Sashe 78
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read
shi ba,wato ita duk inda taga maza sakin jikinta takeyi?,a ina tasan musaddiq da daga haduwar farko xata sake masa fuska da murmushi har haka?. Idanu ya xuba mata yana kallon yadda take duban musaddiq kai tsaye. "Anyi maka.....amna ma na tabbatar tsokanarka take,don kullum cikin kewarka take,nasha labarinka a wajenta sosai". Ta fada har zuciyarta tana mamakin family din. Kowa na gidan kenan me kirki ne,shi kadai ne maras kirki,maras fara'a,marason jama'a?. Ta tambayi kanta sanda idanunta ya sauka a kanshi. Cikin sa'a idanunsu suka sarqafe guri guda,kusan tare kowa ya dauke dubansa daga kan dan uwansa,sai ya miqa hannu yana karbar takardar hannun ahmad. Da yaren dhivehi asalin harshen mutanen qasar ahmad din yake masa godiyan da batasan ta mece ba. Ga mamakinta sai taji ya maida masa shima da yaren sannan ya ya soma takawa shima yana wucewa ciki da qasaitaccen takun nan nasa. Tana jin muryar musaddiq yana fadin "Godiya nakeyi" Tare da maida kansa ga anni. "Zan kamaki,saikin gayamin dalilin da yasa kina kewata amma baki taba fadimin ko sau daya ba". "Diyata zo mu wuce ciki,wadannan idan kika biye musu zaki wuni a tsaye ne kam" Anni ta furta tana saka hannunta ta kamo hannun sabreen suka fara wucewa cikin gidan. Duk kunyar anni sai ta kamata,tayi qasa da kanta tana biye da ita. Batasan wani abu a duniya da takejin nauyinsa haka ba kaman annin,tana da wani kima a idanunta na musamman. "Yanzu nake shirin leqawa na kiraki ki shigo ciki......wancan shirmammiyar tunda ta hadu da dan uwanta kuma ai shi kenan.....may be daga nan ma yawo zasu wuce iyayen zumudi". " Saddiq....." Fu'ad dake zaune hannun kujera yana duba takardun daya karba yayi kiran Sadiq dake qoqarin daukan ruwa a fridge. Samun kanta tayi da lumshe idonta,batasan me yasa muryarsa take mata nauyi da yawa ba,ba ita ya kira ba,amma sautin kiran yakai mata har tsakiyar qirjinta. Muryarsa tana da wani irin amo me ratsa mutum koda ba dakai yake magana ba. "Na'am" Sadiq yabar abinda yakeyi ya waiwaya yana dubansa,bai daga kai ya kalleshi ba yace "Fita ka gayawa musaddiq kada suje ko ina" "Okay" Ya fada yana ajiye ruwan gami da kama hanyar fita. Numfashi kawai ta aje tana tabe baki,kowa a sake yake amma bandashi,ya iya bada umarni,daga wannan sai wancan,kuma yana iya gama magana dakai kaf ba tare da ya kalli fuskarka ba,ta rasa wanne irin mulki ne haka a cikin jininsa?. Idan kuma muguntarsa ya motsa,ta lura kowa ma da idanu yake hukuntashi,ko don yasan akwai wani abu me nauyi a cikin kallonsa oho?,saita dauke kai gefe tana tabe baki,idanunta kuwa suka sauka kan wani glass door wanda daga nan kana iya hangen wani ruwa nesa kadan dasu dake lullube da farin yashi kaman ta miqa hannu ta kamo. "Gidan ya miki anni?" Ya fada yana sauke takardar daga fuskarsa bayan ya gama jan ajin nasa.