← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 215

Sashe 81

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kamata ayi ba" . Kunya ta saukarwa sabreen,sai kawai ta saki kunnen amna din "Saikije ki daukomin hijab dinki,kayan fice ficen ma duk na fasa sakasu tunda baki sakamin kayan zaman gida na arziqi ba,da hijab zanta zama" "Kaina bisa wuya na" Ta furta tana dariya gami da ficewa. Gudun jira sai kawai ta shirya kanta cikin riga da wandon,rigar ta sauko mata har saman mazaunanta,wandon kuma cif jikinta,don ya fidda sigar santala santalan cinyoyinta da faffadan qugunta. Murda qofan ya sanyata juyowa da sauri tana zaton amna ce ta dawo,saidai a maimakon amna din sai taga hammanta. Fuad ne tsaye fuskarsa babu walwala,kai tsaye ya soma kallonta tun daga qasan qafafunta,idanunsa kuma suka cake akan qirjinta,abinda ya sanya yaji wani yarrr tsigar jikinsa ta zuba. Fes abinda yaji da dumi da qamshin da wajen kiyi ya dawo masa fes a qwalqwalrsa,sosai jini ya harba ko ina a jikinsa,yayi gaggawar damqe numfashinsa gami da hana faruwar abinda yake shirin faruwar dashi. Kallon qurillar da a yau yayi mata karon far ko a tarayyarsu ya ratsa kowanne jini dake gudu a sassan jikinta. Idan tace zata juya masa baya nan ma tasan bata tsira ba,komai na jikinta ita ka ta tayi imanin a bayyane yake. "Karki fara gangancin fitowa a haka......ki nema kinomo ko hijab ki saka a jikinki". Sai ya saki qofar yana juyawa yana jin numfashinsa kaman zai tsaya da aiki. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ Tun kafin ya qaraso idanun farouq yana kanshi,fata ne fal zuciyarsa na daidaituwar al'amura,yasan sarai halin fu'ad......yana da kafiya da taurin kai akan abubuwan da bai fuskancesu ba,amma da zarar ya fuskanta din yafi kowa bawa abun muhimmanci. Ba jiya ko yau suke tare da fu'ad ba,tsohuwar alaqa ce da aka kafata tun basu mallaki hankalin kawunansu ba,mutuwar jiki a wajen fu'ad na fassara abu guda ne tattare dashi,rashin lafiya ta jiki irin ta kowa,da kuma motsawar feeling irin na kowanne lafiyayyen namiji. "Baka da lafiya ne dude?" Farouq ya fada qasa qasa sanda fu'ad ke zama a dining din kusa da farouq din. Qoqarin murjewa yayi yana cewa "Am fine......bacci nayi bai kuma isheni yadda ya kamata ba" "I see..." Kawai ya furta da salon dashi kansa yasan farouq din bai aminta ba. Tare suka jero da amna din suna fitowa,sai ya zare idonsa daga kan wayarsa yana duban sashenta. Baiyi tsammanin zata saka hijab din kamar yadda ya umarta ba,saboda yasam taurin kanta da kafiyarta,sai yaji wani sanyi na ratsashi ganin karon farko tayi abinda yace da ita. Gaida anni ta sakeyi tana rusunawa,sannan suma suka gaidata harda farouq da yake da sauqin kai. Amna ce ta soma servings nasu daga girkin cook din da sukayo hiring anan qasar wato hidaya. Musulma ce data qware wajen sarrafa abinciccikan qasashe da dama. Yawa yawan wadanda takewa aiki masu hannu da shuni ne don ta qware matuqa wajen iya sarrafa tukunya. Da kudi sosai ake daukanta tayi maka iya adadin watanni ko kwanakin da kakeso,amma a wajen mutane irinsu fu'ad din wannan din ba wani aiki bane babba. "Sabreen" Anni ta fada tana dubanta "Na'am anni" "Tashi ki serving mijinki" Wani nauyi taji ta aza mata,amma hakanan ta miqe ta dauki plate ta soma xuba mishin. Tana xubawa tana kallonsa wai ko zaice ya isa haka,amma abun takaici dukka hankalinsa yana kan wayarsa "Qila ma chart yakeyi da fareeda" Wata zuciyar ta raya mata. Wato fareedan ce mutum.....ita tana tsaye saboda shi amma.baida lokacinta?. Duka anni na ankare da komai,abinda ya sake tabbatar mata da tunaninta "It's family time muhammadu....a aje wayar nan haka ko?". Kansa ya daga ya dubi anni yana gyada kai yana sakin qaramin murmushi. Karon farko data gayawa kanta da gaske yana da kyau kaman yadda takeji daga bakin mutane. Bata taba ganin wani abu me kama da murmushi akan fuskarsa ba sai a yau,zancan amna ya sake tabbata na ba wanda yake samun fu'ad din a asalin fu'ad dinsa sai anni. "Is okay" Yace sanda yake maida hankalinsa kan abincin data zuba masan. Abinci sukeci cikin qauna da fahimtar juna,saidai ita din ta koma tamkar bare a cikinsu,hasalima ta kasa sakewa sam,sai juya spoon takeyi. Sai kunnuwa data sanya sanda suke lissafin ina da ina zaa fara fita a goben. Amna keta lissafin abinda zasu kashe "Adda nawa zaa saka miki a account" Amna ta tambayi sabreen,murmushi kadan tayi ta girgiza kai "Ko sisi amna.....me zan siya?" "Tsaraba mana adda.... Akwai traditional market nasu fa,zakiga abubuwa da yawa da zasu burgeki.....kinji anni wai batason komai......adda komai sai tace bataso?". "Musaddiq ka saka mata wani abu itama... Mijinta ya qara mata,idan kuma bata da dolla account saina ara mata nawa guda daya". Anni ta fada tana murmushi,kunyarta tana dada burgeta sosai. Tsam ya miqe abinsa yana dauke wayoyinsa. "Zan kwanta anni" "Mu tashi lafiya,muma kusan kwanciya kowa zaiyi ai dare ya fara" A nan ya barsu ya gangara ya wuce dakinsa,don bayajin sakewa har yanzu a jikinsa. 71 Tun kafin ya qaraso idanun farouq yana kanshi,fata ne fal zuciyarsa na daidaituwar al'amura,yasan sarai halin fu'ad......yana da kafiya da taurin kai akan abubuwan da bai fuskancesu ba,amma da zarar ya fuskanta din yafi kowa bawa abun muhimmanci. Ba jiya ko yau suke tare da fu'ad ba,tsohuwar alaqa ce da aka kafata tun basu mallaki hankalin kawunansu ba,mutuwar jiki a wajen fu'ad na fassara abu guda ne tattare dashi,rashin lafiya ta jiki irin ta kowa,da kuma motsawar feeling irin na kowanne lafiyayyen namiji. "Baka da lafiya ne dude?" Farouq ya fada qasa qasa sanda fu'ad ke zama a dining din kusa da farouq din. Qoqarin murjewa yayi yana cewa "Am fine......bacci nayi bai kuma isheni yadda ya kamata ba" "I see..." Kawai ya furta da salon dashi kansa yasan farouq din bai aminta ba. Tare suka jero da amna din suna fitowa,sai ya zare idonsa daga kan wayarsa yana duban sashenta. Baiyi tsammanin zata saka hijab din kamar yadda ya umarta ba,saboda yasam taurin kanta da kafiyarta,sai yaji wani sanyi na ratsashi ganin karon farko tayi abinda yace da ita. Gaida anni ta sakeyi tana rusunawa,sannan suma suka gaidata harda farouq da yake da sauqin kai. Amna ce ta soma servings nasu daga girkin cook din da sukayo hiring anan qasar wato hidaya. Musulma ce data qware wajen sarrafa abinciccikan qasashe da dama. Yawa yawan wadanda takewa aiki masu hannu da shuni ne don ta qware matuqa wajen iya sarrafa tukunya. Da kudi sosai ake daukanta tayi maka iya adadin watanni ko kwanakin da kakeso,amma a wajen mutane irinsu fu'ad din wannan din ba wani aiki bane babba. "Sabreen" Anni ta fada tana dubanta "Na'am anni" "Tashi ki serving mijinki" Wani nauyi taji ta aza mata,amma hakanan ta miqe ta dauki plate ta soma xuba mishin. Tana xubawa tana kallonsa wai ko zaice ya isa haka,amma abun takaici dukka hankalinsa yana kan wayarsa "Qila ma chart yakeyi da fareeda" Wata zuciyar ta raya mata. Wato fareedan ce mutum.....ita tana tsaye saboda shi amma.baida lokacinta?. Duka anni na ankare da komai,abinda ya sake tabbatar mata da tunaninta "It's family time muhammadu....a aje wayar nan haka ko?". Kansa ya daga ya dubi anni yana gyada kai yana sakin qaramin murmushi. Karon farko data gayawa kanta da gaske yana da kyau kaman yadda takeji daga bakin mutane. Bata taba ganin wani abu me kama da murmushi akan fuskarsa ba sai a yau,zancan amna ya sake tabbata na ba wanda yake samun fu'ad din a asalin fu'ad dinsa sai anni. "Is okay" Yace sanda yake maida hankalinsa kan abincin data zuba masan. Abinci sukeci cikin qauna da fahimtar juna,saidai ita din ta koma tamkar bare a cikinsu,hasalima ta kasa sakewa sam,sai juya spoon takeyi. Sai kunnuwa data sanya sanda suke lissafin ina da ina zaa fara fita a goben. Amna keta lissafin abinda zasu kashe "Adda nawa zaa saka miki a account" Amna ta tambayi sabreen,murmushi kadan tayi ta girgiza kai "Ko sisi amna.....me zan siya?" "Tsaraba mana adda.... Akwai traditional market nasu fa,zakiga abubuwa da yawa da zasu burgeki.....kinji anni wai batason komai......adda komai sai tace bataso?". "Musaddiq ka saka mata wani abu itama... Mijinta ya qara mata,idan kuma bata da dolla account saina ara mata nawa guda daya". Anni ta fada tana murmushi,kunyarta tana dada burgeta sosai. Tsam ya miqe abinsa yana dauke wayoyinsa. "Zan kwanta anni" "Mu tashi lafiya,muma kusan kwanciya kowa zaiyi ai dare ya fara" A nan ya barsu ya gangara ya wuce dakinsa,don bayajin sakewa har yanzu a jikinsa. Wani mummunan horo kawai yakeji farouq yayi masa na hadashi kwana daki daya da ita. Gaba dayansa sai yake jinsa kaman a birkice yake,tun yana qaryata wanzuwarta daki daya dashi ne ya sanya yanayinsa komawa hakan,har yayi amanna cewa hakanne. A dare daya tak ya kasa samin isashen bacci har zuwa wayewar gari,wayewar garin da ya tashi da ninkin rashin kuzari da karsashi a tattare dashi,fiye ma da yadda ya kwana jiya. Kowanne motsi farouq yana ankare dashi,dariya qasan ranshi kaman zata kasheshi. "Duk dacin ranka.....duk miskilancinka halittar mace tafi qarfinka ko kai waye......qaton tuzuru dakai sai taurin kai da kafiyan da ba inda zasu kaika?,dama can sarari ka samu,nisan tazarar dake tsakaninku ya sanya kake ganin kamar baka da wata buqata ko sha'awa irin ta d'a namiji.....wallahi qarya kake fu'ad......a wannan fannin ni kaina na sallama maka.....zan gani idan tusa zata hura huta......daga yau zuwa gobe kawai na baka,if kaci gaba da taurin kai.....nasan matakin da zan dauka a kanka" Farouq yayi dukka wannan gulmar cikin zuciyarsa yana duban fu'ad dake zaune yana kurbar maca and ginseng tea. Kaman baiso yake daga cup din zuwa bakinsa,shi kansa,ranshi a jagule,baiso irin wannan yanayin ya tasammasa a irin wannan lokacin ba sam,saidai koma meye zaya faru bayajin zai yarda koda da wasa ya hada jikinsa da ita. Jikin da akullum ya kalla sai yayita lissafin adadin maza nawa ne suka rabeshi?,adadin maza nawa ne suka tabashi?,dame dame sukayi da ita?. Yana da bala'in qyanqyami na fitar hankali,wannan qyanqyamin ya sanya bayajin shikam ko mata biyu zai iya aura,gwara ya tattara mutuntakarsa a muhalli daya. Uwa uba wani irin kishi ne dashi,ba kuma wai yanzu ba,tun tale tale zai iya cewa da kishin ya tashi,dashi aka halicceshi. Baisan maruka nawa yasha daga hannun maamah ba
Chapter 81 · 0% Book details