← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 215

Sashe 128

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

a awannin da sukayi suna tafiya cikin sararin samaniya duka bacci tayi sosai,duk da irin zazzabin dake a jikinta bai kuma sauka ba. Tafiyar awanni biyar suka sauka a dubai Abu Dhabi.
Movenpick hotel and apartments nan farouq ya kama musu,5star hotel ne dake da tsada saboda kusancinsa da burj alkhalifa. Ya zabar musu shi saboda yafi kusa da American hospital.
Kafin su qarasa ma tuni yayi booking Dr din da zata dubata,don ya tabbatar fu'ad bazai yarda mo giyar wake yasha namiji ya taba sabreen ba.
Cikin mintuna kadan ya kammala dubata,akwai test da taso ayi amma fu'ad din yace suna kan hanya,awanni kadan zasu wuce madina,a can za'ayi mata general checkup gaba daya,ta bata kawai taimakon da zazzabin zai sauka.
Ruwa ta saka mata wanda zai suake zafin zazzabin,ya kuma bata qwarin jiki,wannan ya sabbaba ba mata wani sabon baccin bayan wanda tayi.
Kwata kwata hankalinta yaqi kwanciya kaman yadda bataso fu'ad din yace abar test din ba,zataso taji mene ne?,wanne irin lalura ce wannan tun daga wata uwa duniya har nan gurin?.
"Wanne irin abune da zai sanya ka hana a gwadata aga abinda yake damunta?,idan akayi maya treatment da ka fa?" Maamah data kasa hadiye abinda yake cin ranta ta fada tana duban fu'ad.
Duba daya anni tayi mata ta maida dubanta ga plate din abincinta da yake dukkaninsu suna kan dining table. Maganin shege karen maguzawa,ta fahimci duk wata alqibla ta maamah.......tana kuma karance da dukmotsina,wannan dalilin shi ya sanya duk sujjadarta idan ta aza goshinta a qasa saita yiwa Allah magiyar ya sanya rabo ne a jikin sabreen din,wala'alla wannan ya zamewa mariya ishara a rayuwarta.
"Ni banason wannan tangal tangal din da rayuwa,karo na gaba dole a gwadata asan me yake damunta,ayita zauje da ciwo ba'asan wanne iri bane?".
"Na alkhairi ne" Shine abinda anni taso fadi,saidai kuma ta duba cewa da d'anta take magana.....bari ta barta da pain din rashin sanin taqameme din ciwon sabreen din,sai hasashe sai zargi da zato da zai hana zuciyarta nutsuwa guri guda.
Shurun da akayi mata ya sake qonata sosai,taso tayita jan maganan ne amma ba wanda ya tayata a cikinsu,dole ta qunshe maganarta,daga qarshe ma abincjn qin ciyuwa mata yayi,saita koma daki ta kasa zama.
"Ko na sakashi ya kawomin ita da xummar zan kula da ita zuwa safiya?,ta nan wataqila na fahimci komai?" Ta shawarci kanta da kanta,saidai ita kanta tasan wannan shawarar bame bullewa bace,don bataga ta inda zai aminta ya bata sabreen ba,mutumin da bai jima da dawo da ita cikinsu ba.
Wayarta ta dauka ta djnga laluben da wanda zata zanta,sam sam bataso rabuwarsu da hajja a irin wannnan lokacin ba bayan muradanta basu kammala cika ba. Number bokanta ta shiga hasashen inama akwaita?,inama yana riqe waya?,saidai nan ma ba wani mafita dole Takoma ta zauna tana tunanin zai wahala ta zauna a makka ko!madina harsu gama kwanakinsu,tanajin zata saka ya sanya a maidata gida ne,idan yaso su sa taho daga baya,kafin su iso djn kuma ta gama nata shirin......sai fashewar bomb din
_WASHEGARI_
*_GAMO DA KATAR_*
_Prince muhammad bin abdul'azeez airport (madina)_
Chapter 128 · 0% Book details