← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 161 OF 215

Sashe 161

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kin bar muhammad ba.....da baki gudu kinbar musaddiq ba". A tattare dasu gaba daya tana ganin wata irin nagarta ta musamman. "Hammanki yace ki rubuta ko kije gurin addarki ki.masa list na kayan lefe duka" Anni ta fada tana nazarin amna data fahimci ta yawaita shuru shuru tun daga yammacin yau din. "Lefe ann?" Amna ta tambaya da wata sassanyar murya "Wani abun daban kikaji na fada?" Anni ta fada tana nazarinta. Kai amna ta girgiza,haka kawai taji hawaye sun cika idanunta,sai anni ta kasa jurewa. "Meya kuma?" "Tsoro nakeji anni......gabana yanata faduwa" Sai hawayen da take maqalewa ya gangaro mata. "Tsoro?" Anni ta maimaita,kai amna ta gyada mata. Yankewa gaban anni yayi ya fadi,ta sauke numfashi tana ambaton sunan Allah. "Tashi kije kiyi alawala,ki karanta hasbunallahu wa ni'imal wakil qafa dubu kafin ki kwanta". Kai amna ta gyada sannan ta miqe a sabule tana fita a dakin zuwa nata. "Addanmu" Fu'ad dake tsugune gaban sabreen da bacci yaketa danneta ya fada yana leqa fuskarta. Da qyar ta sake bude idon nata a karo na uku. "Adda sabreen.....tashi don Allah" A cikin baccin taketa mamakin kiranta da adda din da yaketa yi,saita miqe tana daquna fuska. "Hamma.....bacci" "Zakiyi,na miki alqawari,amma kafin sannan jeki wanki fuskarki ki dawo". A daddafe ta miqe saboda nauyin bacci,ta lalubi toilet din ta shige. Ba jimawa ta fito,fuskarta tayi fresh da digo digon ruwa,idanunta sun dan tashi kadan alamun bacci,ta zauna saman sofa tana dubansa. Ajiye abinda yakeyi yayi ya taso,ya iso gabanta ya tsugunna a hankali. Hannuwansa yakai ya kamo tafukan hannayenta a tausashe. "Adda sabreen" Ya maimaita fadi yana murmushi. Idanu tadan ware tana dubansa wani malalacin murmushi yana qwace mata. Kai ya jinjina mata. "Kin bamu daman neman auren sister huda?.....kin bamu izini mu nemawa musaddiq auren sister huda?". *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ 136 *_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_* *_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_* *_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_* *_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_* *_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_* *_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_* *_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_* *_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_* *_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_* *_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_* *_HAIHUWA KIKAYI?_* *_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_* *_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_* _Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_ 08104553105 08127084190 *_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_* *_BGAWO'S KITCHEN_* *MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU* Wani saukar ba zata zancen yayi mata,wani irin zuwa ya yiwa kunnuwanta. "Saddiq kuma?,saddiq dai hamma?" Ta fadi da sautin muryar bacci da har yanzu bata gama warwarewa ba,banda ta zuba ruwa saman fuskarta da sai tace cikin jerin gwanon mafarki kawai wannan maganar take dibanta. Murmushi ya saki me sanyi yana jinjina mata kai. "Eh......saddiq dinmu addanmu......inaso ya zama mijin huda nan da kwana hudu,kaman yadda farouq zai zama mijin fannah in sha Allah" A hankali ta daga ido tana sake duban fu'ad din,sai takeji kaman wasa yake mata da hankali kawai ko tsokana,saidai kuma ko daya bataga wannan a cikin idanunsa ba. "Hamma.....huda fa?.....ka manta mudin ba kowa bane hamma.... Mu din ba wasu madaukaka bane,ni din kawai a cikin family dinku ya isa,basai huda ta shigo ba...." "Shshshsh" Ya fada yana dora yatsantsa akan lips dinsa. Bayason wannan karayar da take nunawa,bayason wannan raunin da yadda har yanzu ta kasa jinta kaman kowa.....bayason yadda ta kasa daina tuna wacece ita a baya "Damu daku dukkaninmu abu daya ne yayimu.....jirgi daya ne ya kwaso mu.....ki manta akwai wani lokaci da abinci da sutura suke gagarar muhammad fu'ad?....ki manta akwai wani lokaci daya shude da yunwa take saka musaddiq kwana yana kukan yunwa?,kin manta wani lokaci daya shude fu'ad dan jari bola ne?......kin manta sanda saddiq ke kwana da yunwa saboda ba gatan uwa a gefansa?,duka damu daku ki gayamin meye banbanci a ciki?" Shuru tayi tana tuna komai kaman yadda yake tunasar da ita yanzu. "Hamma.....amma huda batayi qanqanta ba?.....yanzu zata gama secondary school fa......a haka an sanyata a makaranta da wuri kaman yadda abbanmu yake mana....." Murmushi ya saki yana dan jan kumatunta. "Qanqanta?.....ke din kanki duka duka shekara nawa kika bata?,banajin yakai biyar,ba gashi muna zaune ba?". "Hamma karatunta fa?" Hannu ya sanya yana dungure mata kai da sauri "Lallai dai sai an ja mana aji kafin a bamu auren sister huda.....lallai ko yaya wai sai an wajiga mu?.....me huda zatayi da karatu duniyata?,ba huda ba.....ko wanda ke rayuwa qarqashin inuwar jadda banajin zai buqaci karatu saboda ainihin buqata ta lalura.....saidai duk me sha'awa yayi karatun don dai sunansa ilimi.....ba abinda huda zatayi da takardu.....saidai.idan har tanason karatu saddiq bazai hanata ba.....za'a dauko mata duk kalar malamin da takeso ya koyar da ita matakin ilimi daga na college har zuwa university har PhD ma.......idan kuma makaranta takeso......ta zabi duk makarantar da takeso a fadin duniya cikin jerin qasashe da muke dasu a duniya 195 zuwa 200....kowacce take so zataje in sha Allah......sai me kuma......a shirye muke mu karba duka qorafinki" Ya qarasa fada yana tsareta da ido tare da jiran abinda zata sake fadi. A hankali ta jinjina kai "Na amince hamma.....na bada izini bisa sharadi da alqawarin zai bata dukkan wata kulawa data dace koda bayan raina". Wani zazzaro idanu wajen fu'ad yayi yana dubanta. "Kul.....karki sake zancan bayan ranki my world......waye ya gaya miki fu'ad yana da sauran rayuwa bayan babu taki?". Idonta ta maida ta lumshe a hankali tana murmushi. " Zamu rayu tar in sha Allah......zamu kula da yaranmu mu kuma basu tarbiyya tare" Ya fada yana sumbatar hannunta a tausashe. "Na gode sosai duniyata.....na gode sosai da sadaukarmana da daya daga cikin abubuwan da kike matuqar so a duniya.....kika yarda ta zama abokiyar rayuwar saddiq" "Kafi qarfin komai a wajena duniyata.....kafi gaban haka muffin". Ta fada itama harshenta da sautinta cike da qauna da soyayya. " Bayan gidan malam......sai ina da ina kike kai taimako?" Ya sake soko Mata tambayar da bata taba kawota ba. Fararen idanunta ta daga ta kalleshi,sai kuma ta sauke idanun nata qasa tana jin nauyinsa. Batason abinda zai sanya ya dauko mata wannan zancan na abinda ya wuce a tsakaninsu. "Ki bani dama.....inaso ki dore da aikin ladan da kikayi niyya in a halal ways.......inaso na miqar dake kici gaba da abinda kika fara a baya". Sake kallonsa tayi a karo na biyu......tana jin yana sake shiga rayuwarta yadda ya kamata. Soyayyarsa tana sake hudata,wani mafarki ne wannan nata,dasu take kwana dasu take tashi.....hayewar su huda kawai bai sanya zuciyarta ta kwanta d'ari bisa dari ba.....bai sanya zuciyarta ta samu nutsuwar da take yunwar samu ba. A yanzun a kuma wannan lokacin sai gashi ya gama qarasa karanta tunaninta kafffff yana son xike mata ragowar gibin da ya rage. "Me yasa a kowacce rana kake sake karantar zuciyata?,me yasa a kowacce rana kake abubuwan da suke sake haukatani a kanka muffin?". Idonsa ya lumshe yana budesu duka a lokaci guda. Yanason irin wannan yanayin.....yana son irin wannan lokacin da zaiyi zaune kawai a gabanta yana tana tona masa asirin zuciyarta. "Sabrrrrr" Ya sake kiranta a tausashe. "Haqqina ne.....kuma cikar kamalar kowanne d'a namiji kenan,ya karanci wace matarsa.....me tafi so?,me tafi buqata?,me zaiyi ya mallaketa?". Mallakar daya fada ta sakata fashewa da dariya tana zaro ido. " Hamma.....mallakata kakeso kayi?" "Nama mallakeki duniyata.....na mallakeki....kedin tawa ce ni kadai har abada" Ya fada yana daga yatsunsa guda biyu. "Gidan marayu.....gidan gajiyayyu.....yaran da iyayensu suka mutu suka barsu kuma babu me tallafa musu irinmu" Takai qarshen maganar muryarta tana karyewa. "Ki zauna ki tsara dukkanin burinki akan wadannan gidajen". Ya fadi yana miqewa tsaye. Wani irin sanyi taji yana sauka saman zuciyarta "Ina fata ubangiji ya lullubeka da dukka rahamarsa......ya yaye maka damuwarka.....ya kyautata qarshenka.....na gode da karamcinka karimin mijina.....na gode da wannan halin dattako naka uban 'ya'yana". Murmushi me sanyi ya kubce masa,yanajin alfahari da wannan addu'ar tata. "Allahumma ameen matata 'yar aljanna.....amma saura abu daya da baki roqamin ba". Idanunta ta juya,abinda ya sake tafiya sosai dashi " Me kenan muffin?" "Baki roqi Allah ya qarawa wannan ameenatun so na ba.....so nake ameenatu ta soni fiye da yadda takeson kanta,don kuwa ta samu wanda zai kula mata da kan nata" . Kunya ta sakata sanya tafin hannunta ta rufe fuskarta kafin tace. "Inda ana iya bude zuciya ko qirji a nunawa wani.....tabbas da na bude maka tawa zuciyar kaga abinda yake ciki a kanka,wataqila zakafi gasgatani.....don maganar fatar baki tayi kadan" Rasa me zaya ce mata yayi,sai kawai ya tsugunna yana kissinh forehead dinta a tausashi. Yana dauke labbansa tana daga idanunta da sauri,sai ta soma rarraba idanun nata tana a narke. "Kai.......ina doughnuts dina?" . Dubanta yayi "Wanne doughnut?". Ya tambaya yana tunanin ko mafarki tayi a dazun kafin ya tashera. Tambayar tata da yayi sai taji kaman zata saki kuka "Doughnuts dina mana da ma'u ta bani......a nan fa na ajjiye naci kadan na ajiye sauran". Qaramin murmushi yayi. "Kin cinye madam....ni na tattara kwalin na zuba a dustbin". Idanu ta waro waje tana dubansa sosai da salon rigima a muryarta. "Ka sakamin a shara?,wallahi ban cinye abuna ba,akwai saura" Ta fadi tana miqewa zumbur gami da nufar dutsbin din. Da mamaki yake binta da kallo ganin yadda ta bude dustbin din tana ciro kwalayen. "Kai?,ka cinyemin?" Ta fada cikin sanyin jiki hawaye yana taruwa cikin oily eyes dinta. Dariya ma abun ya bashi,ya daga hannunsa alamun surrender yana dubanta. "Innalillahi,Allah ba ruwana,sanda nazo ba komai a ciki sai boxes din da leda". Dariyar tasa ta qular da ita,sai kawai ta fashe da kuka tana sakin boxes din. "Wallahi kaine.....kaine ka cinyemin kuma bazan yarda ba" Mamaki sosai ya kamashi ganin yadda ta zube tana kuka bilhaqqi,hawaye shabe shabe ta dage wai shine ya cinye mata. Da sauri ya isa inda take yana miqa mata hannu. "Yi haquri ki tashi.....eh na yarda nine na ci". Ya fadi hakan don ya lura
Chapter 161 · 0% Book details