← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 215

Sashe 66

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sai yaji wani tsoro da razani ya kamashi,bai taba magana dasu da irin wannan sautin dake cike da fushi da tsawa ba. Maida wayar yayi sannan ya matsa cikin hikima ya qyasawa abokin aikinsa. A zuciye ya wurgar da kan wayar,sannan ya juyo yana takowa zuwa inda ya ajiye mashkur. Zagayashi yayi har kusan sau uku,zuciyarsa na masa wani irin tsalle a qirji,ba abinda zuciyarsa ke gaya masa illa ya dauko bindigar ya fasa tsakiyar kansa da ita. Numfashi yaja sosai,sai ya juya yana komawa ciki bayan tunawa da yayi da ita,sa'annan muddin yaci gaba da zama a gaban mashkur zai harbeshi dinne abinda yaketa qoqarin hana kansa aiwatarwa. A bude qofar dakin yake,wannan ya bashi damar shiga kansa tsaye. Dakin da zuwa sannan gaba daya komai na cikinsa ya hargitse,banda fasasssun glass da kwalaben fitilar data kwatsawa mashkur ba komai a qasan,sai wargatsatstsun kayan dake saman dressing table dinta da suka tarwatse a qasa. Inda take kwace ya maida idanunsa,har yanzu tana kwance inda ya barta din,idanunsa kafe a kanta ya qarasa gabanta. Sauka idanunsa yayi a saitin bakinta,pink lips dinta da suka sauya launi kadan suka kuma bushe qamas,hoton yadda wiwin ta zauna akan lips dinta ya dawo masa,wani mulmulallen abu ya tokare masa wuya,da sauri ya ture hoton daga kwanyarsa,ya tsugunna a gabanta yana tunanin me zaiyi mata?,me ya kamata ya fara yi?. Sake maida dubansa yayi ga fuskarta wadda har dogon dokin wuyanta ya bayyana,hakanan wani sashe na kafadunta saboda saukar hijabin da ya fara samun nasarar yagawa. Sauka dubansa ya qarayi xuwa saitin qirjinta,inda a daidai nan hijabin ya nuna muguwat cukuikuyewar da zata gaya maka an riqe wajen ne da mugun riqo. Qirjinsa yaji ya wani doka,yawun bakinsa kuma yaji ya dauke qaf kaman ba'a taba halittar yawu cikin bakinsa ba. Abinda bai taba ji ba tsahon rayuwarsa yau karon farko ya jishi......wata mummunar faduwa gaba,sannan take yaji hannuwansa da qafafunsa sun fara rawa sakamakon tunanin daya bijiro masa. Sake xubawa wajen ido yayi,yayin da zuciya ta fara masa imagination na hannuwan mashkur a wajen,wani abu me qarfi ya daki zuciyarsa har sai da ya fusgo numfashinsa da kyau,dai dai sanda yaji itama ta ja numfashin da matsanancin qarfi har sai da qirjinta ya daga. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ Da wani irin yanayi numfashin nata ya soma fita,abinda ya sanyashi karon farko tunaninsa yazo masa cewa asthmatic ce. Miqewa yayi yana ranqwafawa saman kanta da nufin dagota ya canza mata makwanci duk da abinda yakeji,yana dagata din towel din jikinta yana zamewa ya kuma fadi saman qafafunsa. "La haula wala quwwata illa billah" Ya furta a sarari da wani irin bugawa da zuciyarsa tayi yana jin sautin har cikin kunnuwansa. Wani jiri da dan qaramin duhu yaji yana mamayarsa har sai daya lumshe idanunsa yana jan numfashi da kyau,ya tattaro dukka ragowar qarfinsa ya hada waje daya sannan ya soma takawa da ita ya ajiyeta saman gadon. Zamewa hijabinta ya qarayi,santala santalan fararen cinyoyinta suka fito,ya dauke idonsa da sauri yana jin yadda bugun zuciyarsa ya dake qaruwa,sai ya sanya hannu yana jan hijab din yana jin zuciyarsa na qara quntata waje daya kaman an daureta a tsakanin qirjinsa "Why?" Ya fada da mabayyanin sauti yana jin idanunsa na masa wani yaji yaji. Ta yaya wani zai samu hanyan shigo masa gida?,garin yaya hakan zata faru?. Kai ya girgiza,hankalinsa bazai dauki wannan ba.......kanshi da tunaninsa ba zasu iya karba ba. Taimakon gaggawa ya soma bata kaman yadda sukewa anni idan irin haka ta taso. Sam ya kasa hada bakinsa da nata saboda warin wiwin da yake tashi daga ciki,wanda yana daya daga cikin abubuwan mayen da ya yiwa muguwar tsana. Laluba aljihunsa yayi,sai a sannan ya tuna da wayarsa,ya cirota a nutse yana budewa gami da nemo number saddiq. Saddiq dinne kadai yasan bai fiya bacci da wuri ba,shima kaman shi yake,yanayin aikinsu ya sanya sukan iya raba dare a gida suna rage ayyuka. Bugu daya tak kuwa ya daga,muryarsa can qasa yace "Barka da dare hamma..." Bai amsa gaisuwar tasa ba yace masa. "Ka nemomin Dr rubayya......please ku kawota gida yanzu if possible" "Subhanallah...waye baida lafiya hamma?". Rasa amsar ma da zai bawa saddiq din yayi,sai kawai yace masa "Ba wani abu bane can.....just kayi sauri ku qaraso". Sauke wayar saddiq yayi yana duban farouq dake zaune a gefansa,wanda tunda ya daga wayar yaji da waye suke waya ya maida hankalinsa wajen duk da idanunsa suna kan system dinsa yau din yana sashen su saddiq dinne,don shima aiki gareshi sosai,sun samu sabon iri da sukeson su fara gwadawa manoma da manyan manoma da 'yan kasuwa,yanaso yayi settling na komai kafin ya kwanta,charger dinsa na system dinsa tayi masa tutsu,dole ya shigo ya karbi ta saddiq din ya jona gudun kada tayi shutting down. "Lafiya yace maka ba?" Farouq ya fada kansa tsaye yana duban saddiq. Daga masa kai saddiq din yayi,sai farouq din ya soma tattare ayyukan nasa waje daya ya killace yana cewa "Ka kirata kace zamu biyo mu dauketa......fu'ad bazai taba gaya maka worsening na komai ba indai shine". Ya furta yana saving ayyukan da sauri cikin aikin nasa,wannan ya sanya saddiq shima ya soma qoqarin kiran nata. Sai daya ajiye wayar saman bedsheets dinnan sannan ya lura da hannunsa da har yanzu yake tsatsafar jini. Radadin dake cikin zuciyarsa ya danne wanda yake ji a hannunsa,shi yasa sam bayajin komai a hannun nasa. Idanunsa ya sake mayarwa kanta,sai kawai ya samu kansa da miqewa yana daukan wayarsa,ya daidaita iskar dakin saboda gumi daya gani saman goshinta ya qara hasken qwan dakin sannan ya fara takawa cikin takatsatsan gudun kada ya taka wani abu ya soma fita a dakin yana komawa parlor. Tun bai qarasa ba ya hangesu sun cika hannunsu da wani baqin kakkauran matashi wanda ke sanye da baqaqen kaya full dress,tun daga hula riga zuwa wandon jikinsa. Iya riqon da sukayi masa kadai zai gaya maka yadda ya matsu a hannunsu. Ci gaba yayi da takowa yana karantarsa,duk wani alamu dake nuna tashin hankali da rudani sun tabbata a fuska da jikinsa. "Sakeshi" Fu'ad ya fadi yana jin hatta da security din gidan suma a yau bazasu tsira a hannunsa ba. Gaban mashkur ya qarasa ya zauna saman kujerar falon "Ku zaunarmin dashi a nan" Ya fada yana musu nuni da gefan mashkur din. Wani mugun duka sukayi masa wanda ya sanyashi zubewa ba shiri yana fasa qara. "Ku jirani a waje" Fu'ad din ya fadi yana qoqarin hana jinin dake diga a hannunsa bata sofa din da yake kai. Kallon fu'ad kawai matashin yakeyi,yana jin yadda kashi da fitsari gaba daya suke neman kufce masa,saidai kuma yasan babban kuskure na gaba da zaiyi shine ya saki fitsari ko kashi a wannan kyakkyawan falon. Zai iya cewa a tarihin rayuwarsa kaf.....a tarihin manya manyan laifukan daya aikata a rayuwarsa bai taba cin karo da mutumin da yayi masa kwarjini irin muhammad jadda ba. Yana zube a gabansa yana jira yaji koda wata kalma daya daga bakinsa amma ko qwayar idanunsa bai daga ya kalleshi ba bare ya sanya ran wata tambaya zata biyo baya,ta goge jinin hannunsa kawai yake da lallausar tissue din daya ciro a tissue box din dake gefansa. Bawai yayi hakan bane saboda ciwon yana da muhimmanci a rayuwarsa ba.....a'ah......yayi shuru ne saboda a yanzu babban muradinsa shine yayi mummunan lahani a garesu da babu me iya gane fuskokinsu,duk kuwa da cewa ko a yanzun fuskar mashkur ta haye tayi kumburin da dukka wata halittar fuskar ta sauya daga asalin yadda take,abinda yake sake sanya tsoro me yawa kenan ga zuciyar hanzari. "Don Allah me gida.... Kayimin rai,ka tausayamin me gida......don girman Allah". Kalaman hanzari kenan wanda ya gaza jiran yaji abinda fu'ad din zai fada. Cillar da tissue din yayi,sannan ya daga idanunsa da har yau launinsu bai koma daidai ba ya aza akan hanzari "Waye ya gayyato ka?,duka ku biyun kuma waye ya aiko ku?' Tambayoyi guda biyun da a wajen hanzari suke masa kamanceceniya da tambayar kabari ga kafiri a ranar daren farko "Shine!.....shine wallahi" Hanzari ya fada yana nuna mashkur dake yashe a qasa har yanzu bakinsa na fidda jini. A yadda mashkur din yake yayita qoqarin murgina kai ya kalli koda idanun hanzari ne amma ya kasa ballantana ya fadi wata kalma da zata zama kariyar kai a gareshi. Kiran sunan mashkur da hanzari yayi shine abu mafi sauqi.....mafita mafi sauqi a gareshi akan ya ayyana ko ya ambaci daga inda ainihin kwangilar aikin ta fito,wanda fadin daidai yake da fadawar mutanen da suka jibanceshi da yawa cikin masifa da bala'in da baisan ranar fitarsu ba......gwara ya danganta kanshi da mashkur.....kusan yasan waye.....kuma koda yafi haka hatsari yazan bazai zartashi a hatsari da hatsabibanci ba.......koda ya zartashi yasan bazaikai mutanen da suka qirqirar da aikin ba. "Kana da masaniyar cewa maqabarta ka kawo kanka?......nan da kake zaune Motuare ce?!" Ya furta da sautin da hatta da mashkur sai da yaji kaman an buga masa guduma still saman ka bayan masifar azabar da yake ciki. Firfito da idanu hanzari yayi.......yayi gwagwarmayar rayuwa da yawa......ayyukan rashin imani bila'adadin......ya shiga komar Jami'an tsaro masu yawan gaske......da wannan kadai yana iya gane mutum da muhallin da ake magana ta gaske kai. Salati ya debo wanda ya manta rabon da ya ambaceshi a bakinsa,sallah kanta ba'a maganarta sam bars aje ga gurbin xama ayi wani xakiri ko tasbihi. "Zip your mouth!" Fu'ad ya furta da fushi "Ko burbushinku ba zaa samu ba.......daga yau ba zaku sake gigin tsallaka gonar wani ba" "Innalillahi wa inna alaihi....." Ya jiyo muryar daga can gefe tana fada cikin maqyarqyata saboda tsananin tsoron data shiga. Duk tsawarsa guda daya sai taji kamar ana finco mata hantarta tare da qoqarin bintiko zuciyarta daga muhallin da take a dashe. Waiwayawa yayi yana mamakin wanda ya rage a falon bayan ya bada umarnin kowa ya fice. Zuwaira ce tsaye yana rawar dari kamar wadda ruwan da yayi saura har yanzu yake sauka kadan kadan a kanta ya qare. Sulalewa tayi a wajen tana jin wata razana tana saukar mata,idanunsa sun mata wani kaifi da bata da juriyar daukarsu. Yadda yake magana ga duk wanda yake falon zai tabbatar abinda yake fadin zai aikata ne. Ba
Chapter 66 · 0% Book details