Sashe 170
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
daya dace a kaiwa amarya da angon. A yau kadai data sanya order Youghourt da sauran wasu snacks daga wajen deeja beerva aka kawosu tsaf.......sai ta dinga jin sha'awar koyon duka nau'in wadannan abubuwan. Ta duba handle dinta na tiktok da Facebook,ita dai a rayuwarta zata iya cewa batasan mace kamarta ba. Komai ta iya,idan nace komai ina nufin komai da komai din,kama daga kayan gashe gashe,girke girke,kayan mata da na mazan ma da zaki hada da hannunki.....kayan maqulashe,man kitso,man shafawa kai duk wani abu da dan adam zai buqata musamman mace cikin rayuwarta. Hatta fannin gyara mu'amala da zamantakewar auratayya ta hanyar shawarwari. Kai tsaye ta nemeta ta number dinta ta yanke yin register da ita,kafin ta qara nauyi tanason ta zama cikakkiyar mace tako ina,itama ta hada wadannan baiwawwakin.+234 907 927 4454 (Ba sabreen ba,ni kaina magana ta gaskiya na jima banga mutum iri nta din ba,akwai qaruwa sosai tattare da ita,in sha Allah bazan gajiya da kawo muku duk wani mutum da zamanku tare dashi zai amfaneku kuda iyalinku ba). Home service takeso sukayi tsada ta gama komai. Tun bata ganta ba kirkinta a iya waya kawai yasa hankalin sabreen sake kwanciya da ita. A nutse ya kashe motar gaban gidan,duk da mai tsaron gate din gidan ya dage qofar tun isowarsu. Ango farouq dake zaune a seat me zaman banza.....sanye da wata danyar dakakkiyar shadda da iya kallo kawai da idanu zai ganar dakai kudin data lashe. "Ya ka tsaya a nan kuma?". Girarsa kawai ya dage masa yana zare key din. "Muje na taka maka kawai.......sabrrrr tana jirana" "Muma dai Allah ya kawomu dadin abun ko?" Farouq ya fada yana bude side dinshi ya fice. Da ido farouq yabi kyakkyawan kwandon da fu'ad ya dauko da kansa. "Da alama wannan aikin adda ne ko?" Farouq din ya fada yana jin wani girma da kimar sabreen suna hauha a ranshi. "Eh.....ai ta rantse sai wannan tsohon tuxurun ya morewa angwancinsa". "Ta fiyemin kai ai hundred percent" Farouq ya fadi yalwataccen murmushi na subuce masa. "Thank god da babu yadda za'ayi dani ai" Fu'ad ya fadi yana yin gaba yana barinsa da wani nannadadden kwali da shima ke cike da tarkacen kayan qwalama. A veranda din farko fu'ad ya cake yana miqa masa kwandon. "Meye haka dude.....ka qaraso ku gaisa mana" "Da wa?" Ya fada yana zaro idonsa waje. "Fannah" Ya amsa masa kai tsaye. "Allah you're mad farouq.........kawai sai in shiga gidan mutane kai tsaye har can ciki?.....kaga forget about it please...........ka shiga da cikakkiyar sallama please.....don't forget to recite addu'an da miji yakewa amaryarsa a daren farko......don't forget to pray two Raka'at........fatan alkhairi ". Wani qaunar dan uwan nasa yaji yana kamashi,sai kawai ya rungume fu'ad din cikin jikinsa yana fadin. " Thank you dude.....thank you,Allah ya cika maka muradinka". "Kukan zakayi tun yanzun?,akwai sauran awanni" Ya fada jin muryarsa kaman ta karye. Dariya farouq ya saki da risunannun idanunsa yana janye jikinsa daga na fu'ad. Hannu fu'ad din ya sanya yadan daddaki kafadarsa,ya zura hannunsa a aljihu ua fiddo wayoyin farouq din. Latsesu dukka yayi ya kashesu sannan ya miqa masa su yana masa magana da ido akan "Ka barsu a kashe,kada ka kunna". Sannan ya juya a nutse yana fita a gidan gami da bawa guards umarnin su kulle ko ina a gidan. Yana takawa zuwa cikin gidan yana jin wani yanayi yana ratsashi. Wani yanayi daba kowanne zai fahimta ba sai wanda yake a matsayi irin nasa. Da cikakkiyar sallama a bakinsa,tare da qarin addu'ar "Allahumma adkhilni mudhkala sidqin,wa akhrijni mukhraja sidqeen,waj'alni minladunka suld'anan naseera,rabbi anzilni munzalan mubarakan wa'anta khairul munzileen" (Addu'ace me kyau ga amare ko angwaye yayin shiga gida,ko idan kunyi sabon gida a sanda zaki shigeshi). Yana yaye curtain din falon duk wani colors da tsari na dream parlor dinsa ya bayyana,lafiyayyen murmushi ya subuce masa. "My dude.......miskili kafi mahaukaci ban haushi" Ya samu kansa da yiwa fu'ad kirari qasan zuciyarsa. Kowanne taku nasa sai yakejin wata rahama da nutsuwa tana saukar masa,wani irin farinciki yana lullube ilahirin zuciyarsa. Qawatattun bedrooms din nasu har guda hudu ya dinga budewa daya bayan daya,sai ana biyar din sannan ya ganta. Nannade cikin laffayar nan da zata baka tabbacin asalin kanuri dince ita,turararren qamshinta daya dumame dakin kuma ya sake gaya maka still KANURI CE. Sallama ya sake jaddadawa,can qasan maqoshi ta amsa,saidai shi yaji abarsa,murmushi ya sake subuce masa,sai kawai ya duqa yana sabule rufaffen takalmin Gaziano & Glirling dake qafarsa,ya rage saura socks kawai wadda ita tayi masa jagoranci har zuwa bakin gadon da take zaune. Hannuwanta dake lullube da kyakkyawan zanen lalle ya kalla,baisan sanda ya ajiye wayarsa da keys dinsa gefe ba,ya miqa hannu yana dora tafin hannunsa saman nata tafukan hannayenta ba ya riqesu sosai. Wata sheshsheqa ya saki gami da nannauyar ajiyar zuciya duka lokaci daya,wanda suka fito tare da kalmar "Alhamdulillah". Karon farko a rayuwarsa da hannunsa ya soma taba na fannah bayan ta zama halalinsa......karon farko da sukayi kusaci da juna har irin haka,duk da yadda yake tsananin sonta,yake kuma shauqinta,itama kuma haka,amma dukkaninsu sun killace hakan,sun kuma boyeshi qasan ransu,ba wanda ya bari dan uwansa ya fuskanci hakan.(qalubale ga matasanmu) "Babarbariya ta" Ya fada a tausashe da wani taushi da baisan yana dashi ba. Wani suna qwaya daya da ba soyayya ba da yake kiranta dashi,yake kuma mata tsananin dadi. "Taimaki wannan dan bawan Allahn a bude masa wannan fuskar mutanen maidugurin ya kalla" Ya fada yana zamewa,sosai ya zauna a gabanta gami da komawa kalar tausayi,ya koma kaman wani dan almajiri,sai yakejin tun yanzun kaman zai fara sakin kukan da fu'ad ke cewa ya riqeshi tukunna. Kafada ta maqale ba tare datace komai ba,sarai ya gani,duk saita rudashi. "Roqo nake badon halina ba" Ya fada yana riqe hannayenta da kyau cikin nasa. Murmushi ya qwace mata,duk da fargabar da take ciki,sai ta zame hannunta daga nashi a hankali ta sanyasu tana janye lafayarta baya ba tare data daga kanta ba. "Kan uba!....subhanallah" Ya fada yana wani wantsalawa cikin wani irin mamaki. Fannah ta shammaceshi,tunda suka fari soyayyarsu har suka qare bazaice ga wani shape nata daya taba gani ba,koda da wasa kuwa,a yanzun saiga wata ajiyayyar kyakkyawar halitta kuma dukka mallakinsa ce?,yayi yadda yakeso?. Hannu ya miqa zai zame lafayar daga kafadarta,yanason ya sake ganinta sosai sai ya janye hannun da sauri yana murmushi,yana jin kaman wani shock ke jansa. "Dan sake budemin please fannah.....i wanted to see you all". Wuyanta ta langabe alamun aah,ai baibi ta kanta ba sai gashi ya dawo gabanta. Hannuwansa duka ya sanya ya dagata,ya miqa hannunsa gefan qugunta inda ta daure lafayar ya wareshi,ya kuma zarce da wareta gaba daya daga jikin nata. Tsaf ya ware kayarsa,sai yakejin wani abu yana ratsa sassan jikinsa. "Subhanallazi lam yattakiz waladan wala saheeba" Ya tsarkake girman zatin Allah a abinda idanuwansa suka gane masa karo na farko(qalubale gareku mata,wata sai ran bikinta ma take fidda shape din gaba daya mazan duniya dana media su tayashi kalla). Ji yayi idan ya qara koda second daya bai sanyata a jikinsa ba kaman zai mutu,sai ya jawota gaba daya cikin jikinsa yana lullubeta da hannuwansa,qamshin jikkunansu suna cakuduwa guri guda. "Alhamdulillah,first halal hug" Ya fadi a bayyane yana sake godewa Allah da yadda ya bashi iko ya tsare mutuncinsa. Sai da yayi da gaske ya zame jikinsa,don ya fahimci wannan al'amarin bame sauqi bane,idanma har za'a biyewa ta zuciya da gangar jiki,tabbas dukka addu'o'innan da musulunci ya koyar da sallolin ba zasu samu ba. "Ki shiga toilet ki daura alwala,ki rage wannan nauyin na jikinki kizo muyi sallah" Ya fada yana tattare mata lafayarta guri daya. Dama gurin tsira take nema,don haka da sauri da sauri ta wuce bandakin ta turo qofar. Wani wawan tsalle ya buga bayan ya isa dakinsa. "Alhamdulillah" Ya sake maimaitawa yana sauraren bugun da zuciyarsa keyi,sai ya miqe ya soma shima rage kayan nasa jikin sannan ya wuce bandaki. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ 142 *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.....siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashin da babu irinsa_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX Sai da suka tabbatar an kai amarya,an kuma dawo,kowacce mota an ajiyeta a muhallinta sannan sukabar farfajiyar gidan shi da saddiq suna wucewa sassansu da tuni kowannensu shima ya kwashe komai nasa banda furniture din ciki,aka kuma shirya a tagwayen gidajensu masu tsananin kyau da fasali. Saida musaddiq din yayi wanka don yaji dadin jikinsa,ya kuma canza kayansa zuwa sassauqar jallabiyya ta maza. Har zai tada sallah sai kuma ya fasa,ya koma da baya yana dauko wayarsa da tunda suka gama waya da amna ya sakata a charge ya kulle ya barta a dakin. Yayi hakanne don kada ta matsa masa da kira da magiya,taje ta karya masa zuciya yayi abinda baiyi niyya ba. Sam bayajin zai barta fita a gidan,fita daya yakeso tayi,daga gidan sai gidanshi a gobe in sha Allah. Ya tarar kuwa da miscal dinta har guda biyar. "Rigimammiya" Ya fadi yana murmushi sannan ya koma ya zauna yana yunqurin kiranta. Kiran farko aka gaya masa layin a kashe yake,mamaki yadan kamashi,don zai wahala ka kira amna wayarta a kashe,tunda dai su ba rashin wuta sukeyi ba,inverter ne 24/7 a gidan. Sake gwadawa yayi aka sake gaya masa hakan,sai ya haqura ya kira saddiq zuciyarsa na raya masa tayi fushi ne dashi bai kaita ba,shi yasa ta kashe wayar don ta rama,shikam bazai iya jura ba,gwara ya lallaso abarsa, "Huda zaka kiramin,kace tace da amna ta bude wayarta badon halina ba". Dariya saddiq ya bushe da ita. "Man.....wannan karyar da kai haka?,'yan mazan anni na dab da zubewa" "C'mon saddiq.....zaka taimakamin ko na shiga gidan da kaina na nemota?". "Ni na isa?,bari na kira maka ita.....hold on kada ka kashe". Ya fada yana hada conference call . "Hubby..." Ta furta da shagwabar data sanya musaddiq jin kunya ta kamashi. "Love ya akayi?". "Ina kewarka hubby" "I know love......but mun kusa kasancewa da juna in sha Allah,awanni kadan suka rage.....kina ina?" Ya tambayeta calmly. "Na boye a daki hubby.....kunyar anni nakeji". "Anni love?....." Ya fada dariya na subuce masa. "Anni ai bata da surukai sai 'ya'ya,tasha fadin hakan.....fell free please". "I will tray hubby" "Good girl....amna fa?" "Tun dazun da muka karbi adda fannah ban sake