma rayuwa mataki!mataki ce. Daga shigarta family din jadda taga abubuwa masu yawan gaske da idan a baya akace mata akwaisu a duniya hankalinta bazai dauka ba,da gaske ne kudi ba wasa bane.....arziqi kuma ba qarya bane......kudi nada wani irin power......suna mallakawa mutum girma da fadin ikon da baisan iyakarsu ba. Wani lokacin idan ta kalleshi sai ta dinga jin yafi qarfinta nesa ba kusa ba......ya kuma tserewa ajinta.....wani lokacin saita dinga jin kokwanto da shakkar sake masa dukka gaba daya.....kada a gaba ya samu dukkan komai ya kuma zame ya barta tunda tabbas ita ba ajinsa bace,saidai kuma wucewar kowacce daqiqa da second yana sake bata dukkan wani dalili na soyayyar gaskiya a aikace ba wai a baki ba. Maida idonta tayi ta rufe tanajin yadda zazzabin ke ratsa qasusuwanta,gefe guda kuma tana jin irin tababar da akeyi tsakanin bangarorin zuciyarta dukka akan MUHAMMAD FU'AD JADDA. Motsinsa taji kafin taji sautin nutsatstsiyar muryar nan tasa da sautari takan mata gizo. "I'd appreciate it if everyone could stay where they are,am looking for some peace and quite,i need some time to myself.......madam bata da lafiya" Yayi maganar cikin dakiya da miskilancin nan nasa. "Okay sir" Crew din data kawo masa abubuwan daya buqata ta fadi tana juyawa bayan ta ajjiye masa. Idanunsa ya daga ya mayar kan farouq daya tsayar daga qofa ba tare da ya barshi ya qaraso ba. "Karkace komai.....wannan saqok ba da crew dinka kawai kake ba.....ni akewa jirwaye da kaman wanka.....aini kaina yanzu nasan kafi qarfina.......system zaka bani zan rage wani aiki kafin mu qarasa dubai......acan zamuyi layover". Hannu ya miqa cikin shariya ya jawota ya miqa masa yana kafeshi da idanu,dole dariya ta qwacewa farouq ya amsa yana komawa. "Wallahi duk kaci bashi saina rama" "Can maka" Ya fada yana takowa ciki,sai tayi saurin lumshe idanunta don kada ya kamata tana qare masa kallo. Rigar ta zauna masa sosai ta fidda muscle dinsa dake boye a rigar,hakanan ta sake haskashi qwarai,dram dinsa da farouq sai data sakata murmusawa duk da yadda takejin zazzabin na rarakarta. Shikam yayi sa'a daya samu amini kaman farouq a sanda yake cikin yanayi na tsanani......ita ta rasa kaman farouq din,ta kuma rasa abbanta da ummienta,su huda kadai suka rage mata,take taji wata kewarsu tana kamata. Tayi nisa a tunaninta ta jishi cikin jikinta. "Oya.....get up" Ya fada yana dan dagota. Mug din hannunsa ta kalla,ita yanzu ba zata iya sawa cikinta komai ba,saita langabe masa tana girgixa kai. "Bazan iya sha ba" "Even a little?" Ya tambayeta tana dage mata girarsa dake da cikakken eyebrows,kai ta daga masa a hankali tace. "Zansha idan na huta.....I'm feeling nauseated" Hannunsa yasa a tausashe ya shafi gefan fuskarta,sannan ya jawo wani qaramin ottoman sofa ya zauna a kai. Haka kawai ya sakata a gaba,yana kurbar tea din yana qare mata kallo kaman wanda ya samu mirror,blanket dinta taja zata rufe fuskarta ya saka hannu daya ya riqeshi gam. "Ki barni mana na kalla......wannan face din kawai nake kalla naji nutsuwa ta saukarmin" Ya fada a karye kaman wani maraya,har sai da taji tausayinsa ya tsarga mata. Hakan bai isheshi ba,koda ya kammaka sai tsintarsa tayi cikin blanket din,ya haye recliner din abinsa yana cusa kansa a cikin blanket din "Wannan ta miki fadi,bari na cike miki space din daya rage" Ya fada yana shigewa abinsa ya kamota cikin jikinsa sosai. "Kai....ya salam......your temperature is too high" Ya fada yana matseta a jikinsa sosai. Ita kanta ta sani,qaruwa kawai zazzabin yake,sai kawai tayi luf a jikinsa shi kuma yayi mata masauki me kyau. Shuru ne ya ratsa tsakaninsu,kowanne yana sauraren bugun zuciyar dan uwansa,suna jin sanda jirgin ya soma motsawa,bayan wasu mintuna kuma ya cira yana lulawa sararin samaniya dasu.
Chapter 127 · 0% Book details